Macron ya ba shugabannin Musulmin Faransa wa'adi su amince da 'tsarin ƙasar'

Asalin hoton, EPA
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nemi shugabannin Musulmai da su amince da abin da ya kira "tsarin mulkin Jamhuriyya" a wani ɓangare na yaƙar masu tsaurin kishin addinin Islama.
A ranar Laraba ya bai wa shugabannin Majalisar Ƙoli ta Musulmi a Faransa (CFCM) wa'adin kwana 15 ta amince da tsarin.
Dokar ta bayyana cewa Musulunci addini ne ba wata manufar siyasa ba, tare da haramta "katsalandan daga ƙasashen waje" a ƙungiyoyin Musulmi.
Wannan na zuwa bayan hare-haren ta'addanci da aka kai ƙasa da wata ɗaya.
Mista Macron ya kuma kare tsarin manufofin Faransa bayan hare-haren da aka kai da suka ƙunshi har da fille kan malamin da ya nuna wa ɗalibai zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad a aji a watan jiya.
A makon da ya gabata, shugaban da ministan harakokin cikin gida Gérald Darmanin, ya gana da shugabannin Musulmi a fadarsa ta Élysée.
"Wasu sharuɗɗa za a rubuta su cikin launin baƙi da fari (cikin kundin): wato ƙin amincewa da manufar siyasa a addinin Musulunci da kuma duk wani katsalandan daga wata ƙasa," kamar yadda wata majiya ta shaida wa jaridar Le Parisien bayan ganawar.
Wakilan majalisar Musulman ta CFCM sun kuma amince da kirkirar Majalisar Limamai ta Kasa, wacce za ta tantance malaman da ba su shaida a hukumance wanda kuma za a iya janye wa idan an saɓa sharuɗɗan.
Shugaba Macron ya kuma sanar da sabbin matakai na tunkarar abin da ya kira "Masu tawayen Islama" a Faransa
Matakan sun haɗa da wani ƙudurin doka da zai nemi haramta tsattsauran ra'ayi.
An gabatar da matakin a ranar Laraba kuma ya ƙunshi hana karatun gida tare da hukunci mai tsauri ga waɗanda suka razana jami'an gwamnati ta fuskantar addini.
Kowane yaro za a ba shi wata lambar shaida ƙarƙashin dokar da za a yi amfani da ita don tabbatar da suna zuwa makaranta. Iyayen da suka saɓa dokar za su iya fuskantar hukuncin ɗaurin watanni shida da kuma tara mai yawa.
Ƙudirin dokar, wanda kamfanin dillacin labaran AFP ya fara gani, kuma laifi ne ga wani ya bayyana bayanan wani ta hanyar da za a gano inda suke domin cutar da su.
Samuel Paty, malamin da aka kashe a wajen makaranta a watan da ya gabata, wata yekuwa ce a intanet ta haifar da kisansa a 16 ga Oktoba.
"Dole ne mu ceto ƴaƴanmu daga hannun masu kaifin kishin Islama," kamar yadda Mista Darmanin ya shaida wa jaridar Le Figaro ranar Laraba. Majalisar zartarwar Faransa za ta tattauna kan daftarin dokar a ranar 9 ga Disamba.
Kare Mujallu
A farkon wannan shekarar, Shugaba Macron ya bayyana addinin Islama a matsayin addinin "rikici" kuma ya kare ƴancin mujallu na wallafa zane-zanen da aka yi na nuna ɓatanci ga Annabi Muhammad.
Zane-zanen da aka ɗauka haramtattu a addinin Islama kuma abin ƙyama ga al'ummar Musulmi.
Bayan waɗannan kalaman, shugaban na Faransa ya zama abin ƙyama a yawancin ƙasashen Musulmi inda masu zanga-zanga suka yi kiran ƙauracewa kayayyakin Faransa.
A Faransa, ana bin tsarin boko zalla, kuma tsarin ƙasar.
Ƴancin faɗar albarkacin baki a makarantu da sauran wuraren taruwar jama'a da daga cikin tsarin ƙasar, kuma ƙoƙarin hana wannan don kare wani ra'ayin wani addini ƙasar na kallonsa a matsayin rusa haɗin kan ƙasa.
Faransa ita ce ƙasar da ta fi yawan Musulmi a ƙasashen Turai.












