An daidaita tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango

Jaruman fina-finan Hausan da suka fi shahara, Ali Nuhu da Adam A. Zango, sun daidaita bayan da suka kwashe wata da watanni ba sa jituwa.
Rashin jituwar dai ya faru ne a kan daya daga cikin jarumai mata, Rahma Sadau, kuma lamarin ya raba kawunan masu sana'ar ta fina-finan na Hausa.
Ranar Jumma'a wani malamin addinin Musulunci, kuma shugaban kungiyar masu sana'ar fina-finan Hausa, MOPPAN, Malam Khalid Musa, ya shiga tsakanin jaruman, yana mai yi musu wa'azi a kan muhimmancin zaman lafiya da kaunar juna.
Jaruman da wadansu jiga-jigai a harkar sun je wurin malamin ne, bayan da ya gayyace su.
Sulhun dai zai rage tsamar da aka samu a tsakanin masu harkar fina-finan Hausa, kasancewa Ali Nuhu da Adam A. Zango su suka fi yawan fitowa a fina-finan, kuma su ne suka fi yawan magoya baya.
Fina-finan na Hausa dai suna matukar kayatar da masu kallonsu, sannan dubban mutane ne ke cin abinci ta hanyar su, koda yake harkar na fuskantar kalubale da dama.







