Mace-macen Kano: Shin Gwamna Ganduje ya gaza ne?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da kakaba dokar kulle tsawon mako biyu a jihar Kano, wadda ke ci gaba da fuskantar mace-macen mutane da ba a saba gani ba.
Al'amarin na faruwa ne daidai lokacin da ake fuskantar annobar korona, wadda zuwa yanzu hukumomi suka ce ta yi sanadin mutuwar mutum arba'in a Najeriya, kuma cibiyar gwaji daya da ake da ita a Kano ta rufe tsawon kwanaki.
Wannan dai na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya fito ya yi bayani, inda ya zayyana irin girman matsalar da jihar tasa ke ciki.
A wata hira da BBC, Gwamna Ganduje ya dora kusan laifin abin da ke faruwa a kan gwamnatin tarayyar kasar.


Laifin Gwamnatin jiha ko Tarayya?

Asalin hoton, KNSG
Masana a ciki da wajen jihar Kano na alakanta mace-macen da ake samu a birnin Kano da irin rashin shiri daga bangaren jihar.
Bashir Hayatu Gentile mai sharhi kuma mazaunin Kano, ya ce " kasancewar gwamnatin Kano karkashin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ita ce ke da iko da hakki na kare dukiyoyi da rayukan 'yan Kano, to dole ita ce mai laifi a matakin farko.
Da farko ma gwamnatin ta ki yarda da rahotannin da kafafen watsa labarai suke bayarwa game da mace-mace saboda haka da gwamnati ta yarda da an shawo kan matsalar tun kafin ta fi karfin jihar."
Dangane da zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na jan kafa wajen taimaka wa jihar Kano kan mace-macen, Bashir Gentile ya ce " tun lokacin da Gwamna Ganduje ya fadi adadin abin da yake son a ba shi alkadarinsa ya karye a wajen gwamnatin tarayyar saboda ita jihar Legas wadda aka bai wa tallafin kudi, ba nema ta yi ba."
Har wa yau, mai fashin bakin ya ce "gwamnatin jihar Kano ba ta zuba mutanen da ya dace a kwamiti na musamman don yaki da annobar korona a jihar ba. Kwararru irin su farfesa Abdussalam Nasidi da Dr Nasiru Sani Gwarzo wadanda dukkanninsu 'yan jihar Kano ne kuma sun yi fice a duniya."
Jihar Legas ta fi Kano shiryawa cutar korona

Asalin hoton, Getty Images
Duk da yake gwamnatin jihar Kano ta kafe cewa ta yi dukkan shiri da ya kamata don tunkarar annobar korona, masu nazari kan al'amura na ganin cewa ba ta yi abin da ya dace ba tun farko kamar yadda jihohin Legas da Kaduna suka yi.
Barrister Bulama Bukarti mai sharhi kuma mazaunin birnin London ya ce "sabanin irin matakin wayar da kan al'umma da gwamnatin jihar Legas ta dauka dangane da cutar korona, jihar Kano ta gaza ta wannan fanni.
Jihar Kano dai ta sha cewa a shirye take amma abin da yanzu ya fito fili shi ne ba ta shirya ba, kuma ba a yi shirin da ya dace ba."
Ya kara da cewa "tun lokacin da cutar nan ta bulla a jihar Legas da birnin Abuja ya kamata a yi hasashen shigarta jihohin arewa irinsu Kano. Sannan kuma ta ce ta tanadi wuraren killace masu cutar, idan ta barke. Har wa yau, gwamnatin ta ce ta rufe iyakokinta amma sai muka ga jama'a na shiga jihar su fito."
Jihar Legas ta yi tanadin wuraren killace jama'a sannan kuma ta sayi injinan feshin sinadari na tsaftace wurare tun ma kafin gwamnatin tarayya ta kai mata dauki."
Jihar Kano ba ta bi tsarin dokar kulle ba

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai gwamnatin jihar Kano ta sanar da tsawaita kwanakin dokar kulle a jihar, da manufar dakile yaduwar korona.
Hakan ya sa 'yan jihar da dama ke sukar tsarin da aka bi na kulle, al'amarin da suke cewa ya haddasa yunwa a tsakanin al'umma.
A karshen makon jiya ne dai wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu mutane suka rinka surar buhunna da katan-katan na abinci daga wata karamar mota kirar a-kori-kura ta a cikin birnin Kano.
Bashir Hayatu Gentile ya ce "An kulle jihar Kano ba tare da wani tsarin tallafi ba. Misali gwamnatin jihar Katsina da Kaduna sun sayi kayan abinci don raba wa jama'arsu a yayin kulle. Amma jihar Kano babu wannan".
"A kididdiga da muka yi idan gwamnatin jihar Kano za ta fitar da naira bilyan uku za a je kowacce daga cikin kananan hukumomin jihar 44, a dauki mutum 12,000 da za a bai wa karamin buhun shinkafa mai cin 25kg tare da garwar mai da katan din taliya sannan kuma a ba shi naira 10,000," in ji shi.
Ya ce kamata ya yi gwamnatin Kano ta tsayar da duk wasu abubuwa ko kuma ayyukan da ake gudanarwa kamar titi da gada domin karkatar da kudin ga tallafawa talakawa har zuwa lokacin da Allah zai yaye wannan annobar.
Girman matsalar mace-mace a Kano

Duk da yake, kawo yanzu babu tabbatattun alkaluman da ke nuna adadin mutanen da suka rasu a jihar cikin mako biyun nan, bayan bullar annobar korona a Kano ranar 11 ga watan Afrilu,
Kwamared Kabiru Dakata na cibiyar wayar da kan al'umma a kan tabbatar da adalci da shugabanci na gari, ya ce matsalar ta wuce duk yadda ake tunani.
Ya ce "al'amarin ya zama ruwan dare... don kuwa kusan babu wata unguwa a cikin birnin Kano da ba ta samu irin wadannan mace-mace ba.
Kullum alkaluman karuwa suke yi shi ya sa abu ne mai wuya mu iya fito da kididdiga saboda haka muna ta bibiyar makarbartun da ake binne mutane.
Alal hakika ko an ce daruruwan mutane (ne suka mutu) ba a yi karin gishiri ba. Ya kamata idan an ce ba korona ba ce to a duba a ga mene ne yake kashe jama'a ba a tsaya ana karyata alkaluman da kafafen watsa labarai ke fitarwa ba."
Shi ma Bashir Hayatu Gentile ya ce "girman (matsalar) ta wuce yadda mutum ke tunani. A unguwar Fagge kawai cikin kwana biyu fiye da mutum 40 sun mutu. Ni ma a unguwar da nake Giginyu mutum uku sun mutu daga ranar Lahadi zuwa Litinin."
A ranar Lahadi ne, ma'aikatan hukumar NCDC a Kano suka dauke gawar wani mutum da ta shafe fiye da sa'a 24 yashe a bakin titi. Jama'ar yankin dai sun ce ba su san dalilin mutuwar mutumin ba.
Yadda Kano ta zama abar gudu

Za a iya cewa jihar da take abar so ga kowa a arewacin Najeriya, yanzu haka ta zama abar tsoro da kyama, bayan da karuwar mace-macen da wasu ke dangantawa da annobar korona.
Kusan mutum 30 da aka gano sun kamu da cutar korona a jihar Gombe sun samo cutar ne a birnin Kano, al'amarin da ya sa gwamnatin jihar Gombe ta rufe iyakokinta.
Ko a ranar Litinin ma sai da gwamna El-rufa'i na jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa : Almajirai biyar daga cikin wadanda jihar Kano ta mayar wa jiharsa na dauke da cutar korona.
Har wa yau, a karshen makon nan ne aka samu wani bidiyo wadda gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ke yin gargadi ga 'yan jihar su guji zuwa Kano don gudun kamuwa da cutar korona.
Martanin Gwamnatin jihar Kano
Kwamishinan yada labarai na jihar ta Kano, Mallam Muhammad Garba ya ce "mutane da dama sun mayar da batun annobar korona siyasa inda suke fadin abubuwan da suke so ta fuskar siyasa."
Mallam Muhammad Garba ya kuma ce "gwamnatin jihar karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yi duk wani shiri da ya kamata a ce jiha ta yi dangane da wannan annoba, illa iyaka dai, idan Allah ya kawo al'amari babu makawa."
Dangane kuma da zargin kin amincewa da alkaluman mace-macen da jihar ke fama da su, kwamishinan ya ce " ba mu ce ba a mutuwa ba kamar yadda kowa yake gani amma ba zai yiwu wani mutum wanda ba jami'in lafiya ba ya ce yana da kididdigar mutanen da suka mutu.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci ma'aikatan lafiya na jihar da su tattaro alkaluma kuma yanzu a kan hakan ake."
Har wa yau, Mallam Muhammad Garba ya ce " game da batun cewa ba su sanya kwararrun likitoci a kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano ba, ina son ka fada min shin wadanda muke da su yanzu a kwamitin ba su cancanta ba ne?"

Masana dai na ganin takaddamar da gwamnatin jihar Kano ke yi da gwamnatin tarayya kan wanda ke da nauyin fitar da jihar daga bala'in da ta fada zai shafi yaki da annobar korona a ba kawai a Kano ba har ma a fadin kasar.
Kasancewar Kano zuciyar arewacin kasar, cutar na iya kara yaduwa zuwa ga jihohi masu makwabtaka.
Bisa alkaluman hukumomi dai har yanzu mutum 77 ne a jihar suka kamu da cutar korona, mutum 3 suka mutu sakamakon cutar.
Sai dai ana ganin rashin gwaji sakamakon dakatar da aiki na wasu 'yan kwanaki da da cibiyar gwajin cutar da ke asibitin Malam Aminu Kano ta yi ne ya yi tasiri wajen rashin samun karin alkaluma.










