Masu tsaurin ra'ayin Musulunci a Mozambique: Majalisar Ɗinkin Duniya na gargaɗi kan ƙaruwar hare-hare a Cabo Delgado

    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent, BBC News

Adadin fararen hular da rikicin da ake yi a arewacin Mozambique ya tilasta wa barin gidajensu ya ruɓanya sau huɗu a wannan shekarar - inda ya kai 420,000 - a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ta ɗora alhakin rikicin da ke faruwa a yankin Cabo Delgado a kan hare-haren masu tsaurin kishin Musulunci da kuma rashin rarraba arzikin da ake samu daga albarkatun ƙasa da makamashin gas ga mutanen ƙasar.

Wata babbar jami'ar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ziyarar aiki a Cabo Delgado ta bayyana halin da ake ciki a can a matsayin "mawuyaci" kuma ta buƙaci maƙwabtan Mozambique da sauran ƙasashen duniya su tsoma baki a kan abin da ta kira rikicin da aka daɗe ana yi ba tare da an mayar da hankali a kansa ba.

"Alƙaluman na hauhawa a kowacce rana kuma wannan yanayi ne da zai iya ta'azzara," a cewar Angèle Dikongué-Atangana, mataimakiyar daraktar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Afrika Ta Kudu, wadda ke jawabi ga BBC daga babban birnin Cabo Delgado, Pemba.

Ms Dikongué-Atangana, ta yi gargaɗin cewa yanayin "ta'addancin" da ke faruwa a Mozambique ya soma yin kama da wanda ke faruwa a arewacin Najeriya, inda Boko Haram ke ci gaba da kashe mutane.

Ms Dikongué-Atangana ta ɗora alhakin hare-haren da ake kai wa a Cabo Delgado kan mayaƙan ƙungiyar da ke da alaƙa da Islamic State inda ta soki halayyar kamfanonin da ke haƙar ma'adinai masu daraja wajen ingaza kai hare-haren.

'Fata na gari'

"Idan aka haife ka a irin wannan wuri, wanda Allah Ya horewa albarkatun ƙasa, sannan ka ga yadda ake ɓarnatar da su... za ka yi matukar rashin jin daɗi," a cewarta, inda ta yi gargaɗin cewa akwai matasan ƙasar Mozambique da "ba su da wani fata na gari," kuma za su iya soma tunanin irin na matuƙar tayar da ƙayar baya.

A watannin baya bayan nan, dubban mutane na taka sayyada ko kuma su shiga kwale-kwale inda suke tuttuɗa birnin Pemba da ke gefen teku, bayan sun guje wa rikicin masu tayar da ƙayar baya da ya yi ƙamari a shekara uku da rabi da suka wuce.

"Babu abin da ya rage mini sai wannan kwale-kwalen," a cewar wani makusancin Adji Wazir a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP. Matarsa, Aziza Falume, ta haifi 'ya mace a cikin teku lokacin da suke tserewa daga rikici.

"Har yanzu ina jin tsoro. Ina ta mamakin yaushe masu iƙirarin jihadi a Pemba za su kawo hari, ko kuma akwai wasu da ke zaune tare da mu," in ji ta.

Hukumar Tsaron Amurka ta yi gargaɗin cewa Pemba "ka iya fuskantar hari saboda kusancinsa da masu tsattsauran ra'ayin addini".