Gwamnatin Somalia ta nisan kanta da shariar fyade

'Yan jaridar da suka bada labarin fyade a Somalia
Bayanan hoto, Abdulmalik Yusuf da Muhammad Bashir ne 'yan jaridar da suka bada labarin zargin fyaden da aka yi a Somalia.

Gwamnatin Somalia ta ce ba za ta iya shiga batun matashiyar nan da aka daure a kurkuku bayan da ta yi zargin an yi mata fyade ba, saboda a cewarta wannan batun da ya shafi bangaren shari'a ne.

Kakakin gwamnatin, Ridwaan Haji ya ce 'yan sanda da jami'an sharia sun gudanar da zuzzurfan bincike, wanda ya haifar da hukuncin dauri ga matashiyar 'yar shekaru 19 da kuma 'yan jaridu biyun da suka bada labarinta.

An yiwa matashiyar daurin talala na tsawon watanni shida, abinda ke nufin ba za ta fito daga gidanta tsawon wannan wa'adi.

Matashiyar dai ta yi zargin wadansu maza biyu sun yi mata fyade da bakin bindiga.