
Shugaba Goodluck Jonathan
Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta fitar da wata sanarwa dake cewa, babu wani wanda zai samu tsayawa takarar kowanne mukami a jam'iyyar ba tare da ya lashe zaben fidda gwani ba.
Jam'iyyar ta kuma ce, samun takara karkashin tutarta zai ta'allaka ne ga irin aikin da duk mai rike da mukami ya yiwa jama'arsa.
PDP ta kuma ce, babu kanshin gaskiya a jita-jitar da wasu ke yadawa cewa, jam'iyyar za ta dagawa wasu kafa domin sake tsayawa takarar zabe.
Sanarwar da babban jami'in hulda da jama'a na jamiyyar Chief Olisa Metuh,ya sanya wa hannu ta nuna cewa jamiyyar ba ta da aniyar yin irin wannan dauki dora, saboda kundin tsarin mulkin jamiyyar da aka yi wa gyara na shekarar 2012 bai tanadi haka ba.
PDP ta ce duk wani dan takara da ke neman jamiyyar ta tsayar da shi, to sai ya samu karbuwa daga alumma sannan ya bi tsarin jamiyyar na zaben fidda gwani kamar kowa, kafin ya samu tikitin takarar jamiyyar.
Dangane da rahotannin dake nuna cewa jamiyyar za ta yi gyaran fuska ga kundin tsarin mulkinta, wanda zai kwaikwayi irin yadda siyasar Amurka take gudana kuwa, sanarwar ta nuna cewa, babu wani gyara da za a yi wa kundin tsarin mulkin jama'iyar wanda zai dace da yanayin siyasar ko ma wacce ce a duniya.
















