Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Afirka ce sabuwar cibiyar gwagwarmayar masu iƙirarin jihadi?
- Marubuci, Daga Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC security correspondent
Kimanin dakarun Birtaniya 300 sun isa kasar Mali mai fama da rikicin da masu iƙirarin jihadi ke tayar wa a lokacin da ake ganin aikace-aikacen kungiyar IS suka koma Afirka daga Gabas ta Tsakiya.
Dakarun za su shiga cikin wani shiri na tsawon shekara uku da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta mai suna Operation Newcombe, wanda dakaru 15 karkashin Faransa za su yi kokarin dawo da zaman lafiya a yankin da aka fi sani da Sahel.
Mali na cikin kasashen yankin na Sahel da ke fama da yake-yake da ake yi da masu iƙirarin jihadi.
Kamar yadda alkaluman wata kungiya mai suna Global Terrorism Index ta wallafa ranar 25 ga wata Nuwamba ke cewa, "ayyukan tayar da kayar baya da kungiyar IS ke yi sun fi karfi a Afirka da kuma Kudancin Asia bayan da kungiyar ke janyewa daga Gabas ta Tsakiya."
Alkaluman na cewa yawan mutanen da IS ta halaka ya karu da kashi 67 cikin 100 a yankin da ke kudu da hamadar Sahara cikin shekarar da ta gabata.
"Bakwai cikin kasashe 10 da ayyukan ta'addanci suka fi karuwa na yankin da ke kudu da hamadar Sahara ne: Burkina Faso, Mozambique, DRC, Mali, Niger, Cameroon da Ethiopia".
Rahoton ya kuma bayyana cewa a shekarar 2019 "yankin na Sahel ya fuskanci ayyukan ta'addanci da ISIS ta haifar misali na kashe-kashen mutane 982, ko kashi 41 cikin 100 na jimillar.
'Mataki na gaba a yaki da ta'addanci'
Masu iƙirarin jihadi sun daɗe a nahiyar Afirka.
A shekarun baya-bayan nan tsohon shugaban al-Qaeda marigayi Osama bin Laden ya mayar da Sudan ta zama cibiyar sa kafin daga baya ya koma Afghanistan a 1996.
Kungiyar Boko Haram ta Najeriya, wadda ta yi kaurin suna saboda garkuwa da daruruwan 'yan matan Chibok da ta yi a 2014, ta rika kai hare-hare bayan da ta yi shekar fara jihadi a 2010.
Amma a yau saboda karuwar kungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke gasa da juna, matsalar ta'addanci sai kara yaduwa take yi a yankin.
Ma'aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta ce: "Afirka ce fage mafi muhimmanci da za a gwabza yaki da ta'addanci a shekaru masu zuwa."
Amma wannan ba kawai ya shafi rikici tsakanin gwamnatoci da masu ikirarin jihadi ba ne, akwai kuma wata mummunar gasa tsakanin masu goyon bayan kungiyoyin al-Qaeda da IS.
Gasar ta kai matsayar da sai da wani kwararre kan harkokin jihadi mai suna Olivier Guitta ya yi wani hasashe:
"Afirka za ta zama fagen dagar masu ayyukan ta'addanci na shekara 20 mai zuwa kuma ita ce za ta maye gurbin Gabas ta Tsakiya."
Al-Qaed da IS na da wata kiyayya ta musamman ga shugabannin da bin tafarkin ilimin boko, wadanda suke kiransu "kafirai".
Amma sun bambanta kan yadda suke gudanar da ayyukansu.
IS ta fi son amfani da matakai masu tayar da hankali da kashe-kashe da barnata dukiya - misali shi ne yadda suke nadar bidiyon lokutan da suke fille kawunan mutane.
Amma al-Qaeda kuwa ta fi son jawo hankulan al'umomin yankunan da ta ke aiki musamman wadanda suka dawo daga rakiyar gwamnatocin da ke mulkinsu, ko jami'am tsaronsu, kuma su kan yi amfani da bambance-bambance kabilanci da na harshe wajen kara raba kawunan al'umomi.
Ƙasashen da suka fi fadawa cikin hatsari
Mali da yankin Sahel
Yawancin kasashe matalauta na duniya na kusa da hamadar Sahara ne.
Wannan ne yankin da ake kira "Sahel", wadda kalma ce ta Larabci da ke nufin "gabar ruwa".
Mali da Chadi da Nijar da Burkina Faso da Mauritania su ne kasashen Sahel kuma dukkansu sun sha hare-hare daga masu tayar da kayar baya.
Najeriya
Najeriya ta sha hare-hare mafi muni daga masu ikirarin jihadi a yankin inda gwamnatin kasar ta gaza kwato yankin arewa maso gabashin kasar, wanda shi ne wurin da Boko Haram ta samo asali.
Kamar yadda rahoton kungiyar Global Terrorism Index ke cewa, Boko Haram ce ke da alhakin kashe fiye da mutum 37,000 a dalilin gumurzu, inda wasu 19,000 kuma saboda dalilan ta'addanci aka kashe su tun shekarar 2011, yawancinsu a Najeriya amma akwai wasunsu a kasashen da ke makwabtaka da ita.
A 2015 ne wani tsagi na Boko Haram ya yi wa kungiiyar IS mubayi'a, inda daga nan ya sauya suna zuwa "Lardin Yammacin Afirka na Daular Islama," wato Islamic State West Africa Province (ISWAP).
Tun wancan lokacin IS ta sha tallata wannan lardin na nahiyar Afirka da ta ke ikirarin yana cikin daularta.
Arewacin Afirka
Al-Qaeda ta fara bayyana ne a yankin arewacin Afirka cikin kasar Aljeriya.
Saboda haka babu mamaki sabon shugaban kungiyar da ta nada a yankin Maghreb dan Aljeriya ne.
Abu Obaida Al-Annabi mai shekara 51 da haihuwa ya gaji Abdelmalik Droukdel, wanda dakarun Faransa suka hallaka a Mali a watan Yuni.
Tunisia ce kasa mafi ƙanƙantar yawan al'umma a yankin, amma ita ce ta samar da 'yan sa kai tsakanin dubu 15 zuwa dubu 20 ta suka tafi Syria domin shiga kungiyar IS a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2018.
Rashin aikin yi da kusanci da Libya ya sa Tunisiya ta ci gaba da kasancewa cikin kasashe masu fuskantar barazanar fadawa cikin ayyukan ta'addanci.
Somaliya
Kungiyar al-Shabab ta Somaliya - wadda ke nufin "matasa" da Larabci - ta kasance kungiya mai matukar hatsari ta masu ikirarin jihadi a nahiyar Afirka baki daya.
Al-Shabab na kalon kanta a matsayin kungiyar da ta fi samun nasaraori cikin kungiyoyi masu alaka da al-Qaeda.
Tana nan da karfin ta duk da kokarin da gwamantoci suke yi na kayar da ita, kuma tana kai hare-hare cikin kasashen Kenya da Uganda har ma da tayar da manyan bama-bamai a Mogadishu, babban birnin Somaliya.
Mozambique
Sai kuma kungiyar da ke kiran kan ta "Islamic State Central Africa Province" (ISCAP), wada ke lardin Cabo Delgado na arewacin Mozambique.
Ita ce kungiyar da ta dauki alhakin kisan wasu kauyawa 50 a yankin Cabo Delgado, kuma ita ma na ikirarin cewa ta yi mubaya'a ga kungiyar IS.
Da alama yawancin wadanda aka shigar cikin kungiyar ta intanet ake samo su, yawanci daga Tanzania.
Kungiyar ta fara gagarar gwamnatin Mozambique, inda rahotanni ke cewa IS na iko da wasu yankuna ba tare da dakarun gwamnati sun iya yi mu su komai ba.
Kuɗin fansa
A watan Yunin 2013 dukkan shugabannin kungiyar G7 ta kasashe masu karfin tattalin arziki su ka kulla wata yarjejeinya a yayin wani taron koli da suka yi a Loch Erne cewa ba za su rika biyan kudin fansa ba ga kungiyoyin 'yan ta'adda.
Amma bayan shekara bakwai, gaskiyar lamarin shi ne 'yan ƙasashen Turai da aka yi garkuwa da su na samun 'yancinsu ne kawai bayan an biya kudin fansa, kuma 'yan kasashen Birtaniya da Amurka sun fi mutuwa a hannun kungiyoyin ta'addancin.
Masu nazari na cewa jimillar kudaden da aka biya kungiyoyin domin karbo wadanda suka yi garkuwa da su a arewaci da yammacin Afirka sun zarce euro miliyan 100 (dala miliyan 120m).
Wadannan ne kudaden da masu ikirarin jihadin ke amfani da su domin sayen makamai da bama-bamai da motoci na zamani da sauran kayan yaki da kuma ba jami'an gwamantoci cin hanci.
Babu mafita mai sauƙi
A ƙarshe tambayar ita ce shin lallai ne Afirka za ta zama cibiyar kungiyoyin 'yan ta'adda, da masu ikirarin jihadi ba Gabas ta Tsakiya ba nan gaba?
Amsar wannan tambaya za ta dogara ne kan abubuwa masu yaa amma babban su shi ne ingancin shugabancin da gwamnatoci ke iya samar wa al'umominsu.
Magance wannan matsalar na wani lokaci mai tsawo kuma wanda zai dore bai tsaya kan samar da jami'an tsaro ko sa ido kan iyakokin kasa-da-kasa kawai ba.
Batun yana nan kan tsohon kalubalen nan: samar wa al'umomin kasashen Afirka ayyukan yi masu gwaɓi da tsarin siyasa mai inganci da dorewa wanda sannu a hankali zai kawar da hankulan mutane daga afkawa cikin ayyuakn tayar da hankali da na ta'addanci.