'Yan bindiga sun kona mutum 13 'yan gida daya a Kaduna

Mutum 13 'yan gida sun kone kurmus bayan 'yan bindiga suka banka musu wuta a kauyen Bakali da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

'Yan bindigar sun kashe mutum 20 sakamakon harbi kan mai uwa da wabi da suka yi ta yi a kona gidaje a lokacin harin na ranar Litinin.

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Wani dan gidan da ya tsallake rijiya da baya ya ce 'yan bindigar sun kulle iyalan a cikin gidansu sannan suka banka wa gidan wuta.

Ya shaida wa BBC cewa mutanen da maharan suka kashe sun hada da limamai da mata da gawarwarwakin mutum uku da aka kona da ba a iya gane ko su wanene ba.

Wasu mazauna garin na ganin harin 'yan bindigar ramuwar gayya ce a kan harin farmakin hadin gwiwar da sojoji da 'yan sintiri suka kai wa 'yan bindigar a maboyarus da ke kusa da kauyen.

Hakan ya fusata 'yan bindigar suka kwararo cikin gari domin daukar fansa, yayin da wasu mazauna suka tsere domin ku

"Wato abin da ya faru sojojin da 'yan banga da suka zo, sai sojoji suka ce wa 'yan banga ku shiga daujin nan tunda ku kuka san inda barayin nan suke.

"Idan kuka je kuka taro su mu kuma za mu taro ta nan, sai mu hadu mu yake su.

"Yan banga su ne suka shiga dauji. Da suka shiga dauji kuma suka ritsa barayin nan. Barayin nan suka bude wa 'yan baga wuta suka fi karfinsu.

"To a nan wurin babu wani gari in ban da garin Bakali. Shi ne 'yan banga suka fado garin Bakali.

"Shi ne sanadiyyar barayin da suka biyo su suka karkashe mutanenmu ke nan."