An kama 'yan Boko Haram a Kamaru

Asalin hoton, AFP
Wasu rahotanni daga Kamaru sun nuna cewa wasu mutane 30 da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun shiga hannun 'yan sanda a kudancin kasar bayan sun taso daga Ngaoundare.
Haka kuma jami'an tsaro a Kasar sun kai hari akan wani ayarin motocin 'yan kungiyar Boko Haram a garin Gamboru.
Jami'an tsaron sun biyo motocin ne a wani mataki na neman mayar da martani akan 'yan kungiyar da suka dasa nakiya hallaka wani soja daya.
Haka kuma nakiyar ta kuma jikkata wasu sojoji biyu a harin da suka kai a garin Achigachia.
Haka kuma rahotanni sun ce jami'an tsaron Kamarun sun kai hari kan ayarin wasu motoci kusan 100 na 'yan Boko Haram da suka fito daga Banki a Najeriya zuwa wani wuri da ba a tantance ba.







