Jane Goodall: Yadda Birrai ke gaisuwa ta hanyar sumbata tamkar mutane

''Suna gaisuwa da sumbata da runguma, sannan suna lalashin juna domin ƙarfafa gwiwa. Suna riƙe hannu. Suna buƙatar kulawar ƙwararru idan suka shiga damuwa ko fargaba. Komai dai kamar yadda muke.''

Haka Jane Goodall, daya daga cikin ƙwararru kan birrai, ta bayyana kamanceceniyar mutum da dabbar da muka zo kusan ɗaya a duniya. Sai dai ba a nan kawai aka tsaya ba.

''Abin mamaki ne sanin cewa suna iya zama marasa imani da ƙaddamar da yaki. Wani lokaci suna zama masu jin-ƙai. Yanayinsu na sauyawa kamar na mutum,'' a cewarta.

Kashi 98.6 cikin 100 na ƙwayoyin halittar birrai guda suke da na mutane, amma har yanzu akwai ƙarancin fahimta ko abu da aka sani a kan su ƙalilan ne kafin zuwan masana kimiyyar Burtaniya, Gombe da ke yammacin Tanzania a 1960.

Goodall ta tattauna da BBC kan shekaru 60 da ta kwashe na sadaukarwa wanda ta ce ya taimaka mata wajen fahimtar da duniya kan wannan dabba, da yadda za su taimaka mana wajen sake fahimtar da mu su waye ɗan adam.

Martabar Jarida

Goodall ta ɗauki wani hoton neman suna a 1965 wanda ya fito a matsayin bangon Mujallar National Geographic.

Aikinta shi ne mayar da hankali kan shirinta na musamma 'Miss Godall and the Wild Chimpanzees' - wannan da sauran fina-finai, labarai da makalolin da ake wallafawa a mujalla da litattafai sun sha bayyana miliyoyin batutuwa a duniya kan rayuwar birrai.

Shirin nata na nuna yadda Goodfall ke tafiya a ƙasa, babu takalmi a kasurgumin daji, tana wasa da kokuwa da jariran birrai. Wannan ya nuna cewa akwai soyayya sosai tattare da aikin nata.

A lokacin da take bai wa danginta labarin waɗannan lokuta a gidanta da ke Bournemouth a kudancin Ingila, ta ce ta yi wannan gwagwarmaya ce domin gina gaskiya.

'Ɗan Biri mai abin mamaki'

''Akwai tsoratarwa.'' Ta san cewa birrai sun fi ta karfi sosai, amma duk da haka ta danne fargabarta.

''Sai da nayi kusan wata hudu kafin na je kusa da guda sannan.... na yi shekara guda kafin na koyi zama da su. Ba su taba ganin wani abu kamar farin ɗan biri ba.''

Ta ba su sunaye na musamman bayan kasafta su rukuni-rukuni.

Bambanci

Masana kimiyya a Burtaniya na taka tsan-tsan da dabarunta da bincikenta lokacin da ta dawo domin ci gaba da karatun PhD a Jami'ar Cambridge.

''Ba zan iya cewa ga abubuwa da suke da shi ba, zuciya ba za ta iya kawo maslaha da tausayi ba,'' a cewarta, yayin da take kwatanta alaka masu karfi tsakaninsu da mutane.

''Birrai na bukatar lambobi ba wai suna ba, a cewarta.

''Don haka galibin waɗannan farfesa na cewa ban yi wani laifi ba.''

Yaƙin basasa

Nasarar Goodall ta ilimantar da duniya a kan Birrai abin yabawa ne.

Ga waɗanda ba su taba ganin biri ba a zahiri tunaninsu ya sauya a kan halittar.

Lokacin da Birin da take nazari a kansa ya mutu a 1972 a Tanzania, Jaridar Times ta wallafa labarin.

Shekaru bayan wannan lokacin an sake samun wasu mace-mace.

Birrai na da wani yanayi na mutunta juna bisa girma.

Alaka tsakanin bangarorin biyu na kasancewa mai tsauri, sannan mazan daga rukunin da suka fi girma ko karfi na kai hari kan maza da ke rukunin marasa yawa daya bayan daya, inda suke mutuwa saboda tsananin rauni.

Fafutika

Shekara 10 bayan nan a 1986, ta ziyarci wajen wani taro kuma yanayin da Birrai ke ciki su ne abubuwa da ta dawo da su gida a matsayin tsaraba.

''Na je taron masana kimiyya kuma na baro a matsayin mai fafutika,'' a cewarta.

Sauyin ya kaita Amurka inda ta gana da masu gwaji a kokarin fadar da su cewa su daina amfani da su a matsayin gwaji, kuma ta yi nasara.

''A Amurka kusan birrai 400 da aka yi amfani da su a cibiyar lafiya don gwaji na killace''

A Afirka, gidajensu na tsukewa, sannan farautarsu na ci gaba da zama matsala.

Ta hango zuwan haka tun a 1991 lokacin da aka rage girma tsibirin Gombe mai tsauninka ya tsuke.