Ana matsa wa Musulmai lamba kan amincewa da al'adun Faransawa

Sallah a babban masallacin birnin Paris, 30 ga watan Octoba 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sallah a babban Masallacin birnin Paris
    • Marubuci, Daga Lucy Williamson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC a Paris

A cikin makon nan ne Majalisar Musulman ƙasar Faransa (CFCM) ke shirin ganawa da Shugaba Emmanuel Macron, don tabbatar da sabuwar ƙasidar ''dokar al'adun Faransa'' ga limamai a ƙasar don su rattaba hannu.

An bayar da rahoton cewa an buƙaci Majalisar ta (CFCM), wacce ta ƙunshi ƙungiyoyi daban-daban na Musulmai a ƙasar da su haɗa a cikin ƙasidar mai ƙunshe da dokar al'adun Jamhuriyyar Faransa, yin watsi da Musulunci a matsayin ƙungiyar siyasa da kuma hana tasirin ƙasashen waje.

"Dukkanninmu ba mu amince da ko mece ce dokar a'ladun Faransa da abin da ta ƙunsa ba,'' in ji Chems-Eddine Hafiz, mataimakin shugaban ƙungiyar ta CFCM kuma shugaban babban masallacin birnin Paris.

Amma kuma, ya ce, ''muna cikin yanayi na tarihin sauyi ga addinin Islama a Faransa kuma mu Musulmai na fuskantar nauyin da ya rataya a wuyanmu''. Shekaru takwas da suka gabata, ya ce, tunaninsa daban ne.

Ba da daɗewa ba ne wani mai tsattsauran ra'ayin addinin Islama Mohamed Merah ya ƙaddamar da hari a birnin Toulouse.

"Tsohon shugaban Faransa Sarkozy ya sa ni saukowa daga kan gado da misalin ƙarfe biyar na safe don tattaunawa a kai, Na faɗa masa: "Sunansa ka iya zama Mohammed, amma kuma mai aikata laifi ne! Ban so in riƙa haɗa aikata laifin da kuma addinina ba. Amma a yau, ina yi. Dole sai limaman Faransa sun yi aiki a kai.''

Tsarin shi ne ƙungiyar ta ƙirƙiri wani kundin rijista ga limaman a Faransa, wanda kowannensu zai saka hannu a kan dokar, kafin a tantance shi.

A watan Oktoba ne Shugaba Macron ya yi magana a kan yin ''matsin lamba'' kan shugabannin Musulmai. Amma kuma ƙasa ce ne mai wuyar shi'ani da take matuƙar son bambanta addinai da al'amuran gwamnati.

Mista Macron na ƙoƙarin dakatar da siyasar Musulunci ne, ba tare da an shaida cewa yana yin katsalandan a harkokin addini ba, ko kuma ware wani addini daban ba.

Haɗe duka ƙungiyoyin Muslmai wuri guda a cikin al'ummar Faransa ya kasance wani batu mai cike da sarƙaƙiyar siyasa a shekarun baya-bayan nan. Faransa na da ƙiyasin Musulmai kimanin miliyan biyar - ƙasa mafi adadin Musulmai marasa rinjaye a cikin ƙasashen Turai.

Olivier Roy, wata ƙwararriya a harkokin addinin Musulunci a Faransa ta ce dokar ta haifar da matsaloli biyu.

Ɗaya ita ce nuna wariya saboda kawai ta shafi masu wa'azin addinin Musulunci ne, kana ɗayar kuma 'yancin gudanar da addinin.

"An umarce ku da ku amince da waɗannan dokoki na ƙasa,'' ya shaida min, ''amma kuma ba a buƙaci ku nuna bambanci kan ƙungiyar LGBT mai goyon bayan kuwaɗi da maɗigo ba , misali ba a amince wa Cocin Katolika ya yarda da auren jinsi ba.''

Mai zayyane-zayyanen kayan ƙawa Iman Mestaoui na shan samun kalaman ɓatanci daga waɗanda ta kira ''masu nuna ƙiyayya'' - masu kaifin kishin Islama da ke cewa tsarin zayyanar ɗankwali da rawaninta ba kasafai suke iya rufe gashin mace yadda ya kamata ba.

Amma kuma, ta ce, batun umartar limaman na su rattaba hannu kan ''dokar al'adar Faransa'' matsala ce, bayan da ake kallon Musulmai waɗanda ba cikakkun 'yan kasar Faransa ba.

"Ya zama saka mu a wani yanayi da dole sai ka nuna wa mutane cewa ka yarda da al'adu da dabi'un kasar Faransa; inda za ka riƙa jin kai ɗan kasar Faransa ne, amma kuma ba ka jin Faransar a jikinka,'' ta bayyana.

Limami Hassen Chalghoumi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Limami Chalghoumi ya jagoranci alhinin malamin da aka datse wa kai Samuel Paty

"Muna jin kamar duk abinda muka yi - biyan haraji, ayyukan ''raya kasa'' - za su wadatar. Dole ka nuna cewa kai dan kasar Faransa ne; dole ka ci naman alade; sha barasa; kada ka saka hijabi, ka saka gajeren siket. Wannan ba daidai bane.''

'Masu tsattsauran ra'ayi - bama-bamai ne'

Amma Hassen Chalghoumi, limamin masallacin Drancy da ke wajen birnin Paris ya ce bayan shekarun da aka shafe ana kai harin ta'addanci, an tilasta wa gwamnati ɗaukar mataki.

Yanzu haka Mr Chalghoumi ya ɓoye kansa, bayan shan samun barazanar kisa kan ra'ayin a kawo sauyi da yake da shi.

"Dole sai da muka kai maƙurar fitowa mu nuna cewa duka kanmu a haɗe yake sosai, cewa muna mutunta doka,'' ya shaida min.'' Wannan shi ne sakamakon ya biyo baya saboda masu tsattsauran ra'ayi.''

Zanga-zanga ka dokar Faransa kan ska hijabi, Avignon, 3 ga watan Satumba 2016

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, " Ba tsokana ba ce, 'yancin da ke raina ne kawai'', Zanga-zanga ka dokar Faransa kan saka hijabi

A wajen babban masallacin birnin Paris, Charki Dennai ya iso don gabatar da sallah, yana matse da dardumar sallarsa da Alkur'ani mai girma a hammatarsa.

" Wadannan matasan masu (tsattsauran ra'ayi) tamkar wasu bama-bamai ne da aka dana,'' ya ce. '' Ina ga limaman kamar suna sausauta musu sosai. Za mu iya mutunta dokar kasar Faransa da kuma Musulunci, abu ne mai sauki. Abinda nake yi kenan.

Amma akwai ayoyin tambaya wane irin tasiri ne limamen ke da shi a kan matasan Musulmai, musamman idan ana batun tashin hankali mai nasaba da tsattsauran ra'ayi.

" Ba zai yi amfani ba,'' in ji Olivier Roy, " dalilan kuwa su ne: 'yan ta;'addanba sun zo daga masallatan Salafi bane. Idan ka duba tarihihn rayuwar 'yan ta'addan, babu daya daga cikinsu da suka fito daga indaake yin wa'azin Salafi " masu bin akidar Salafi na da tsattsauran ra'ayi, kungiyar masu kaifin ra'ayin da ake dangantawa da Musluncin siyasa.

Shawo kan matsalar matasan da aka yi watsi da su

Dokar daya daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnati ne na shawo kan matsalar tasirin ƙasashen waje, hana abkuwar tashin hankali da kuma barazana daga masu tsattsauran ra'ayi, tare da sake janyo hankalin matasa da ke ganin an mayar da su saniyar ware a ƙasar.

Mr Macron na tunanin ƙara bunƙasa koyar da harshen Larabci a makarantun ƙasar da ƙara zuba bunƙasa yankunan da suke koma baya, ya kuma tabbatar da cewa ya saka ƙafar wando daya da masu tsattsauran ra'ayi da suke ƙin amincewa da doka da al'adun Faransa, amma ba ɗaukacin Musulmai ba.

Bayanan bidiyo, Bidiyon abin da ya jawo ƙasashen Musulmai suka juya wa Faransa baya

Hakim El-Karoui wani ƙwararre ne kan ƙungiyoyin Musulmai na Faransa a cibiyar Montaigne da suka saba bayar da gudunmawa ga tunanin gwamnati.

Amma ya ce, ya kamata a saka Musulmai da kansu a cikin ayyukan gwamnati irin waɗannan, ''saboda za su iya bayar da gudunmawa wajen yadawa da kuma wayar da kan wani ɓangare na addinin Islama a shafukan sada zumunta - gwamnatin ta kasa yin hakan''.

Kuma ba tare da sa hannun ''Musulam da ke karkara ba", in ji Olivier Roy, zai yi wahala sabuwar dokar ta iya fara aiki.

"Mu yi tunanin a ce Musulman yankin su yanke shawarar ƙungiyar ta CFCM su sake naɗa nasu limamin,'' ya shaida min.

''Me gwamnati za ta yi? Ko mu sauya kundin tsarin mulki kuma mu haƙura da tsarin 'yancin yin addini ko kuma gwamnati ba za ta iya zaɓar wa al'umomin Musulmai limaman da ta tantance ba.''

A ɗakin ɗaukar hoton na birnin Paris, yayin da take ɗaukar hotunan sabuwar mujallarta, Iman Mestaoui ta shaida min cewa ta saka duka iyalanta kada wa Shugaba Macron ƙuri'a a zaɓen shekara ta 2017.

Tun daga wannan lokacin, ta lura da ''babban sauyi'' a samun ƴanci kan batutuwa da suka shafi tsaro da harkokin shige-da-fice.

"Na kasance me goyon bayan Macron," ta ce. "Ya kasance fatan da muke da shi a cikin al'umma, amma yanzu muna ganin an mayar da mu saniyar ware.''