Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Amurka 2020: Mai zai faru idan ɗan takara ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓe?
Menene zai faru idan ɗan takara ya yi inkarin sakamakon zaɓe? kuma mai ya sanya ƙuri'un wasu johohin suka fi na wasu muhimmanci?
Ga wasu muhimman tambayoyi game da zaɓen kasar Amurka tare da amsoshinsu.
Shin Trump na ƙoƙarin ƙin amincewa da sakamakon zaɓe ne? - Tambayar Basel, Isra'ila
Eh. Duka ƴan takarar sun ce sun shirya tsaf domin neman matakan shari'a bayan zaɓen.
Tawagar yaƙin neman zaben Trump na ja da sakamakon zaɓen wasu manyan jihohi, da suka haɗa da Nevada da Georgia da Pennsylvania da kuma Michigan.
Suna da haƙƙin neman a sake ƙirga ƙuri'un a mafi yawan jihohi, musamman idan sakamakon ya yi kusa da kusa.
An samu ƙaruwar jefa ƙuri'a ta gidan waya a wannan shekara, kuma da yiwuwar a ƙalubalanci ingancin wadannan ƙuri'u a kotu.
Kuma bibiyar sahun shari'a zai iya kai su har ga kotun ƙolin Amurka - ƙololuwar shari'a kenan a Amurka.
Hakan ya faru a 2000, yayin da kotun ƙoli ta dakatar da ƙirga ƙuri'a a jihar Florida, ta kuma yi hukuncin da ya yi wa jam'iyyar Republican daɗi, wanda karshe ya bai wa George W Bush damar zama shugaban ƙasa.
Mai zai faru in abubuwa suka cakuɗe? - Tambayar Chinga, China
Akwai kuri'ar wakilai 538 da ake jiran a kawo, da kuma adadin wasu wakilai da ke wakiltar jihohi.
Wanda hakan ke nuna da yiwuwar ƙarfi ya zo ɗaya a mazaɓu 269, duk da cewa hakan na da wuya.
Idan babu ɗan takarar da ya lashe kuri'ar wakilai, lamarin zai koma hannun majalisar dokokin Amurka su yanke hukunci.
Mambobin majalisar da aka zaɓa a 2020 su ne ke da wannan alhaki.
Majalisar wakilai za ta yi zaɓe domin tabbatar da shugaban ƙasa, ko wanne wakilin jiha zai zama yana da ƙuri'a daya - wanda ya samu ƙuri'a 26 ta mafi yawa shi ne zai zama shugaba.
Su kuma majalisar dokoki su zabi mataimakin shugaban ƙasa, kuma duka sanatoci 100 sai sun yi zabe.
Wanne tasiri kuri'un jama'a ke da su kan kuri'un wakilan masu zaɓe? - Caroline Bonwitt, Gloucestershire, Birtaniya
Shugabannin ƙasar Amurka na darewa kujera ne ba da yawan ƙuri'un jama'a ba, amma da lashe wani kaso mai yawa na kuri'un a jihohi.
Wanda ya lashe zaben ko wacce jiha zai samu goyon bayan wakilan masu zabe, ya danganta da yawan mutanen jihar.
Wadannan wakilan zaɓen za su haɗu a makonni bayan ranar zaɓe, da za su yi zaɓen ƙarshe domin tabbatar da shugaban ƙasar na gaba.
Domin lashe zaben fadaar White House, akwai buƙatar kuri'a 270.
Su wanene mambobin wakilai na musamman, ta yaya ake zaɓar su, har zuwa yaushe suke wannan aiki? - Tambayar Penny Reid, Northumberland, Birtaniya
A mafi yawan lokuta jam'iyyun Republican da Democrat ne ke zaɓar wadannan mambobi na musamman yayin ko wanne zaɓe.
Akwai dokoki mabambanta wajen ba da su daga ko wacce jiha, kuma ana zabarsu ne a hukumance a ranar zabe.
Wakilai na musamman - suna da alaƙa da jam'iyyun siyasar Amurka, yawancinsu masu fafutuka ne ko kuma tsofaffin 'yan siyasa.
A 2016, Bill Clinton na cikin wakilai na musamman daga jam'iyyar Democrat, shi kuma Trump karami daga Republican.
Menene zai tantance makomar shugaban ƙasa idan wakilai na musamman suka gaza fitar da wanda ya lashe zabe? - Tambayar Robert Pallone, Maryland
Idan wakilai na musamman suka gaza fitar da wanda ya lashe zabe, hakan na nufin an yi kankankan a sakamakon zabe kenan, ko kuma an kasa shawo kan kalubalen rikicin da ake fuskanta a jihohi a shari'ance, kuma ba za su iya zabar wakilan zabe ba.
Wakilai na musamman - wadanda kuma aikinsu shi ne fitar da shugaban ƙasa - za su haɗu a ranar 14 ga watan Disambar wannan shekarar.
Dole ne ko wacce jiha ta ba da sunan wakilinta na musamman domin dan ɗan takararta ya samu damar lashe zabe.
Idan aka samu rikici a sakamakon zaɓe kuma wasu jihohin suka gaza fitar da wakilansu na musamman, to a nan haƙƙin majalisar dokokin Amurka ne ta shigo ciki.
Kundin tsarin mulkin Amurka ya sanya lokaci na ƙarshe ga tawagar shugaban kasa da mataimakinsa, ranar 20 ga watan Janairu domin ruguje su.
Me ya sanya kuri'un wasu jihohi ke da muhimmanci sama da wasu ? - Tambayar Robertson, Sussex, Birtaniya
'Yan takarar da suka yi yakin zabe a jihohin da sakamakonsu ba shi da tabbas - shi yasa mutanen ke ganin kuri'un wasu jihohin sun fi na wasu muhimmanci.
Irin wadannan ake kira fagen yaƙi a neman zaɓen Amurka.
A jihohin da ake da tabbaci kan tsarin zabensu - kamar California ga jami'iyyar Democrat ko kuma Alabama ga Republican - masu takara masu bukatar yin kamfe da yawa.
Sai su mayar da hakalinsu ga sauran jihohin - kamar su Florida da Pennsylvania, domin neman goyon bayan masu zaben da za su iya zabar kowa.
Idan aka kammala ƙirga kuri'un da aka kaɗa ta gidan waya bayan kwanaki sai aka samu sauyin kan sakamakon karshe wadannane hanyoyi ake bi domin sanar da wanda ya lashe zabe? - Charlie Etheridge, Kent, Birtaniya
Babu wani tanadi a shari'ance kan yadda za a sanar da wanda ya lashe zabe, wannan abu ne da mafi yawan kafafen yaɗa labaran Amurka ke yi.
Ko da ba a kammala kiɗayar kuri'un ba - amma aka samu wanda ya cika kuri'un da ake so, to za a bayyana wanda ya yi nasara.
A wannan shekarar sai kafafen yaɗa labaran Amurka sun yi taka-tsantsan wajen bayyana wanda ya yi nasara, saboda yawan kuri'un da aka kaɗa ta gidan waya wanda zai iya kara tsawaita lokacin bayyana sakamakon.