An rantsar da Buhari a matsayin shugaba

Asalin hoton, NTA
An rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban Nigeria a wani biki a Abuja.
Shugabannin kasashen duniya da dama ne suka halarci bikin wanda aka yi a dandalin Eagle Square.
Sannan an rantsar da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.
An kafa tarihi a karon farko a kasar inda dan adawa a dare kujerar mulki bayan da Mr Goodluck Jonathan ya amsa shan kaye a zaben da aka yi a watan Maris.
Wannan ne karo na biyu da Buhari zai karbi mulki, saboda a shekarar 1983 ya shugabanci kasar a gwamnatin mulkin soji.
Ya karbi mulki a lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro da na tattalin arziki.







