Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Amurka na 2020: Shugabannin Larabawa za su fuskanci sabon yanayi bayan nasarar Biden
- Marubuci, Daga Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan tsaro
"Dole ne ku gafarce ni idan na ga kamar na ɗan shiga rudani," in ji jakadan Saudiyya a Burtaniya yayin da idonsa ya koma ga wayarsa. "Ina sa ido kan sakamakon da yake shigowa daga Wisconsin."
Kwanaki takwas kenan da suka gabata, lokacin da ba mu san wa zai kasance a Fadar White House ba a watan Janairu.
Lokacin da aka tabbatar da Joe Biden ne ya yi nasara, shugabannin Saudiyya a Riyadh sun ɗauki lokaci kafin su ce wani abu saɓanin lokacin da aka zaɓi Donald Trump.
Wannan ba abin mamaki ba ne: sun rasa babban amini a can sama.
Nasarar Mista Biden a yanzu na iya haifar da wani yanayi ga Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa na yankin Tekun Fasha.
Ƙawancen Amurka da yankin ya samo asali tun a shekarar 1945 kuma da alama zai ɗore, amma sauyi na zuwa kuma ga alama ƙasashen Gulf ba za su ji daɗin wasu sauye-sauyen ba.
Rasa babban amini
Shugaba Trump babban amini ne kuma wanda ke goyon bayan gidan Sarautar Sa'ud.
Riyadh Trump ya zaɓa a matsayin garin da ya fara kai ziyara zuwa wata ƙasa bayan lashe zaɓe a 2017.
Surukinsa, Jared Kushner, ya ƙulla wata babbar dangantaka mai ƙarfi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman.
Lokacin da duk hukumomin leƙen asiri na ƙasashen yammaci suka yi zargin Yarima mai jiran gado na Saudiyya yana da hannu a kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi a 2018, Shugaba Trump ya ƙi zarginsa kai tsaye.
Wani abin mamaki shi ne yadda tawagar Yarima mai jiran gado suka shaida wa mutane cewa "kada ku damu muna da wannan.|
Mista Trump kuma bijire wa kiraye-kirayen majalisa na neman hana sayar wa Saudiyya da makamai.
Don haka Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE da kuma Bahrain za su rasa babban amini a Fadar White House.
Abubuwa da dama ba za su sauya ba, amma ga wasu abubuwan da za su iya faruwa.
Yaƙin Yemen
Shugaban Amurka Barack Obama, wanda ƙarƙashinsa Mista Biden ya yi aiki matsayin mataimakin shugaban kasa a shekaru takwas, ba ya jin daɗin yaƙin da Saudiyya ke yi da ƴan tawayen Houthi na Yemen.
A lokacin da ya bar mulki, an ci gaba da luguden wuta ta sama kusan shekaru biyu ba tare da wata nasarar soja ba yayin da yaƙin ke haifar da babbar illa ga fararen hula da ƙadarorin ƙasar.
Saboda yaƙin, Shugaba Obama ya datse tallafin soji da na leƙen asiri da Amurka ke ba Saudiyya.
Amma gwamnatin Trump ta sauya wannan matakin kuma ta ba Saudiyya ƙarin goyon baya a yaƙin da take a Yemen.
Yanzu ga alama abubuwa za su sake sauyawa, inda Mista Biden a kwanan baya ya fada wa Majalisar Harkokin Hulda da Kasashen Waje cewa zai kawo "ƙarshen goyon bayan Amurka game da mummunan yakin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen tare da ba da umarnin sake duba alakar ƙasar da Saudiyya."
Matsin lamba daga gwamnati mai zuwa ta Biden kan Saudiyya da ƙawayenta na Yemen na kawo ƙarshen yaƙin za ta ƙaru.
Saudiyya da Daular Larabawa, sun fahimci a baya cewa wannan yaƙin ba zai ƙare ba ta nasarar soja kawai, inda suke neman hanyar da za su tsira wadda ba za ta bar ƴan Houthi kasancewa a yadda suke ba lokacin da aka fara yaƙin sama a watan Maris na 2015.
Iran
Babbar nasarar da Shugaba Obama ya samu a Gabas Ta Tsakiya ita ce yarjejeniyar nukiliyar Iran wacce ake kira JCPOA.
Wannan ya sa an ɗage wa Iran takunkumai domin ita kuma ta rage aikinta na ƙera makaman nukiliya tare da bada damar shiga cibiyoyin na nukiliya.
Shugaba Trump ya kira ta "yarjejeniya mafi muni" tare da ficewa daga yarjejeniyar.
Yanzu kuma wanda zai gaje shi yana da niyyar mayar da Amurka cikin yarjejeniyar.
Wannan ya taɓa Saudiyya. A Riyadh a ƙarshen shekara, bayan harin makami mai linzami da aka kai kan matatun mai na Saudiyya, na halarci taron manema labarai da Ministan Harkokin Waje na Masarautar, Adel al-Jubeir, wanda ya caccaki yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Bala'i ne, in ji shi, saboda ba a yi la'akari da (ba a taɓa nufin hakan ba) da faɗaɗa shirin makami mai linzami na Iran ko kuma yaɗuwar dakarunta a duk yankin Gabas Ta Tsakiya ba.
Yarjejeniyar baki ɗayanta, a cewarsa tana cikin rashin nasarorin gwamnatin Obama wanda bai taɓa tunanin barazanar gwamnatin musuluncin Iran ba.
Saudiyya da wasu ƙawayenta, sun yi murna tare da yaba wa Amurka da ta kashe kwamandan Iran Janar Qasem Soleimani a harin da ta kai watan Janairu da jirgi marar matuki.
Yanzu kuma sun damu ko gwamnati mai zuwa a fadar White House za ta nemi buƙata a Iran wanda kuma zai datse buƙatunsu.
Qatar
Qatar ta kasance gida kuma mai matuƙar muhimmanci ga ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon a Gabas Ta Tsakiya inda take da sansanin sojin Amurka na Al-Udeid.
Daga can ne, Amurka ke bayar da umurnin kai farmaki ta sama a Syria zuwa Afghanistan.
Amma duk da haka Qatar na fuskantar ƙyama daga makwabtanta Larabawa inda suke - Saudiyya da Daular Larabawa da Bahrain da Masar - dukkaninsu suna adawa da goyon bayanta ga fafutukar ƙungiyar ƴan uwa Musulmai ta Muslmin Brotherhood.
Matakin ƙauracewa Qatar ya fara aiki ne lokaci kaɗan bayan ziyarar Trump zuwa Riyadh a 2017, kuma ƙasashen sun yi tunanin ya ba su goyon baya.
Da farko an tursasa wa Trump goyon bayan matakin kafin a fayyace masa cewa Qatar ita ma aminiyar Amurka domin sansanin Al-Udaid yana da muhimmanci ga ma'aikatar tsaron Amurka.
Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden akwai yiyuwar zai ƙoƙarin sasanta saɓanin ƙasashen na Larabawa, wanda ba ya cikin buƙatu ko manufofin Amurka ko kuma abin su ƙasashen na Larabawa suke so.
Haƙƙin ɗan Adam
Yawancin kasashen Tekun Fasha ba su da kyakkyawan tarihi na keta haƙƙin ɗan adam.
Amma Shugaba Trump bai taɓa nuna shawa'arsa ba ga ƙawayensa na Larabawa game da batun.
Ya nuna cewa buƙatun Amurka da kasuwancinta sun sha gaban duk wasu buƙatu na kama mata masu rajin tabbatar da haƙƙin mata, da cin zarafin lebarori a Qatar.
Ko kuma batun watan Oktoban 2018 inda jami'an tsaron Saudiyya suka shiga jirgi zuwa Santanbul suka kashe babban ɗan jarida da ya yi fice wajen cacaccakar gwamnati Jamal Khashoggi tare da ɓoye gawarsa da har yanzu ba a gano ba.
Yana da wahala zaɓaɓɓen Shugaba Biden da gwamnatinsa su kasance masu yafiya.