Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda kakana ɗan Najeriya ya yi cinikayyar bayi'
Yayin da duniya ta shiga cikin yanayin muhawara kan alakar jinsi, mulkar bakar-fata da bautarwa, ana waiwaye kan rayuwar wasu daga cikin Turawa da Amurkawan da suka yi arziki ta hanyar cinikin bayi.
Wasu an tumbuke mutum-mutuminsu sannan an cire sunayensu daga gine-ginen gwamnati.
Wata 'yar Najeriya da ke aikin jarida da rubutun litattafai, Adaobi Tricia Nwaubani ta rubuta cewa daga cikin kakanninta akwai wanda ya sayar da bayi,
Sai dai ta ce ba daidai ba ne a fassara shi da sauyin da duniya ta zo da shi a yanzu.
Ta bayyana kakan-kakanta, Nwaubani Ogogo Oriaku, a matsayin dan kasuwa, daga kabilar Igbo a kudu maso gabashin Najeriya.
Abubuwan da ya yi kasuwancinsu a wancan lokaci sun hada da ganyen taba sigari da kwakwar manja. Yana kuma sayar da mutane.
''Yana da mutane da ke kamo masa bayi daga yankuna daban-daban,'' kamar yadda mahaifina ya shaida min.
Nwaubani Ogogo na cinikin bayinsa ne a gabar tekun Calabar da Bonny da ke kudu wanda a yau ake kira Najeriya.
Mutanen da suka fito daga kabilun da ke rayuwa a wannan yankin, kamar Efik da Ijaw ke taimaka wa Turawa a cinikin, su kan karbo bayin daga kabilun Igbo 'yan kasuwa kamar dai yadda kakan-kakana ke yi.
Bayi kusan miliyan 1.5 daga kabilar Igbo aka yi cinikinsu a yankunan Tekun Atlantic daga karni na 15 zuwa 19.
Sama da 'yan Afrika miliyan 1.5 aka yi safara, zuwa inda ake kira sabuwar duniya - wato Amurka - ta gabar tekun Calabar, wannan ita ce babbar hanyar da ake cinikin bayi a wancan zamanin.
Rayuwa daya tilo da suka sani
Nwaubani Ogogo, ya yi rayuwa a zamanin da mai karfi kawai ke iya rayuwa, sannan mai wayo kadai ke samun galaba. Tunanin ''duk maza daya suke'' kalma ce da ba ta tasiri a al'adu ko dokokin al'umma a wannan lokacin.
Babu adalci a ce za a yanke hukunci kan rayuwar mutumin da ya yi zamani a karni na 19 kan tsari ko dokokin karni na 21.
Kabilar Igbo da ke harkar sayar da bayi kamar kakan-kakana bai taba fuskantar matsalar kyama ko kiyayya daga al'umma ba. Ba sa bukatar wasu bayanai na addini ko kimiyya wajen kare kansu ko laifukansu.
Rayuwar kawai suke kamar yadda suka taso suka iske ana yin ta.
Binne bayi da rai
Wani labari wanda ba boyayye ba ne da na ji a kan kakan-kakana shi ne yadda ya tunkari jami'an gwamnatin Turawan Burtaniya bayan sun kwace wasu daga cikin bayinsa.
Ana safarar bayi hade da tabar tobbaco da man-ja, daga garinsu Nwaubani Ogogo da ke Umuahia zuwa kan tekun.
Kakan-kakana yana ganin ba a yi masa adalci ba, bayan kwace bayinsa.
Cinikin mutane tsakanin kabilar Igbo daddadiyar sana'a ce tun kafin zuwan Turawa. Ana mayar da mutane bayi a matsayin hukuncin wani laifi da suka aikata, ko kasa biyan bashi ko fursunonin yaki.
Harkar bayi ta yi fice sosai a tsakanin kabilar Igbo kuma wannan dalili ne yasa take amfani da kalmar ''bawa'' a karin magana da dama.
Zuwan Turawa da bijiro da tsarin tayin ba da bindigu da madubi da giya da kayan maye a matsayin musaya da mutane ya sake habbaka harkar bayi, mutane sun yi ta sace mutane suna sayar da su a wannan lokacin.
Yadda ake cinikin bayi a Afirka
- Turawan da ke sayan bayi na jira a gabar teku
- Masu sayar da bayin 'yan Afirka na taho da bayin a kasa
- Suna tafiyar tsawon kilomita 485 (300 miles)
- Ana sanya musu kaca ko ankwa
- Wadanda Turawa suka cafke ana daure su da igiya ta wuya
- Kashi 10 zuwa 15 cikin 100 na bayin na mutuwa a hanya
Bayanai daga: Encyclopaedia Britannica
Yakin daina bautarwa
Har shekara ta 1888 ana cinikin bayi a Afirka, Brazil ce kasa ta karshe a yammacin duniya da ta dakile cinikin bayi.
Lokacin da Burtaniya ta tsawaita mulkinta a kudu maso gabashin Najeriya a karshen karni na 19 zuwa 20, ta soma hana cinikin baya ta amfani da karfin soja.
Amfani da karfi maimakon ganar da mutane da dama kamar kakan-kakana wanda ba shi da ilimin gane cewa ana kokarin hana harkar bayi ne saboda kare martabar dan adama ba wai sauyi ba ne da gangan da zummar nakasa tattalin arzikinsu.
A sanin kakan-kakana, yana da lasisi da kamfanin Royal Niger ta gwamnatin Burtaniya ta bashi domin gudanar da harkokinsa a karni na 19.
Don haka lokacin da aka kwace kayayyakinsa, Nwaubani Ogogo a fusace ya tunkari jami'an Turawa ya kuma nuna musu lasisinsa. Nan take suka sakar masa kayayyakinsa da bayi.
Cinikin bayi a karni na 20
Masanin tarihi Igbo, Adiele Afigbo ya bayyana cinikin bayi a kudu maso gabashin Najeriya har zuwa shekarun 1940 zuwa 1950 a matsayin sirri mafi girma karkashin mulkin turawar mulkin mallaka.
Yayin da aka kawo kashen wannan harkar tsakanin kasa da kasa, harkar bayi a cikin gida bai sauya ba.
''Gwamnati tana sane da cewa ana harkar bayi a sirrance tsakanin masu gadi a bakin teku,'' kamar yadda Afigbo ya wallafa a littafinsa - The Abolition of the Slave Trade in Southern Nigeria: 1885 to 1950.''
Suna bukatar masu harkar bayi a mulki, da kuma kokarin habbaka ci gaba da halastaccen kasuwanci.
A wasu lokutan, suna kau da kai maimakon aiwatar da abubuwan da suka fi muhimmanci, kamar abin da ya faru da Nwaubani Ogogo lokacin da suka mai do masa bayinsa.
Wannan kuma ya kasance jigo wajen kula alaka tsakanin turawa da kakan-kakana, Nwaubani Ogogo abin da ya kai ga an ba shi mukami a lokacin mulkin Turawan.
Ya kasance wakilin gwamnati ga mutanan yankinsa.
Wasu rahotannin da aka samu daga kundin adana bayanai na Burtaniya ya nuna yadda Turawa suka sha bakar-wuya wajen kawo karshen cinikin bayin cikin gida wasu sun shafe kusan duk shekarun da suke mulki wajen cimma hakan.
Sun kawo tsarin kasuwanci halastacce, musamman harkar samar da kwakwa. Sun bijiro da kudin kashewa maimakon amfani da wuri ko musaya. Sun kuma kawo tsarin aike mai laifi gidan yari.
Aiki da Turawan Burtaniya
A matsayinsa na shugaban al'umma, Nwaubani Ogogo na karbar haraji a wajen mutane a madadin Turawan sannan ya samu nasa kasafin.
Ya sha jagorantar shari'a a kotu. Ya dauki leburori da ke aikin gina layin-dogo. Ya kuma bai wa masu yada bishara filin gina coci da makarantu.
Gidan na da girma da kuma iyayena suka yi rayuwa, fili ne da ya mallaka shekaru sama da 100.
Yanki ne da Nwaubani Ogogo ke karbar baki, yana sauke jami'an Turawa. Suna aike masa sakonnin dauke da alamar da ke nuna cewa suna tafe nan kusa.
A cikin karni na 20 Nwaubani Ogogo ya mutu. Ya bar gomman mata da yara. Babu hotonsa amma bayanai sun nuna cewa yana da hasken fata.
Kakan-kakana ya yi suna sosai saboda karfin kasuwancinsa, ba ya ga batun rashin jin tsoro da iya shugabanci, ya na da tasiri sosai ya kuma bada gudunmawa sosai ga al'umma da kuma addinin kirista.
'Yan Igbo ba su da al'adar adana kayayyakin tarihin mutanen da suka yi shahara - da an samu ko guda a rumbin tarihi yankin Umuahia.
''Yana da daraja a idon mutane,''a cewar mahaifina. ''Turawa na daraja shi sosai.''