Matar da ke yaƙi da masu safarar mata don yin karuwanci a Sicily

A Nigerian woman at a shelter for trafficked women in Sicily, Italy

Asalin hoton, Kate Stanworth

A cikin jerin wasiƙunmu da muke samu daga ƴan jaridar Afrika, a wannan karon Isma'il Einashe ya bankaɗo yadda matan Najeriya suka tashi tsaye wajen yaƙi da safarar mata a Italiya.

A saman wani tsauni a Sicily wata 'yar Najeriya na jan gora a yaƙin taimakon ceto mata kamar ta daga rayuwar karuwanci.

Osas Egbon ta buɗe wani gida na matan da suka samu kansu cikin matsalar safarar mata a tsibirin na Italiya a watan Janairu - irin shi na farko da ƴar Najeriya ta ƙirƙira.

Osas Egbon 'yar Najeriya a Sicily

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, An yi safarar Osas Egbon shekara 18 baya kuma burinta shi ne taimakon wadansu domin kar su faɗa cikin halin da ta samu kanta ciki

A yanzu ta tsugunar da mata huɗu da ke shekara 20, ɗaya ma tana da jariri - kuma tana fatan nan da karshen shekara wasu ƙarin biyu na nan tafe.

Cikin wani yammaci mai zafi, na ɗauki mota har zuwa ƙauyen da ta gina wannan gida - wurin na nesa da tsakiyar Palermo, inda za a iya ɓoye mata daga waɗanda suka tserewa.

Ƙarin wasu labaran da za ku so karantawa:

A wani ƙauyen Sicily gidan yake, ciki kuma da ƙatoton ɗakin dafa abinci, kowacce mace na da ɗaki ɗaya amma suna amfani da banɗaki da kicin guda.

Wata ƙawarta ce 'yar Italiya ta ba ta wurin da take zaune.

Da yawa daga cikin 'yan Italiya na da burin taimaka wa matar 'yar Najeriya, in ji ta, wannan na zuwa ne daidai lokacin ake samun ƙaruwar safarar mutane, shi yasa ƴan Italiya da yawa suke murna da wannan aikin nata.

Mummunan kisan kai

Na fara haɗuwa da Mis Egbon a 2018, shekara uku bayan ita da wasu mata ƴan Najeriya sun kafa wata ƙungiyar matan jihar Benin.

Tana taimaka wa mata da suka samu kansu a rikicin safarar mata zuwa Sicily - mafi yawansu sun zo daga jihar Edo a Najeriya, babban birnin Benin.

An kai Mis Egbon Italiya da zummar tilasta mata yin karuwanci tun tana shekara 18.

Street scene in Ballarò market, Palermo, Sicily in Italy

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Mafi yawan wadanda ake yin safarar tasu suna karewa da rayuwa ne a Ballaro da ke makwabtaka da Palermo

Ta yi ta ƙoƙari ta riƙa biyan wanda ya kaita - a yanzu kuma tana zaune cikin farin ciki da iyalanta a Palermo, amma tana da himmar ganin an dakatar da irin wannan rayuwar ƙasƙancin.

Ita da wasu ƙawayenta sun fara wannan yunƙurin ne bayan wani mummunan kisan kai da aka yi wa wasu mata biyu a karshen 2011 da kuma farkon 2012.

Kuma ɗaya tana shekara 20 ɗayar kuma tana 22.

Wannan kisan kai ya matuƙar girgiza mutane a Sicily, ya kuma haskaka cin zarafin da ake yi wa matan Najeriya da ake tilasta wa karuwanci.

Lamarin safara ba wani baƙon abu ba ne, amma abin damuwar shi ne yadda adadin yake ninkawa tun daga 2015.

Kamar yadda hukumar kula da ƴan gudun hijira ta duniya ta bayyana, a 2016, mata 'yan asalain Najeriya 11,000 aka yi wa rijista sun sauka a Sicily, kuma kashi 80 cikinsu an yi safarar su ne, wadanda a karshe ake tilasta musu yin karuwanci.

Da zarar matan sun sauka, za su fara biyan basukan da wadanda suka kai su ke binsu - wanda yake kai wa dalar Amurka 35,000 - ta hanyar yin karuwanci kuma duk da haka karshe suna karewa ne da bashi a kansu.

'Rantsuwa da Juju'

A Palermo matan a lokuta mafi yawa suna ƙarewa ne da zama a Balloro, inda ake matsa musu su yi aiki kan abin da ake kira "mu'amalar gidaje" da kuma ta tsofaffi ko kuma aiki a kan tituna.

The silhouette of a woman at a shelter for Nigerian women in Sicily, Italy
Kate Stanworth
The traffickers prey on the women's spiritual beliefs so they become too afraid to speak up, fearing if they do so harm will come to them or loved ones back home"
Ismail Einashe
Journalist
1px transparent line

Kafin su isa Italiya duka matan sai an matsa musu sun yi rantsuwa da juju (wani abu mai tamkar ubangiji a gare su) domin riƙe su kan alƙawarinsu ta yadda ba za su iya bijirewa ko kuma su shigar da ƙarar wadanda suka kai su zuwa ga 'yan sanda, za su yi biyayya ga "Magajiyar karuwan da aka haɗa su tare'' kuma dole su biya cikakken bashin da ake bin su.

Za kuma a yi wa matan asiri da abin da suka yi imani da su, ta yadda za su riƙa jin tsoron su yi magana, tare da jin idan suka saɓa ƙa'idar da suka amince da ita wani mugun abu zai shafe su ko kuma waɗanda suke ƙauna.

A wurin Mis Egbo wannan rantsuwar da suke yi ita ce babbar koma bayan da ke hana matan samun 'yanci daga gungun masu safarar mutanen.

Shekara biyu da suka gabata, ita da ƙawayenta sun yi ta samun goyon bayan Oba na birnin Benin, ɗaya daga cikin masu faɗa a jin a cikin shugabannin Najeriya, lokacin da ya yi muguwar addu'a ga masu safarar.

Oba Ewuare II na ƙasar Benin, wanda ya tsinewa masu safarar a 2018

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Oba Ewuare II na ƙasar Benin, wanda ya tsinewa masu safarar a 2018

A lokacin an ta liƙa fastosi a Palermo kan labarin sanarwar.

Tun daga lokacin Mis Egbon ta fara samun sauƙi wurin kan samun lamarin mata kuma hakan ya taimaka mata wajen kuɓutar da su.

'Buri ya cika'

Mata a birnin Benin suna kai ziyara tsakiyar inda matan suke, suna ba su shawara, abu mafi muhimmanci nuna damuwa kan yanayin da suke ciki, yanda ke janyo guduwarsu daga inda suke.

Yadda hoton Palermo yake a Sicily da ke Italy

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Matan Benin na kai ziyara birnin Ballarò

Masu aikin sa kai a wurin sun fahimci alaƙar karuwancin da ke tsakanin matan da masu safarar tasu, wanda hakan ke zama wata hanya ta haka suke tserewa.

A gidan da take ajiye matan, Mis Egbon ta ce tana son ƙarfafa wa matan gwiwa ta hanyar ba su damar yin karatu saboda mafi yawansu yara ne - za ta kai su azuzuwan da za su taimaka musu samun aiki da sun kammala.

Tana barin matan su zauna tare da ita ne na tsawon shekara guda domin su dan farfaɗo daga damuwar da suke shiga, sannan kuma su nufi rayuwarsu ta gaba.

Wata 'yar Najeriya na yi wa 'yar uwarta kitso

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Matan da ke zaune a gidan na jin suna da amince kuma suna rayuwa ne cikin farin ciki - wanda hakan ke basu damar farfaɗowa daga damuwa da suke samun kansu ciki.

A wurin Mis Ebgon, wadda ta zama uwa kuma ta zama tamkar wata jami'ar wayar da aki ga matan, samar da wannan gida wani ɓangare ne na cikar Burinta.

Amma bayyana abubuwan da suke gudana a wurin yana da wahala, saboda tana tafiyar da wurin ne daga tallafin da take samu daga mutane.

Kungiyar ƴan Najeriya mazauna Palermo suna ɗan tattara abin da za su iya bayarwa su aika mata, haka su ma coci-coci suna aikawa da nasu tallafin.

A yinin da na yi a wannan gidan a ɓoye, na fahimci matan suna zaune cikin aminci kuma cikin farin ciki - kuma sukna warkewa daga damuwar da suka samu kansu ciki.