Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Guinea: Alpha Condé mai shekara 82 yana neman ƙarin shekaru shida
- Marubuci, Daga Paul Melly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai sharhi kan Afrika Ta Yamma
A ranar Lahadi mai zuwa ne Alpha Condé, shugaban ƙasar Guinea mai shekara 82, zai nemi ƴan ƙasar masu zaɓe miliyan 5.4 su kaɗa masa ƙuri'unsu a karo na uku, a wani lamari mai cike da ɗarɗarɗar na yanayin siyasa a Afrika Ta yamma, inda baya ga ƙasar za a kuma yi zaɓuka a Ivory Coast da Ghana da Nijar.
Idan ya gaza samun nasarar da fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un, to akwai yiwuwar shugaban ƙasar zai fafata da abokin hamayyarsa Cellou Dalein Diallo, a zagaye na biyu na zaɓen, wanda ake hasashen yiwuwar ɓarkewar rikici a kan titunan birnin Conakry, babban birnin ƙasar mai yawan al'umma.
Hawan Mr Condé kan mulki a watan Disamban 2010 shi ne karo na farko da aka miƙa mulki na gaskiya ga dimokraɗiyya tun bayan shekara 52 da samun ƴancin kan ƙasar - an yi ta samun rikita-rikita na mulkin kama karya da mulkin soji da suka haɗa da damuwa da musgunawa, na bayan-bayan nan shi ne kisan kiyashin da ya faru a ranar 28 ga watan Satumba, inda dakaru suka kashe a ƙalla magoya bayan ƴan hamayya 160, da yi wa mata 11 fyaɗe, waɗanda suka haraci wani gagarumin taro a filin wasa.
An sha kulle shi a gidan yari kan ƙalubalantar Janar Lansana Conté, wanda ya yi mulki daga shekarar 1984 har lokacin mutuwarsa a 2008, ya kuma durfafi yin wani babban aiki na yi wa dakarun tsaro garambawul tare da gina dimokraɗiyya a ƙasar da girmama hakkin ɗan adam da kuma yin ƙe-ƙe da ƙe-ƙe wajen kashe kuɗaɗen ƙasa.
Nasarori
An samu ci gaba sosi a shekaru 10 da suka gabata.
Fargabar yin juyin mulkin soji ta kau a hankali, sannan a ƙalla an samu sauyi a ɓangaren soji, inda aka yi wa jami'ai da dama ritaya.
Tawagar wasu ƙwararrun ministoci sun farfaɗo da tattalin arziki, tare da sake farfaɗo da alaƙar ƙasar IMF, da kuma ƙungiyoyin bayar da tallafi.
Guinea tana da ɗumbin arzikin albarkatun ƙasa da kuma sa ido tare da yin garambawul kan ɓangaren da ke kula da su.
Masu zuba jari sun samu ƙarfin gwiwa, inda aka sa ran za a ci gajiyar albarkatun ƙasar da ke yankin Simandou - tare da samar da dubban ayyuka ga mutane da dama.
Kana ƙasar ta samu shawo kan annobar cutar korona da kuma annobar cutar Ebola da ta ɓarke a can kamar yadda ta barke a maƙwabtanta Saliyo da Laberiya.
Rashin nasara
Amma an samu wasu manyan matsaloli da suka haɗa da cin zarafin ɗan adam.
Ƴan hamayya kamar irin su Mr Diallo sun sha fuskantar cin zarafi, yayin da ake yawan samun ɓarkewar rikici a kan tituna, na faɗa tsakanin matasa masu zanga-zanga da jami'an tsaro.
Haka kuma, har yanzu ba a yi shari'ar manyan hafsoshin soja ba da ake zargi da kisan kiyashin 28 ga Satumba, duk da gwagwarmayar da ƴan uwan waɗanda aka kashe suka daɗe suna yi, da matsin lambar ƙasashen waje da kuma alamun cewa kotun hukunta manyan laifuka za ta shigo ciki idan har mahukuntan Guinea suka kasa ɗaukar mataki.
Aƙalla ɗaya daga cikin sojojin da ake tuhuma ya riƙe muƙamin gwamnati ƙarƙashin Mista Conde, yayin da Moussa Dadis Camara - shugaban soja da dakarunsa suka yi kisan kiyashin aka binciken sa amma kuma ya samu hanyar barin ƙasar ya samu makafa a Burkina Faso.
Kaftin Camara sananne ne a yankinsa, Guinée Forestière, kuma manyan ƴan siyasa ba su son ɗaukar matakin da zai zama barazana.
A zaɓen 2015, Mista Diallo ya ƙulla wani ƙawance da ɓangarensa, yayin da babban amininsa Kaftin Camara babban minista ne a gwamnatin Mista Conde.
Sabon kundin tsarin mulki bai yi warsi da wa'adin shugabanci biyu ba, amma ya sake tsara matakin, don haka yawan wa'adin da aka yi a baya ba su cikin lissafi.
A farkon shekarar nan, Ƙungiyar Ecowas ta gano sunayen masu ƙada kuri'a da ta yi zargin na bugi ne kusan miliyan 2.5.
Ƴan adawa sun ƙauracewa ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a, wadda ta ba Mista Conde nasara cikin sauƙi.
Amma an matsa masa kan ko yana da burin zama shugaban ƙasa har abada.
Ko da yake Mista Condé bai fito ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takara a hukumance ba, ko a farkon shekarar da ta gabata burinsa na yin hakan ya riga ya zama abin ce-ce-ku-ce a Conakry - wani abu da ke haifar da damuwa tsakanin sauran shugabannin Afirka Ta Yamma, da jami'an diflomasiyyar Turai, saboda fargabar sake ɓarkewar rikici.
A cikin ƙasar da ta ke da irin wannan dogon tarihin rikice-rikicen siyasa.
Akwai fatan cewa za a iya shawo kan shugaban ya hakura ya ɗora wani ma'aikacin gwamnati. Amma kuma burinsa a bayyane yake tsawon watanni.
Ƙabilanci
Wannan wani babban ƙalubale ne ga abokan hamayya, musamman ƙarfin gwamnati wajen kashe kuɗi ƙarfin Mista Condé a hamayyar shugabancin.
Abu biyar game da Guinea:
- Shugaban da ya jagoranci ƴancin kai Sekou Touré ya faɗawa Faransa a 1958 cewar: "Guinea ta fi son talauci cikin' yanci fiye da bautar bayi"
- Jagoran gwagwarmayar "Black power"Stokely Carmichael ya dawo daga Amurka zuwa 1968, tare da matarsa Miriam Makeba, wanda ya zama babban ɗan gwagwarmaya a Afirka
- Ita ce babbar mai arzikin dutsen bauxite - da ake samar da ƙarfen gorar ruwa
- Gandun dajin Nimba, manyan gandun daji na hukumar Unesco da ke kan iyaka da Ivory Coast da Liberia, yana cikin manya a duniya
- MawakiMory Kanté, sananne a wajajen 1980 musamman Yéké Yéké, ɗan asalin Guinea ne.
A zaɓukan da suka gabata, wasu daga ɓangarensa sun yi amfani da ƙabilanci inda suke razana masu kaɗa ƙuri'a ƴan ƙabilar Malinke da Soussou domin adawa da Mista Diallo, ɗan ƙavilar Peul ko Fulani, ƙabilu mafi yawa a Guinea.
A cikin irin wannan yanayi, a watanni da dama kamar ƴan adawa galibi sun haɗu ƙarƙashin inuwar gamayyar FNDC, suka ƙauracewa hamayyar da suke tunanin ba za a shuka adalci ba duk da ƙoƙarin gyara rijistar zaɓe da Ecowas ta amince.
Amma a farkon Satumba, Mista Diallo ya ɓalle daga gamayyar FNDC, inda ya bayyana cewa zai tsaya takara wanda ke nufin zai fafata da Mista Conde karo na uku a jere.
Rabuwar kan ƴan adawa
Ba shi kaɗai ba ne mai hamayya amma shi ne babban mai hamayya.
Ya nace cewa yana da damar lashe zaɓen amma yana fuskantar ƙalubale.
Farin jinin tsarinsa na farfaɗo da tattalin arziki a matsayin Firaminista a tsakanin 2004 zuwa 2006 ya ragu.
Kuma yadda ƴan adawa suka rabu kan tunanin ƙauracewa zaben, ba ya da tabbaci kan samun goyon baya.
Yakin neman zaɓensa ya gamu da cikas da kuma musgunawa a cikin gida, musamman ma yankin Kankan arewa maso gabashi da Mr Condé ke da dimbin magoya baya.
Amma ga alama ya san me ya taka, watakila yana tunanin samun goyon bayan matasa a birane, musamman idan kundin rijistar da aka tsabtace da kuma masu sa ido da suka takaita yiyuwar yin magudi.
Amma duk da haka, ƙarfin ikon shugaban kasa, kamar Mista Mr Condé yana da kwarin gwiwar nasara a zaɓen