Zan yi bincike kan wutar lantarki — Buhari

Asalin hoton, STATE HOUSE
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai binciki gwamnatocin da suka gabata kan yadda suka tafiyar da harkokin wutar lantarkin kasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da gidajen talajibin da rediyo a Katsina a karshen mako.
Shugaba Buhari ya ce Najeriya ba za ta ci gaba ba idan dai ba a samu tsayayyiyar wutar lantarki ba, yana mai cewa dole ya yi bincike kan makudan kudaden da gwamnatocin da suka gabace shi suka kashe a fannin domin yin gyara mai dorewa.
Ya ce, "Dole ne mu yi bincike kan makudan kudaden da aka kashe a harkar wutar lantarki, ganin cewa duk da kudin da aka kashe ba a samun isasshiyar wutar. Matsalar ma'aikatar samar da hasken lantarki kamar matsalar ma'aikatar man fetur ce. An kashe fiye da $16bn amma babu tsayayyiyar wuta."
A baya dai tsohon shugaban kasar marigayi Umaru Musa 'Yar Adua ya zargi tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo da kashe fiye da $16bn domin samar da wutar lantarkin amma maimakon hakan kasar ta ci gaba da fama da matsalar rashin wutar.







