Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Illar Coronavirus: Yadda cutar take lalata ƙwaƙwalwa
- Marubuci, Daga Zoe Cormier
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
Wasu masana kimiyya sun ce cutar korona mai haifar da sarkewar numfashi ba ta huhu kawai take ƙisa ba, takan lalata ƙwaƙwalwa, kuma alamominta sun hada da ciwon kai da shanyewar barin jiki.
Wata kwararriyar likita da ta yi nazari kan batun, Julie Helms, ta ce bincikenta ya soma ne lokacin da aka kwantar da marasa lafiya a fannin bayar da kulawar gaggawa da ke asibitin Jami'ar Strasbourg na arewacin Faransa a farkon watan Maris din 2020.
A cikin 'yan kwanaki, duk wani mara lafiya da aka kwantar a wannan sashen na dauke da Covid-19 - kuma ba wai sarkewar numfashin da suke fama da ita ba ce ya ankarar da ita.
"Sun shiga mummunan yanayi, kuma da damansu na da matsalar ƙwaƙwalwa - mai rikitarwa da jefa damuwa,'' a cewarta.
"Hakan ba daidai ba ne. Akwai tsoratarwa, musamman ganin yadda akasarin mutanen da aka yi wa magani matasa ne -shekarunsu bai haura 30 zuwa 40 ba, har da 'yan 18."
Matsalar ƙwaƙwalwa
Helms da abokan aikinta sun wallafa wani dan binciken da suka yi a jaridar kiwon lafiya ta New England Journal of Medicine inda suka bayyana alamomin matsalar ƙwaƙwala ga marasa lafiya da ke dauke da Covid-19.
Duk alamomin da suka nuna sun yi daidai da na wadanda ƙwaƙwalwarsu ta lalace - wani abu da dama masu bincike a birnin Wuhan na China suka gano tun a watan Fabarairu.
Yanzu haka akwai bincike sama da 300 da aka aiwatar a sassan daban-daban na duniya, kuma sun gano cewa matsalar ƙwaƙwalwa na tattare da masu Covid-19, ciki akwai 'yan alamomi kamar na ciwon kai, rashin jin wari ko kanshi, wanda hakan kuma na kai wa ga shanyewar barin jiki ko daukewar numfashi.
Wannan wani kari ne kan bincike da aka yi kan cutar, wanda a baya ake ganin kawai ta matsalar numfashi ce, sannan an gano tana lalata ƙoda da hanci da zuciya da kuma kowanne sashe na jiki.
"Sai dai har yanzu ba mu sani ba ko cutar da ke shafar ƙwaƙwalwa takan yi tsanani idan mutum yana dauke da Covid-19 kan wasu cutuka, amma ina shaida muku mun ga yadda take illa a yanzu,'' a cewar Elissa Fory likitar ƙwaƙwalwa a gidauniyar Henry Ford da ke Detroit, a Michigan.
"Yayin da alkaluman masu dauke da wannan cuta ke ƙaruwa, za a rika ci gaba da ganin wasu sabbin alamomi wadannda a baya ba a taba tunaninsu ba - kuma duk muna ganinsu ne lokaci guda, wanda ba abu ne da wasu daga cikin mu suka taba gamuwa da shi a rayuwa ba."
Ƙiyasin dai ya bambanta, sai dai da alama kusan kashi 50 cikin 100 na mutanen da aka gano suna dauke da cutar korona sun fuskanci matsalolin da ke da alaka da ƙwaƙwalwa.
Girman matsalar da yawaitar ta abu ne da har yanzu akwai sauran bincike a kai.
Akasarin mutane, har da likitoci ba su fiye ganin matsalolin ƙwaƙwalwa da zarar sun bayyana ba -wasu mutane ba sa nuna alamomin kafin barin jikinsu ko numfashinsu ya dauke.
Rashin nuna wasu alamomin
Akwai wasu matsalolin da ake fuskanta, akasarin mutane da ke fama da Covid-19 gwaji bai cika nuna suna dauke da cutar ba, musamman idan ba su nuna alamomin tari ko zazzabi ba.
Hakan na nufin idan aka gano suna da alamomin matsalar ƙwaƙwala ba lallai a alaƙanta hakan da korona ba.
''A zahiri, akwai mutane da ke dauke da korona amma alamomin da suke nuna akawai shi na rikidewa,'' a cewar Robert Stevens ƙwarrare kan irin wadannan cutuka a Jami'ar Johns Hopkins.
"Muna fuskantar matsala a wani mataki na daban wanda ke da alaka da ƙwaƙwalwa."
Cuta na daban
Masu bincike da dama sun yarda cewa watakila matsalar ƙwaƙwalwar tana tasowa ne saboda ƙarancin iskar da ke taimaka wa numfashi zuwa ƙwaƙwalwa.
Sai dai Fory da Helms ba su gamsu da hakan ba.
Akwai kuma wadanda ba su yarda cewa cutar tana shiga ƙwaƙwalwa ba.
"Idan kun tambaye ni a watan da ya gabata cewa akwai alaka tsakanin korona da ƙwaƙwalwa da amsar da zan baku ita ce A'a - amma yanzu sai ga rahotannin da ke neman tabbatar da hakan," a cewar Stevens.
A Japan, masu bincike sun bayar da rahotan wani mutum mai shekara 24 da aka tsinta kwance cikin aman da ya kwarara.
Numfashinsa ya dauke lokacin da aka yi kokarin gaggawar kai shi asibiti.
Gwaje-gwajen da aka yi a ƙwaƙwalwarsa sun nuna alamomin sanƙarau mai tsanani wanda kuma aka alakanta da Covid-19.
Masu bincike na China sun gano irin wannan matsalar kan wani mutum mai shekara 56 da ya zo musu da korafi kan maƙoshinsa.
Kuma bincike da dama kan Covid-19 a Italiya ya gano marasa lafiya sun fuskanci matsalolin ƙwaƙwalwa.
Hasali ma, yanzu wasu masu bincike na zargin cutar korona da ke haddasa daukewar numfashi ba ta hanyar lalata huhu take kisa ba, takan lalata ƙwaƙwalwa ne, kuma alamominta sun hada da ciwon kai da shanyewar barin jiki.
Mamayar cutar
Akwai cutuka da tabonsu kan zauna tare da mutum har karshen rayuwa.
Kashi 30 cikin 100 na mutane da suka yi ƙyanda a lokacin yarantarsu suna iya zama da tabo har karshen rayuwarsu.
Wasu cutuka tasirinsu ko barnar suna har abada ne.
Daya daga cikin misalai na irin wadanan cutuka shi ne annobar Influenza ta shekarar 1918, ta yi wa mutane barnar da har abada a ƙwaƙwalwa da kuma jikinsu.
Mutum miliyan biyar a duniya aka ƙiyasta cewa suna dauke da wasu nau'ukan cutuka da ake alakantawa da rashin bacci.
Cikin wadanda suka rasu akwai kalilan da ake ganin har yanzu ba su dawo daidai ba.
David Nutt, wani farfesa lafiya ne a kwalajen Imperial na Landan, ya ce shi da kansa ya yi wa mutane da dama magani tsakanin 1970 zuwa 1980 bayan sun gamu da damuwa sakamokon wata annoba da ta taba barkewa a Burtaniya a shekara ta 1957.
"Damuwar da suke ciki ya wuce wanda a lokaci guda a shawo kanta," in ji shi.
Nutt ya gargadi cewa irin wannan yanayi na sake iya maimaita kansa, watakila ya haura abin da aka gani a baya.
"Mutanen da suka warke daga cutar korona akwai bukatar a sanya musu ido sosai na tsawon lokaci domin tabbatar da cewa ba su da matsala ko ba ta shafi lafiyar ƙwaƙwalwarsu ba.
"Abin damuwa shi ne kusan kowanne jami'in lafiya a Burtaniya kokarinsa bai wuce gano alamomin korona ba - babu wanda ke mayar da hankali kan lafiyar ƙwaƙwalwa."
Bincike mai zurfi
Nutt ya tsara aiwatar da gwaji ta hanyar samun mutane 20 da suka yi korona kuma ta haddasa musu damuwa ko wata matsala da ta shafi lafiyar ƙwakwalwarsu.
A Baltimore, Steven, na son ya gwada irin wannan bincike kan marasa lafiya da suka yi fama da korona kuma ba a jima da sallamarsu daga sashen samun kulawar gaggawa ba.
A Pittsburgh, Shery Chou wanda shi ma ƙwararren likita ne ya gayyato ƙwararru daga kasashe 17 domin yin irin wannan nazari tare da gwaje-gwaje ƙwaƙwalwa.