Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Boko Haram suka kona mutane da ransu a Auno
Mazauna jihar Borno a arewacin Najeriya na cigaba da martani game da harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai garin Auno da ya janyo mutuwar fiye da mutum 30.
Wasu rahotannin Najeriya sun rawaito gwamnan jihar Babagana Umara Zulum na nuna bacin ransa game da tafiyar da harkokin tsaro a jihar tun bayan hawan sa karagar mulki.
Mayakan sun kai harin ne da tsakanin karfe 9 zuwa 10 na daren Lahadi yayin da matafiyan ke barci cikin motocinsu bayan jami'an tsaro sun hana su shiga birnin Maiduguri tun da misalin karfe biyar na yammaci.
Wani ganau kuma daya daga cikin matafiyan da ke wajen a lokacin da aka kai harin ya shaida wa BBC yadda lamarin faru, inda ya ce shi ya yi lodin fasinja ne a garin Potaskum da ke jihar Yobe.
Ya ce bayan sun isa mashigar Borno, sai aka ce musu lokacin daina shiga cikin Maiduguri ya yi domin a lokacin karfe biyar ne saura minti 24.
Ganau din ya ce, sun roki jami'an tsaron da ke wajen amma suka hana su shiga, sai suka koma wani gari Auno da ke da nisan kilomita 24 daga Maidiguri suka ajiye motocinsu suka samu waje suka zauna.
Ya ce can suna cikin hira da misalin karfe tara na daren ranar, sai suka ce bari su dan yi bacci.
Direban motar ya ce, wasu fasinjojin na tare da su suna hira, wasu kuma na cikin mota sun dan kwanta a ciki, sai kawai ba su yi aune ba sai suka fara jin harbin bindiga.
Ya ce, motoci ne da dama da suka hada da tankoki da manyan motoci da kuma kananan motoci sun fi 20 a wajen.
"Da muka fara jin harbin sai mutane wajen suka rude kowa ya fara ta kansa, anan ne 'yan bindigar suka rinka harbin fasinjoji da kuma direbobin da ke wajen." in ji direban motar.
Ya ci gaba da cewa "Da na ga abin ya munana sai na koma motata na fara gudu, ban aune ba sai na gansu a gabana a kan babura na yi ta maza na gudu amma hakan bai yi wu ba, na fita daga cikin motar na samu waje na buya".
"Haka 'yan bindigar suka rinka harbi, sannan kuma suka cinna wa wata tankar mai wuta, anan ne motocin da ke wajen suka kama da wuta," in ji shi.
Ganau din ya ce "A idona suka cinna wa wata mota da fasinjoji a ciki wuta".
Direban motar ya ce, haka 'yan bindigar suka kasance a garin Auno har bayan karfe 12 na daren ranar sannan suka tafi.
Ganau din ya ce: "Muna boye a inda muka buya wajen karfe biyu da rabi zuwa uku, sai muka ji sojoji sun zo wajen".
Direban motar ya ce, "Da gari waye muka fito na ga tashin hankali saboda motocin wajen duk sun kone, ga gawarwakin mutane baya ga wadanda aka kona a cikin mota".
Matashiya
Harin da aka kai Auno matashiya ce a kan cewa har yanzu akwai barazana a bangaren tsaron Najeriya bisa la'akari da yadda 'yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba su gani ba.
A lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama mulki a 2015, ya yi alkawarin kawo karshen masu tayar da kayar baya.
Ko da yake, dakarun kasar sun samu nasara wajen murkushe masu tayar da kayar bayan, to amma idan aka yi la'ari da harin da aka kai Auno a kwanan nan, za a fahimci cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Daya daga cikin 'yan Najeriya na kiran da a yi garanbawul a tsarin tsaron kasar tare da sauya manyan shugabannin dakarun tsaron kasar, saboda suna gani idan aka yi hakan za a kara samun sauyi da ci gaba a bangaren tsaron kasar.