An yi yunkurin hallaka Burutai — Sojoji

Buratai ya tsallake rijiya da baya.

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto, Buratai ya tsallake rijiya da baya.

Babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya tsallake rijiya da baya a Zariya, bayan da wasu mutane suka yi wa tawagarsa kwanton bauna.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanal Sani Usman Kuka-Sheka, ya shaidawa BBC faruwar lamarin, in da ya ce suna zargin mabiya kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Shi'a ne suka kai harin.

Al'amarin ya faru ne a lokacin da Laftanal Janar Buratai ke kan hanyarsa ta dawowa daga Dutse, inda zai tsaya a Zariya wajen wani bikin yaye dalibai.

Rundunar sojin ta tabbatar da cewa an jikkata wasu daga cikin sojojin tawagar, amma bata fadi adadinsu ba.

To sai dai wasu majiyoyi daga bangaren 'yan shi'a na cewa ba su ne su ka yi kokarin halaka babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya ba.

Majiyoyin sun ce sojojin ne ma suka afka wa wasu mabiya kungiyar ba hawa ballantan sauka a cibiyar al-Husainiyyah da ke Zaria