Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Youth Democratic Party: Zanga-zangar SARS ta yi wa matasan Najeriya ƙaimi na son kafa sabuwar jam'iyya
Yayin da ake ci gaba da zanga-zangar EndSars a Najeriya, wasu matasan ƙasar sun bijiro da wata jam'iyya da suke yaɗawa a shafin Twitter da sunan sabuwar jam'iyyar matasa ta ƙasar.
Tun wayewar garin Laraba, tambarin jam'iyyar ke yawo a shafin Twitter kuma matasa ke neman goyon bayan juna wajen kafuwarta.
Sunan jam'iyyar dai Youth Democratic Party wato YDP, kamar yadda matasan ke yaɗa ta a shafin Twitter duk da cewa akwai wata jam'iyyar mai rajista da ake kira Young Democratic Party.
Tun bayan da matasan suka ga sun yi nasara wurin neman gwamnatin ƙasar ta rushe rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta ƙasar wato SARS, sai su ka ga cewa lallai muryarsu tana da matuƙar tasiri.
Wannan ne ya sa matasan da dama suka fara ba juna shawarwari kan cewa su fito da jam'iyya da za su tsayar da matasa 'yan uwansu domin su yi takarar shugabancin ƙasa a 2023.
Da alama wannan yunƙuri nasu ya fara karɓuwa ganin yadda matasa da dama suka yi na'am da wannan jam'iyya kuma suke ta yaɗa tambarinta a shafin na Twitter.
Shafin Twitter dai ya kasance tamkar wani dandali inda masu zangar ke haɗuwa domin gudanar da shawarwari da kuma taimakon junansu da yaɗa farfagandar su.
Me matasan ke cewa?
Wannan wan shafi ne da ke iƙirarin shafin jam'iyyar inda yake cewa matasan Najeriya a shirye suke domin su sake ɗaga tutarsu sama. Sun yi kira ga cewa a tanaji katin zaɓe a shekarar 2023.
Wannan kuma rantsuwa ya yi da Allah inda ya ce idan yadda mutane suka fito a lokacin wannan zanga-zangar suka fito domin goyon bayan matasan da jam'iyyar YDP za ta tsayar takara a 2023, sai sun lashe zaɓe ko da an yi maguɗi.
Wannan kuma na daga cikin masu fafutikar ganin cewa an kawo ƙarshen SARS a Najeriya inda yake cewa wani juyin juya halin na kan hanya.
Ya ce babu wani muƙami da za a ba tsofaffin mutane a 2023.
Me ya jawo matasan neman ƙirƙirar sabuwar jam'iyya?
Zanga-zanga a Najeriya ba ta cika tasiri ba, inda a kullum idan aka dage da zanga-zangar, gwamnati kan yi amfani da jami'an tsaro wurin tarwatsa masu zanga-zangar.
An ga yadda aka ƙare tsakanin gwamnatin ƙasar da masu bin aƙidar Shi'a da kuma masu fafutikar kafa ƙasar Biafra da dai sauran zanga-zanga da aka yi a baya-bayan nan.
Sai dai a wannan karon, zanga-zangar da matsan suka yi ta yi tasiri inda suke ganin cewa ƙarfinsu da suka yi amfani wurin wannan zanga-zangar, zai iya yin amfani a nan gaba musamman lokacin zaɓen 2023.
Matasan suna ganin cewa a tsakaninsu idan suka yi karo-karo suka haɗa kudi za su iya yin kamfe kuma su tsayar da ɗan takararsu domin cin zaɓe.
Shin wannan jam'iyyar da ake neman kafawa za ta yi tasiri? shin haƙar su za ta cimma ruwa? lokaci ne kaɗai zai iya tabbatar da hakan.