Wainar da ake toyawa a Fadar White House bayan faɗuwar Trump zaɓe

.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Tara McKelvey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC White House reporter

A daidai lokacin da zaman Shugaba Trump na Amurka ke kawowa ƙarshe a Fadar White House, harabar fadar ta yi tsit duk da ƙoƙarin da shugaban yake yi na ƙalubalantar zaɓen ƙasar a kotu.

Brian Morgenstern, wanda shi ne mataimakin daraktan sadarwa, na sanye da wata rigar sanyi da kuma ƙyallen White House a ofishinsa da ke yammacin fadar. Rigar sanyin a rufe take har sama, tamkar yana kan hanyarsa ta fita.

Mai gidansa, wanda shi ne shugaban ƙasar, na wani sashe na Fadar White House ɗin. A lokacin, Shugaba Trump na kan waya da Rudy Giuliani, wanda shi ne ke jagorantar gabatar da ƙara kan zaɓen shugaban, da kuma wasu lauyoyin jihar waɗanda suka taru domin yin shawara.

"An yi maguɗi a wannan zaɓen, kuma ba za mu bari haka kawai ba," kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana ta waya.

Morgenstern na kallon tattaunawar ta kwamfutarsa, kuma kamar bai damu da abin da shugaban ke faɗa ba. Bayan lokaci kaɗan, sai ya juya kujerarsa inda ya yi magana da wani baƙonsa kan batun rukunin gidaje da makaranta, sai daga baya ya yi magana kan batun nasarorin da Shugaba Trump ya samu.

A ranar Juma'a ne aka tabbatar da rashin nasarar Trump a ƙarar da ya kai kan sakamkon zaɓen jihar Pennsylvania. Wani alƙali na kotun ɗaukaka ƙara ya bayyana cewa Mista Trump ɗin ba shi da wata hujja kan wannan iƙirarin nasa.

Sakamon zaɓe ya nuna cewa Joe Biden ya lashe zaɓen jihar da ƙuri'u 80,000.

An tabbatar da sakamakon zaɓen Arizona a ranar Litinin, inda ake tsammanin na Wisconsin nan ba da daɗewa ba - Joe Biden ya kayar da Trump a duka jihohin.

Tuni dai jami'an gwamnatin ƙasar suka fara shirye-shiryen miƙa mulki ga sabuwar gwamnati, kuma za a rantsar da sabon shugaban ƙasar a a ranar 20 ga watan Janairu.

.

Asalin hoton, Getty Images

Trump na ci gaba da ɓaɓatun shi ya ci zaɓe, amma wasu 'yan Fadar White House ɗin na kallon abubuwa yadda suke. Sun san cewa kwanakinsu sun zo ƙarshe dangane da zamansu a fadar.

Sun kuma san cewa idan mai gidansu ya kama hanyar faɗuwa, babban abu shi ne su ƙaurace masa.

Kusan kowane lokaci ofisoshin fadar a cike suke da mutane, ma'aikata na aiki kowane lokaci. Sai dai ban da yanzu.

Jack O'Donnell, wanda ya taɓa kula da wani gidan caca mallakar Trump a biranen Atlantic da New Jersey, ya bayyana cewa ya fahimci dalilin da ya sa mutanen da ke yi wa shugaban ƙasar aiki za su bar shi a irin wannan lokaci.

"Kuna tafiya kan ɓawon ƙwai, babu wanda ke so ya faɗi ba daidai ba."

.

Asalin hoton, Reuters

Jack O'Donnell, ya tuna da wani abin da ya taɓa faruwa a baya, inda wata rana Mista Trump ɗin na tafiya cikin wani ɗaki da silin ɗinsa bai da tsawo a wani gini da ake tsaka da gyara shi. "Akwai wasu matsaloli," in ji O'Donnell.

Yana alaƙanta matsalolin ne da gyaran gini, wasu kura-kuran da Trump ɗin ya lura cikin lokaci kaɗan.

"Sai ya yi tsalle sama ya naushi silin ɗin," in ji O'Donnell. "Babu wanda ke so ya tsaya kusa da shi idan ya yi fushi."

Mista Trump na da fushi matuƙa. Ya sha cin nasara sakamkon yadda yake ƙin yarda da rashin nasara, wanda wannan wani hali ne nasa na shugabanci da ya samo asali tun yana matashi.

Pro-Trump protesters in Atlanta

Asalin hoton, Getty Images