Zaɓen Amurka 2020: Ko Trump ya sha kaye a zaɓen Amurka, ya riga ya sauya duniya

    • Marubuci, Daga Rebecca Seales
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 6

Duk wani shugaban Amurka ba wai yana shugabancin kasarsa kawai ba ne, ana kuma kallonsa a matsayin mutumin da ya fi kowa karfin fada a ji a duniya, Trump bai tsira ba, don haka duk abin da ya yi, na iya sauya rayuwar jama'a.

Yadda duniya ke kallon Amurka

Shugaba Trump ya sha bayyana Amurka a matsayin kasar da ta fi kowacce karfin fada a ji a duniya, sai dai wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da Pew Reserch ta gudanar ta nuna cewa shugaban bai yi wani abin a zo a gani ba, wajen ɗaga martabar kasar a idon duniya.

A kasashen turai da dama, adadin mutanen da ke kallon Amurka da kima ya yi irin raguwar da bai taba yi ba tun tsawon shekaru ashirin da suka gabata.

A Birtaniya kaso 41 na 'yan kasar ne ke kallon Amurka da daraja, a Faransa kaso 31, a Jamus kuma kaso 26.

Yadda Amurka ke yaki da annobar korona ya taka muhimmiyar rawa kwarai wajen rage martabarta a idon duniya, domin kaso 15 cikin 100 ne kadai ke ganin kasar ta bi hanyar da ta kamata wajen shawo kanta, kamar yadda alkalumma suka nuna.

Yadda Amurka ta ja baya kan sauyin yanayi

Abu ne mai wuya ka iya cewa ga manufar shugaba Trump game da sauyin yanayi, saboda yadda ya rika raina al'amarin, ya sha kiran sauyin yanayi a matsayin camfi,

Ya firgita masana kimiyya ta hanyar sanar da ficewar Amurka daga yarjejeniyar canjin yanayi ta Paris, wacce ta sanya kusan kasashe 200 kiyaye yanayin zafin duniya.

Amurka ita ce kasa ta biyu mafi girman fitar da hayaki mai gurbata yanayi bayan China, kuma masu binciken sun yi gargadin cewa idan aka sake zaben Mista Trump, zai yi wuya a iya kiyaye yanayi.

Da yake kin amincewa da yarjejeniyar ta Paris, shugaban ya yi ikirarin cewa sharuddan yarjejeniyar na iya kawo cikas ga kamfanonin Amurka.

Yawancin wuraren hakar ma'adinan kwal na Amurka har yanzu na rufe, kodayake, sakamakon gasa tsakanin kamfanonin da ke sayar da iskar gas a rahusa, da kuma kokarin da kasar ke yi wajen karfafa guiwar bangaren makamashi alkaluman gwamnati sun nuna cewa ana samun ci gaba.

Ficewar Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris a hukumance ta fara aiki a ranar 4 ga Nuwamba, washegari bayan zaben shugaban kasa.

Joe Biden ya yi alkawarin sake shiga yarjejeniyar idan ya yi nasara.

Ficewar Amurkan na ci gaba da haifar da sakamako mai muni, ko da yake wasu masu lura da al'amura na ganin cewa ta sassauta hanyar zuwa Brazil da Saudiyya don toshe ci gaban da aka samu game da fitar da hayakin carbon.

Rufe iyakoki da wasu kasashe.

Shugaba Trump ya tsaurara iyakokin kasar mako guda bayan rantsar da shi.

Ya rufe kan iyakokin Amurka ga matafiya daga kasashe bakwai da Musulmi suka fi yawa.

A yanzu haka kasashe 13 na karkashin tsauraran matakan takaita zirga-zirga.

Adadin mutanen da aka haifa a kasashen waje da ke zaune a Amurka ya kai kusan kashi 3 a 2019 fiye da na 2016, shekarar Shugaba Obama ta karshe a kan mulki.

Adadin mazauna Amurka da aka haifa a Mexico ya rika yin kasa sannu a hankali a lokacin mulkin Mista Trump, yayin da adadin da suka haura daga wani wuri a Latin Amurka da Karebiyan ya karu.

An kuma takaita yawan biza da ke ba mutane damar zama na dindindin a Amurka, musamman ma dangin waɗanda ke zaune a can.

Idan ana maganar manufar shugaba Trump game da iyakokin kasarsa da makwabta, ba shakka za a yi batun (Katanga) da ya yi alkawarin ginawa a iyakar kasar da Mexico.

Ya zuwa ranar 19 ga Oktoba, hukumar kula da shige da fice ta Amurka ta ce an gina katanga mai nisan mil 371.

Adadin bakin haure da aka tsare a kan iyakar Amurka da Mexico ya kai adadin da bai taba kaiwa ba a shekarar 2019, wanda hakan ya haifar da karuwar masu zuwa a lokacin bazara.

Fiye da rabi sun kasance iyalai, galibi daga Guatemala, Honduras, da El Salvador, inda tashin hankali da talauci ke sa mutane neman mafaka da sabuwar rayuwa a wasu wurare.

Karuwar labaran boge

"Ina ganin yawancin abubuwan da nake cin karo da su karya ne'' in ji Donald Trump a wata hira a watan Oktoban 2017.

Ko da yake tabbas shugaban bai kirkiro bayanin "labaran karya ba", amma ya dace a ce ya kara fito da kalaman.

Dangane da sakonnin da yake watsawa a kafofin sada zumunta da kuma bayanan sauti da shafin Factba.se ke lura da su, ya yi amfani da kalmar kusan sau 2,000 tun lokacin da ya fara rubuta wa a watan Disamban 2016.

Je ka Google ka rubuta "fake news", wato labaran karya, za ka ga sakamako kusan biliyan daya daga dukkanin sassan duniya, yawancinsu daga Amurka.

Yayin zaben Amurka na 2016, kalmar na nufin labaran da ba na gaskiya ba, kamar labarin da ke cewa Fafaaroma ya goyi bayan Trump a matsayin shugaban Amurka na 2016.

Shugaba Trump ya sha amfani da kalmar wajen sukar kafafen watsa labarai, a shekarar 2017 ya kama sunan wasu kafofin watsa labarai da dama da ba ya jituwa da su, in da ya bayyana su a matsayin masu watsa labaran karya.

Nan take shugabannin wasu kasashe kamar Thailand da Philippines da Saudiyya suka karbi wnanan kalma tare da fara amfani da ita, wajen kare laifukan da ake zarginsu da aikatawa na take hakkin jama'a.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce ta hanyar amfani da wannan kalma ga sahihan labarai na kawo cikas ga dimukradiyya, wadda ta dogara a kan yadda jama'a ke gamsuwa da yadda bayanai suke.

Yakin da Amurka ke yi a gabas ta tsakiya

Yayin da yake gabatar da jawabinsa ga 'yan kasa a shekarar 2019, shugaba Trump ya yi alkawarin kwashe dakarun Amurka daga gabas ta tsakiya, yana cewa ''Manyan kasashe ba sa shiga yaki mara iyaka."

Shugaba Trump ya yi abin da shugabannin da suka gabace shi suka kaucewa yi, ta hanyar mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Jerusalem daga Tel-Aviv a shekarar 2018, da kuma amincewa da birnin a matsayin na Isra'ila.

A ajiye martanin da kasashen duniya suka yi, wannan shi ne ci gaba mafi girma da gwamnatin Trump ta samu dangane da manufofinta na kasashen waje.

A watan da ya gabata gwamnatin Trump ta soma cimma wata gagarumar nasara ta inganta alakar Isra'ila da wasu kasashen musulmai, ciki har da hadaddiyar daular larabawa da kuma Bahirain, sai kuma Sudan a baya-bayan nan.

A shekarar 2019, dangantakar kasuwancin kayayyaki tsakanin Amurka da China ta yi kasa idan aka kwatanta da 2016.

Kamfanonin Amurka sun fitar da kaya marasa yawa daga Amurka zuwa China domin gudun kada shugaba Trump ya kakaba musu haraji.

To sai dai duk da annobar korona, kayayyakin da Amurka ke fitar wa sun fi wadanda ta ke shigo da su yawa nesa ba kusa ba.

A ranar 2 ga Disambar 2016, Mista Trump wanda shi ne zababben shugaban kasa na wancan lokacin, ya dauki matakin da ba a saba gani ba na yin magana kai tsaye ga shugabar Taiwan - inda ya karya dokar da aka amince da ita ta yanke kawance da kasar a shekarar 1979.

Carrie Gracie, wadda a lokacin ita ce Editar BBC a China, ta yi hasashen matakin zai haifar da "firgita da fushi" a Beijing, wacce ke ganin Taiwan a matsayin wani lardin China ba wata kasa mai cin gashin kanta ba.

Amurka ta dauki matakai da dama a kan China bayan lalacewar alakarsu, da suka hadar da sanya haraji a kan kayanta, da dakatar da sauke manhajar TikTok da WeChat, da kuma sanya wa kamfanonin sadarwar China haraji.

Shugaba Xi Jinping na China, da ke kan karagar mulki tun daga 2013, ya jagoranci wata dokar tsaro da ake ta takaddama a kanta a Hong Kong, da kuma daurin talala ga Musulmai tsiraru na Uighurs, abin da Amurka ke adawa da shi.

Shugaba Trump ya sake sanya wa cutar korona sunan "kwayar cutar kasar Sin", domin a cewarsa, sakacin kasar ne ya janyo yaduwar cutar a fadin duniya.

Sauran kiris Amurka ta shiga yaki da Iran

Ba shakka Iran za ta dandana kudarta ga duk ran wani ba'amurke da ya rasa ransa, "Babban sakamako ma kuwa", wannan ba gargadi ba ne, barazana ce ga Iran, a cikin wani sako da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na tuwita, a farkon shekarar 2019.

Kwanaki kadan daga bisani Amurka ta razana duniya, ta hanyar hallaka babban Janar din sojan Iran wato Janar Qaseim Sulaimani, wanda ke jangorantar ayyukan sojin Iran a kasashen duniya, ta hanyar harba gwamman makaman roka kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagadaza da ke kasar Iraqi, abin da ya janyo barazanar yaki tsakanin kasashen biyu.

Ba a yi yakin ba, amma gwamman mutane da ba su ji ba su gani ba sun mutu, awanni kadan bayan da Amurka ta harba makamanta a matsayin wani martani, inda cikin kuskure ta kakkabo wani jirgin fasinjan Ukraine da ke balaguro.

Ya akai har ta kai ga haka? Abubuwa da dama sun faru a kashin gaskiya, fushi, kokarin ramuwar gayya, da kuma son yayyafawa zukatan Iraniya ruwa.

Kasashen Amurka da Iran na fama da tsamin dangantaka tun shekarar 1979, lokacin da Amurka ta goyi bayan Shah, tsohon sarkin kasar da aka hambarar, an yi garkuwa da wasu Amurkawa tare da boye su a ofishin jakadancin Amurka da ke Iran a watan Mayun 2018.

Shugaba Trump ya mayar da martani ta hanyar ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan Iran a 2015, wadda a cikinta Iran ta amince ta iyakance shirinta na mallakar makamin nukiliya, yayin da ita kuma Amurka za ta janyo takunkuman da ta kakabawa Iran.

Bayan ficewa daga yarjejeniyar ne kuma shugaba Trump ya sanya wa kasar wasu jerin takunkumai da ya kira mafiya tsauri, domin ta amince da wata sabubuwar yarjejeniya da yake son a cimma.

Iran ta ki ta bada kai bori ya hau, abin da ya janyo fadawarta cikin matsalar tattalin arziki, abin da ya sa a shekarar 2019 farashin yakan abinci ya yi sama da kaso 61.

Wasu 'yan Iran sun kwarara a kan titunan kasar suna zanga-zanga sakamakon shiga halin kunci da taskun rayuwa sakamakon takunkumin da Amurkan ta kakabawa Iran.

Yayin da annobar korona ta janyowa kasashen gagarumar matsala, duk da haka babu wata kofa ta samun sulhu tsakaninsu.