Muhammadu Buhari: Abin da ya kamata ku sani kan sabon tsarin shugaban Najeriya na inganta rayuwar malamai

Asalin hoton, Buhari Sallau
Malamai a Najeriya sun ci ribar bikin ranar malamai ta duniya, inda shugaban ƙasar ya sanar da sabbin matakai na inganta rayuwarsu.
A ranar Litinin 5 ga watan Oktoba da ake gudanar da bikin ranar Malamai ta duniya shugaba Muammadu Buhari na Najeriya ya sanar da sabbin tsare-tsare ga malamai da suka ƙunshi har da ƙarin albashi da ƙarin shekarun ritaya da kuma gina wa ga malaman makaranta gidaje a faɗin ƙasar.
Shugaban ya ce malamai sun kasance tubali na ci gaban ko wace ƙasa da ta inganta tsarin iliminta, domin a cewarsa malamai ne ke gina yara da rayuwarsu da za ta kasance mai kyau gare su da kuma ƙasarsu.
Buhari ya ce yana sane da halin da malamai suke ciki da kuma ƙalubalen da suke fuskanta.
Don haka shugaban ya ce gwamnatinsa ta ɓullo da sabon tsari da kuma sabbin sauye-sauyen inganta aikin koyarwa a Najeriya, kuma wannan domin ƙarfafa gwiwar malaman don ƙara zage damtse a aikinsu.
Buhari ya amince da sabbin tsare-tsaren magance matsalolin malamai kamar haka:
- Za a ƙarfafa gwiwa da janyo hankalin masu digiri don su rungumi aikin malanta
- Ƙirƙiro da sabon tsarin gwamnati na bayar da wani ihsani ga ɗaliban da ke karatun koyarwa a Jami'o'i
- Tabbacin samun aiki kai-tsaye da zarar sun kammala karatu
- Asusun kula da karatun gaba da sakandare da bayar da tallafin karo karatu da ake kira TEFUND zai ɗauki nauyin koyon karantarwa
- Za fi ba waɗanda suka fi ƙoƙari muhimmanci a aikin koyarwa
- Sabon tsarin albashi na musamman ga makarantun firamare da sakandare
- Za a dinga ba malaman da aka tura karkara da malaman da ke koyar da kimiya kuɗaɗen alawus
- Samar da sabon tsarin fansho na musamman ga malamai
- Ƙarin yawan shekarun ritaya zuwa 65 da kuma shekarun aikin koyarwa ga malamai daga 35 zuwa 40
- Samar da tsari na musamman ga aikin koyarwa da kuma ba malamai horo
Baya ga waɗannan sabbin tsare-tsaren, shugaban na Najeriya ya kuma amince da wani tsarin ƙarin ihisanin na inganta rayuwar malamai domin ƙarfafa masu gwiwa, kamar haka:
- Za a gina wa malaman makaranta gidaje a birane
- Duk shekara za a dinga ba malaman horo
- Za a faɗaɗa lambar yabo ta shugaban ƙasa ga makarantu da malamai ga fannoni da dama
A Najeriya matsalar ilimi sai ƙara taɓarɓarewa ta ke, inda kusan duk shekara sai wani ɓangare na malaman ya tafi yajin aiki.
Saɓanin yadda a wasu kasashe da dama a duniya ake fifita malaman makaranta, kasancewarsu ginshiki ga ci gaban al`umma, amma malaman makaranta, musamma ƙananan makarantu sun daɗe suna kukan cewa ana mai da su ƴaƴan bora.

Asalin hoton, Getty Images
Rashin tsari mai kyau ga malamai ya sa ƴan ƙasar ke gudun aikin koyarwa a Najeriya. Waɗanda ya kamata su koyar, ba su ba ne ke koyarwa a Najeriya.
Yawanci masu ruwa da tsaki da kula da harakar ilimi a Najeriya ba su kai ƴaƴansu makarantun gwamnati sai na kuɗi masu zaman kansu, saboda lalacewar ilimin a ƙasar.
Tabbas idan har gwamnati ta cika waɗannan alkawullan da ta ɗauka na inganta rayuwar malaman makaranta, wasu na ganin za a samu sauyi.
Amma ko wannan zai shafi malaman makarantun da ke jihohin Najeriya da matsalar taɓarɓarewar ilimin ta fi ƙamari?











