Amurka ta ki sayar wa Nigeria makaman yaki

Asalin hoton, Reuters
Jakadan Nigeria a Amurka ya soki Amurkar saboda kin sayarwa da kasar muggan makamai domin yaki da Boko Haram.
Ambasada Ade Adefuye ya yi zargin cewar an ki sayarwa Nigeria makamanne saboda zargin cin zarafin bil adama da ake yi wa sojojin kasar.
Ya karyata zargin cewar dakarun Nigeria na cin zarafin jama'a, inda ya ce Nigeria ba ta zaci Amurka za ta yi mata haka ba.
A cewarsa kungiyar Boko Haram tamkar kungiyar IS ce a don haka ana bukatar manyan makamai domin yakarta.







