Manyan matsaloli takwas da suka fi addabar yankin arewacin Najeriya

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau

A ranar Litinin 2 ga watan Nuwamba gwamnonin jihohin arewacin Najeriya guda 19 suka taru a Kaduna domin tattauna matsalolin da suka shafi yankin da kuma nemo mafita.

Matsalolin tsaro da rashin aikin yi da yaɗa labaran ƙarya a shafukan sada zumunta na daga cikin abubuwan da suka ce na addabar yankin a cikin sanarwar bayan taro da suka fitar.

Sai dai masu sharhi sun soki gwamnoni kan rashin bayar da fifiko wajen magance matsalolin inda a maimakon hakan suke ɓugewa da kalaman fatar baki.

BBC Hausa ta tuntuɓi wasu masana game da manyan matsalolin da suka fi addabar yankin, inda suka bayyana matsala takwas daga ciki kamar haka:

Talauci

Kabiru Sa'idu Sufi, mai sharhi kan lamuran yau da kullum kuma Malami a kan harkokin siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, ya ce talauci ne babbar matsalar da ta fi addabar arewacin Najeriya a yanzu idan aka kwatanta da ɓangaren kudanci.

"Matsalar tattalin arziki ce ta ɗaya a Arewa idan aka kwatanta da Kudu, saboda ƙididdiga ta nuna cewa talauci ya fi yawa a Arewa ɗin," in ji shi.

"Idan kana tahowa daga Legas ko Fatakwal za ga kana kusanto Arewa kana ƙara ganin bambancin tattalin arzikin."

Game da hanyoyin da za a bi wurin maganin matsalolin, masanin kimiyyar siyasar ya ce sai an samar da yanayin da matasa za su ƙirƙiri harkokin kasuwanci da kansu.

"Lallai sai an ƙirƙiri masana'antu na zamani kamar na harkar sadarwa da sauransu, kar a dogara da harkar saye da sayarwa kawai."

Ya ƙara da cewa "shi kansa saye da sayarwar da akwai kuɗi a hannun jama'a zai inganta sosai, saboda haka wajibi ne gwamnati ta samar da wasu hanyoyi ta yadda matasa za su iya buɗe harkokin kasuwanci da kansu".

Matsalar tsaro

Hare-haren ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da 'yan fashin daji na cikin matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya.

Kabiru Sufi ya ce matsalar tsaron ta addabi fannoni daba-daban musamman noma saboda akasarin mutanen yankin Arewa manoma ne.

Ya ƙara da cewa idan dai ana so a kawo ƙarshen matsalar sai an bi matakai masu gajeren zango da masu dogon zango.

"Daga cikin matakai na gajeren zango, sai gwamnati ta samar wa jami'an tsaro kayan aiki na zamani sannan kuma sai kowa ya shigo cikin harkar tsaro, kamar kafa ƙungiyoyin sa-kai.

"Na dogon zango kuma, wajibi ne a gyara tare da samar da masana'antu domin bai wa matasa aikin yi saboda su daina shiga ciin ƙungiyoyin 'yan bindiga."

Shan miyagun ƙwayoyi

Kabiru Dakata wani ɗan gwagwarmaya ne da ke aiki da ƙungiyoyin farar hula da na matasa a Najeriya, ya ce akwai bambanci tsakanin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da matasa ke yi a kudancin Najeriya da kuma na arewaci.

Hasali ma ɗan gwagwarmayar ya yi zargin cewa da yawan ƙwayoyin da ake sha a arewacin Najeriya baƙi ne suke shiga da su jihohin amma ba sa kai wa yankinsu.

"Wajibi ne sai mun yarda cewa ɗa na kowa ne, ba zai yiwu mutane su riƙa tunanin cewa ba za su tsawatar wa 'ya'yan maƙwabtansu ba idan suna shaye-shaye saboda kar su yi musu rashin kunya," in ji Dakata.

"Shaye-shayen su ne suke haifar da wasu matsalolin kamar faɗan daba da ƙwace. Sukan tare hanya domin yi wa mata ƙwace da sace-sace saboda su sayi kayan shaye-shaye da kudin."

Jahilci

Malam Kabiru Sufi na ganin akwai jihohin da suka kamata su sanya dokar ta-ɓaci a kan harkar ilimi a Arewacin Najeriya.

"Ina ganin akwai jihohin da ya kamata su saka dokar ta-ɓaci a kan harkar ilimi. Ai ƙirƙirar masana'atun ma sai da ilimi zai yiwu, abokan zamanmu suna ta ƙirƙire-ƙirƙire," in ji Kabiru Sufi.

Game da ilimin mata, malamin Kwalejin ya ce shi kansa tattalin arzikin idan mata suka samu zai fi bunƙasa.

"Sai an duba an gano irin iliman da ba mu da su sannan a samar da makarantu da kuma inganta su saboda waɗanda muke da su a yanzu kamar ba makarantu ba."

Rashin kishin kai

Ɗan gwagwarmaya Kabiru Dakata na ganin rashin kishin yankin Arewa da 'yan siyasar yankin ke nunawa na taka rawa wurin ƙara yawan matsalolin da ke addabar mazauna yankin.

"Misali, sai ka ga a cikin mataimaka na musamman na 'yan majalisun tarayya har da waɗanda ba 'yan Arewa ba."

Ya ƙara da cewa akwai wasu damarmaki da wasu ministoci ke samu amma ƙalilan ne ke ɗibar 'yan yankinsu.

"Babbar hanyar da za ta taimaka a shawo kan matsalar ita ce, sai 'yan jarida sun fara bincike tare da gano sunaye da adadin hadiman 'yan majalisar na jihohin Arewa.

''Idan aka gano a cikinsu akwai wasu da ba 'yan yankin ba sai a yayata shi domin mutane su sani.

Yawan yaran da ba sa zuwa makaranta

Haka nan, Kabiru Dakata ya alaƙanta matsalolin tsaro da yaran da ba sa zuwa makaranta, waɗanda bincike ya nuna suna da yawa a arewacin Najeriya.

"Yaran da ba sa zuwa makaranta, su ne waɗanda aka fi saurin saka su cikin ƙungiyoyin 'yan ta'adda da kuma 'yan daba."

'Dalilai na addini'

Ta'addanci

Dr. Mansur Isa Yalwa, Shugaban Sashen Shari'ar Musulunci na Jami'ar Bayero ta Kano, ya ce matsalar ta'addanci ce ta fi damun arewacin Najeriya a yanzu bisa dalilai na malamai da mabiyansu.

"Wannan matsala ta ta'addanci na faruwa ne sakamakon wasu malamai da suka fara fahimtar addinin amma ba su fahimce shi daidai ba ko kuma suna sane suka ɓatar da matasa daga yadda ya kamata a yi addini," in ji shi.

"Ba a yin addini da zafin kai, ba a yin addini da zafin rai da cewa idan abubuwa sun cukwikwiye a rama ta wannan hanya. Sai dai ta hanyar ilimi da fahimta."

Malamin jami'ar ya ce hanyar da za a bi wurin kawo ƙarshen wannan matsala ita ce, wajibi ne matasa su fahimci cikakkiyar fassarar addini ingantacciya ba wai ra'ayinsu ba.

Rashin bin addinin Musulunci sau da ƙafa

Dr. Yalwa ya ce "addinin Musulunci a cike yake domin kuwa Alla Ya ce ya cika addininsa", saboda haka ne ya ce "yana ɗaya daga cikin matsalolin da ke damun Arewa yadda Musulmi ke yin koyi da wasu".

"Misali a ɓangaren siyasa, akwai abin da ya dace da addini akwai wanda bai dace ba. Ya kamata mutum ya nemi abin da addinin ya ce a kanta. Haka ma a fannin tattalin arziki.

"Idan mutane za su yi addini to su yi addini, idan kuma za su bar addini to su bar addinin gaba ɗaya.