APC na zawarcin gwamnoni 7 na PDP

A Najeriya, wasu shugabannin jam'iyyar adawa ta APC reshen arewa-maso-gabashin Kasar, sun kaiwa Gwamnan jahar Adamawa Murtala Nyako, goron gayyatar shiga jam'iyyar.
Har ila yau sun bukaci gwamnan ya tuntubi sauran takwarorinsa da ake takun- saka da su a jamiyyar PDP mai mulki, game da bukatar tasu.
Sakataren yada labaran jahar Adamawa, Malam Ahmad Sajo ya tabbatar wa da BBC cewa, Gwamna Murtala Nyako ya karbi goran gayyatar, amma hakan ba yana nufin ya zama dan jamiyyar adawa ta APC ba ne.
A ranar Laraba ne dai 'yan jam'iyyar adawar ta APC suka ziyarci gwamna Nyako.







