'Jami'an tsaro na azabtar da 'yan Nigeria'

An zargi 'yan sanda da karbar cin hanci a caji ofis

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, An zargi 'yan sanda da karbar cin hanci a caji ofis

Kungiyar Amnesty International ta zargi sojoji da 'yan sandan Nigeria da azabtar da mutane musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta ce jami'an tsaron na amfani da hanyoyi daban-daban wajen gallazawa mutane ta hanyar lakada masu duka, da cire hakora, da fyade da kuma wasu hanyoyin cin zarafin maza, da mata, da kananan yara.

A rahoton da ta fitar, kungiyar ta ce tun daga shekara ta 2009, jami'an tsaron Nigeria sun tsare mutane tsakanin 5,000 zuwa 10,000 a kurkuku ba tare da gurfanar da su gaban shari'a ba.

Rahoton ya ce 'yan sanda da dama na azabtar da mutane a caji ofis domin a ba su cin hanci.

Wata mata 'yar shekaru 24 ta shaidawa kungiyar ta Amnesty International cewar, an fesa mata barkonon tsohuwa a farjinta lokacin da aka kama ta bisa zargin yin sata kuma bayan watanni 10 har yanzu tana kurkuku ba a gabatar da ita gaban alkali ba.

Kawo yanzu gwamnatin Nigeria ba ta maida martani ba game da wadannan zarge-zargen.