Kamaru ta kai soji 3000 iyakarta da Nigeria

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun tura karin dakaru zuwa yankin arewa mai nisa, inda adadinsu a yansu ya kai 3000.
Sannan jami'an tsaro na bincike ababen hawa da tantance matafiya a cikin kasar da kuma yankin na arewa mai nisa.
A baya-bayan nan yankin arewacin ya fuskanci hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa.
Kasar Kamaru ta yi iyaka da jihohin Adamawa da kuma Borno tungar Boko Haram a Najeriya.







