Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rantsar da Biden: Yadda fadar White House take sauyawa tsakanin sabo da tsohon shugaban kasa
- Marubuci, Daga Tara McKelvey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC White House reporter
A ranar Laraba ne za a kawar da duk wasu abubuwa da suka shafi shugabancin Trump, yayin da iyalan Biden za su shiga fadar White House. Za a kwashe, tare da goge duk abubuwan da ke kan tebura, da share cikin dakuna, kana za a maye gurbin mataimakan Trump da sabbin tawagogin masu rike da mukaman siyasa daban-daban. Wannan wani bangare ne na gagarumin sauyin da sabuwar gwamnati za ta shigo da shi.
A yammacin wata rana ne, Stephen Miller, mai bayar da shawara kan harkokin siyasa kuma babban kusa a fadar White House ta Trump, yana shakatawa a bangaren yamma na fadar shugaban kasar wato "West Wing".
Miller, wanda ya sha rubuta jawabai da manufofin gwamnati ga shugaban kasa tun farkon kama aikinsa, na daya daga cikin mambobi kadan da suka rage a tawagar Trump ta farko a tare da shi zuwa wannan lokaci.
Da alamu ya nuna ba a gaggauce yake ya bar fadar ba, yayin da yake kishingide a jikin bango yana tattaunawa da abokan aikinsa kan zaman tattaunawar da aka shirya yi nan gaba kadan a waccan ranar.
Galibi wannan bangare na West Wing an saba ganin shi cike da kai komon jama'a, amma yanzu wurin tsit domin babu jama'a. Babu karar buga wayoyin salula. Tebura a ofisoshin da babu kowa cike da takardu da wasikun da ba a bude ba, kai ka ce mutane sun fice ne cikin gaggawa kuma ba za su sake dawowa ba.
Gwamman manyan jami'an gwamnati da mataimakan shugaban kasa sun fice a ranar da aka yi hargitsi a majalisar dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairu. Kadan daga cikin masu yin biyayya da Trump irin su Miller ne kawai suka rage.
Yayin da muka soma hira, ya matsa daga kusa da abokan aikinsa. Lokacin da na tambaye shi ina zai koma nan gaba kuma, ya yi murmushi. "Zan koma ofishina," ya ce kana yana takawa a sannu cikin zauren taron.
'Akwai sarkakiya'
A ranar da za a rantsar da sabon shugaban kasar, ofishin Miller zai kasance a share, sharewar da za ta kasance tamkar shi da abokan aikinsa ba su taba zama a nan wurin ba, yayin da ake jiran tawagar Biden ta shiga.
Share ofisoshin da ke bangaren na West Wing, da kuma bikin mika mulki tsakanin shugabannin biyu, bangaren wata al'ada da aka saba yi tun a karni da dama da suka wuce.
Daya shugaban kasar da aka taba tsigewa, Andrew Johnson, na jam'iyar Democrat, ya ki ya amince da Ulysses S Grant na jam'iyar Republican a shekarar 1869 kana ya ki halartar taron bikin rantsar da shi. Grant, wanda ya goyi bayan tsige Johnson daga kan karagar Mulki, bai yi mamaki ba.
A wannan shekarar, ko shakka babu mika mulkin na cike da nuna jin zafi. Akan fara aiwatar da shi da zarar an kammala zabe, amma wannan ya fara ne bayan jinkirin makonni saboda Trump ya ki amincewa da sakamakon zaben.
Kana shugaban kasar ya ce ba zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar ba.
Me yiwuwa zai tafi wurin shakatawarsa na Mar-a-Lago club a jihar Florida.
Za a gudanar da mika mulkin ne kamar yadda aka saba yi a baya.
"Za a gudanar da bikin kamar yadda aka tsara," in ji Sean Wilentz, wani farfesan tarihin Amurka a Jami'ar Princeton University. "Yana da sarkakiya, yana da gutsiri-tsoma, amma duk da haka za a gudanar da bikin mika mulkin.''
Ko da a lokuta masu dadi ne, gudanar da bukukuwan mika mulki na da matukar wahalarwa, sun shafi manyan sauye-sauyen ma'aikata da sauran harkokin tafiyar ta sabuwar gwamnati.
Stephen Miller daya daga cikin masu rike da mukaman siyasa 4,000 ne da gwamnatin Trump ta nada da za su rasa aikinsu, kana a maye gurbinsu da wasu wadanda Mista Biden ya nada.
Lokacin mika mulki, mutane akalla daga 150,000 zuwa 300,000 ne ke rubuta takardar neman ayyuka ko mukamai, a cewar cibiyar lura da mika mulkin shugaban kasa, kungiyar mai zaman kanta da ke birnin Washington. Kuma mukamai 1,100 a ciki na bukatar amincewar majalisar dattawa. Cike guraban duka mukaman na saukar watanni, har ma shekaru.
Za a mayar da takardu masu kunshe da manufofin gwamnati na shekaru hudu, litattafan jawabai da sauran kasidu da suka danganci ayyukan shugaban kasa zuwa kundin ma'ajiyar kasa, inda za a ajiye su cikin sirri har na tsawon shekaru 12, muddin ba shugaban kasa da kansa ya bukaci a fito da wasu daga ciki ba.
Kwanakin karshe
A ranar aiki da yamma lokacin makon karshe na Trump a ofis, kofar shiga ofishin Kayleigh McEnany, sakatariyar yada labarai ta shugaban kasa ta kasance a bude.
McEnany na daya daga cikin manyan masu kare muradan shugaban kasa.
Shi ma ofishin nata an gyara shi sosai, duk da cewa tana shirin barinsa. Akwai wani madubi na kafe a kan teburinta, akwai kuma itatuwan wuta da yawa daure wuri guda a cikin wata leda.
Galibi dai kwanakin karshe kan zama "lokacin damuwa da rashin nutsuwa" ''in ji Kate Andersen Brower, wacce ta rubuta littafi a kan fadar White House, 'The Residence'.
Kayyaki a fadar White House, kamar su teburin alfarma a ofishin shugaban kasa, da sauran kayan kyale-kyale da kayan karau na cin abinci duk na gwamnati ne, don haka za su ci gaba da kasancewa a nan.
Amma sauran kayayyaki kamar su hotunan tsohon shugaban kasa da aka kafa a wasu wurare duk an saukar da su, saboda fadar White House za ta karbi bakuncin sabbin mutane.
Ma'aikata na cigaba da fitar da wasu kayayyakin daga cikin ginin. Wata ma'aikaciyar fadar White House na fitar da wasu kayayyaki da hotunan mai dakin shugaban kasa Melania Trump daga bangaren 'East Wing' na fadar. Ana kiran hotunan "jumbos" saboda irin girman da suke da su, ta ce za a kai su wurin ajiyar kaya na gwamnatin kasar.
Za kuma a mayar da kayan Trumps kamar su tufafi, agoguna, da sauran kaya zuwa sabon gidansa da ke Mar-a-Lago jihar Florida.
Shugaban kasa da Mr Miller, har ma da gwamman sauran mutane a fadar White House, sun kamu da cutar korona a cikin watannin da suka gabata, kuma za a wanke tare da tsaftace hawa na shida na ginin da dakuna 132.
Komai da komai, kama daga karafunan hawa bene, abin danna lambar hawa litfa da wurin shiga bandakuna duk za a goge su da maganin kashe kwayoyin cuta, kamar yadda mai magana da yawun sashen gudanarwa na hukumar lura aikace-aikacen fadar White House ta bayyana.
Galibi iyalan shugaban kasa masu shigowa kan sake tsarin adon wuraren. A cikin kwanakin da suka shigo fadar ta White House, Mr Trump ya zabi hoton shugaba Andrew Jackson ya kasance a ofsishin shugaban kasa. Ya kuma maye gurbin labulaye, da kujerun shakatawa da darduma a ofishin da wasu masu launin ruwan gwal.
A ranar rantsar da sabon shugaban kasa, mataimakin shugaban kasar Pence da matarsa za su bai wa Kamala Harris da mijinta Doug Emhoff wuri. Za s koma da zama a gidansu na gwamnati , mai nisan kilomita kadan daga fadar White House.
Rufe wani shafi
Mai yiwuwa Stephen Miller zai ci gaba da kai komo a bangaren yamma na fadar White Housa, amma sauran a shirye suke su tafi.
A fadar White House, mutane na ta diba da jan manyan hotuna, ambulan da jakunkuna. ''Wannan ita ce ranata ce ta karshe," in ji wani mutum yana murmushi yayin da yake dibar hotunan 'yayansa maza. Yana dauke da wata makararriyar jakar goyo a kafadarsa.
Wasu jami'an hukumar tsaron kasa sun taru wuri guda a gaban ginin bangaren yammacin fadar White House, sun bukaci na dauke su a hoto.
"Ka tabbatar wurin 'marine guard' ya fito," in ji daya daga cikin jai'an, yana nufin jami'n tsaron da ke tsaywa a bakin kofar shiga ofishin shugaban kasa.
Jami'an na cike da annashuwa, suna ta barkwanci suna kallon kyamara.
Masu rike da mukaman siyasa a fadar White House na cike da farin ciki a bisa dalilai. Sun shafe makonni hudu cikin tsaka mai wuya. Shugabansu nuna rashin amincewa da sahihancin zabe, amma sun san cewa lokacin ficewarsu ya kusa. Yanzu za su iya fitowa fili su tsara yadda makomarsu za ta kasance, kuma da alamu suna jin dadi.
Wani mai rike da mukamin siyasa, sanye da bakar kwat, ya riga ya tsara yadda rayuwarsa za ta kasance. Ya yi kicibis da wani abokin aikinsa a wajen ofishin tarbar baki. "Sai mun hadu a daya wurin," ya ce yana murmushi. Yana nufin a wajen bikin mika mulki, lokacin da dukkanninsu za su fice daga aikinsu na fadar White House. Ya kuma fara tunanin inda za su sake haduwa. "Me yiwuwa a wani wuri da ban."
"Kwarai kuwa. Tabbas gaskiya ne,'' in ji abokin aikinsa, yana dariya. Sun tafa hannu sannan kowa ya kama gabansa.