
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Kungiyar dattawan Kiristocin arewacin Najeriya ta bayyana cewar ba za ta goyi bayan dukkan wani wanda zai tsaya shugabancin kasar a zaben shekara ta 2015 muddun dai ba Kirista ba ne.
A wani bayanin bayan taro da kungiyar ta rabawa manema labarai a Kaduna kungiyar ta magabatan Kiristocin arewacin Najeriya ta ce ba ta ga dalilin da zai sa Kirista ba zai tsaya shugabancin kasar a zaben 2015 ba.
Kungiyar ta ce daga cikin dukkan yan arewar da suka yi mulki baya a kasar, walau zababbu ko na Soji kwaya daya ne kacal Kirista a cikin su.
Ta ce idan aka yi la'akari da cewar yawan al'umar yankin arewar kankan yake tsakanin Musulmi da Kirista, wannan karon Kirista daga yankin za su saka gaba saboda kuwa suna da wadanda suka cancanci shugabantar kasar.
















