Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/07/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 24 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Sai da safenku,

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Wata fashewa ta hallaka mutum shida a Siriya

    Jami'ai a Siriya sun ce aƙalla mutum shida sun rasa rayukansu yayin da ɗaruruwa suka jikkata a arewa maso yammacin lardin Idlib sakamkon wata fashewa.

    Ba a dai san abin da ya haifar da fashewar ba, wadda ta afku a cibiyar ajiyar makami da ke birnin Maarrat Misrin.

    An kai waɗanda suka samu raunuka asibitocin da ke kusa, an kuma umarci jama'a su ƙauracewa yankin da lamarin ya faru.

  3. Yin tattaki kafa 7,000 a kullum na rage haɗarin kamuwa da cututtuka - Bincike

    Motsa jiki

    Asalin hoton, Getty Images

    Yin tattaki kafa 7,000 a kullum shi kaɗai yana ƙara wa kwakwalwa lafiya da kuma taimakawa mutum daga kamuwa da cututtuka daban-daban, kamar yadda wani bincike ya gano.

    Abu ne mai kyau bayan da aka amince da tattakin kafa 10,000 a can baya, a matsayin iya adadin ya kamata mutum ya yi.

    Bincike wanda aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet, ya gano cewa yin tattaki kaɗan ma yana da alfanu wajen rage barazanar kamuwa da cutuka masu tsanani, ciki har da kansa da cutar mantuwa da kuma cutukan zuciya.

    Karanta cikakken labarin a nan...

  4. Shugabannin Najeriya da suka rasu

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
  5. An kashe mutum 16 a rikici tsakanin ƴantawayen M23 da dakarun gwamnati a Kongo

    Kongo

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    An samu rahotannin kashe aƙalla mutum 16 a rikici tsakanin ƴantawayen M23 da Rwanda ke goyon baya da dakaru a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo.

    Al'amarin na zuwa kwanaki biyar bayan gwamnatin Kinshasa da ƴantawayen M23 sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Qatar.

    Mazauna Masisi sun ce lamarin ya rutsa da fararen hula da dama.

    Kafofin yaɗa labarai a arewacin lardin Kivu sun zargi mayakan M23 da yunkutin ƙwace ƙauyuka da dama a wannan makon, abin da kakakin ƴan tawayen ya musanta.

  6. Sabon shugaban APC ya ce zai janyo ƙarin gwamnonin PDP zuwa cikin jam'iyyar

    Nentawe Yilwatda

    Asalin hoton, X/Nentawe Yilwatda

    Sabon shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya ɗau alwashin ɗaukar matakai don ganin ya ƙara janyo gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta PDP zuwa cikin jam'iyyar mai mulki.

    Yilwatda ya bayyana haka ne yayin tattaunawa a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, jim kaɗan bayan zama shugaban APC.

    Ya ce baya ga ƴan jam'iyyar PDP da zai janyo zuwa APC, har da wasu ƴaƴan jam'iyyun adawa.

    "Abun da na fi mayar da hankali a yanzu shi ne ganin haɗin kan jam'iyyar mu," in ji shi - inda ya ce zai tabbatar da cewa jam'iyyar ta yaɗa manufofinta yadda ya kamata.

    Sabon shugaban jam'iyyar ta APC ya ce duba da irin tarihi da yake da shi a fannoni daban-daban, yana da ƙwarewar da ta kamata wajen jagorantar jam'iyyar mai mulki.

  7. 'Za mu dawo da masu shiga tsakani da muka aika don tattauna yaƙin Gaza'

    Isra'ila ta ce za ta dawo da masu shiga tsakanin da ta aika zuwa wurin tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, sakamakon martanin da Hamas ta mayar wa masu shiga tsakanin.

    An kwashe sama da makonni biyu masu shiga tsakani na Qatar da Masar na neman yin sulhu ta bayan fage da fatan kulla yarjejeniyar da Amurka ke mara wa baya na dakatar da faɗa da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

    Wakilin Shugaba Trump a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff, ya je Italiya domin ganawa da manyan jami'an Isra'ila da kuma na Qatar.

  8. Gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin arewa - Kwankwaso

    Kwankwaso

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan abin da ya kira watsi da yankin arewacin Najeriya, inda ya ce shugaban ya fi mayar da hankali kan gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.

    Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen taron shawarwari na masu ruwa da tsaki a jihar Kano na 2025 - wanda aka gudanar yau Alhamis, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    "Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan," in ji Kwankwaso.

    Karanta cikakken labarin a nan

  9. 'Motocin agaji 6,000 ne ke jira don samun izinin shiga Gaza'

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Motocin agaji na hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Unrwa, kusan motocin agaji 6,000 ɗauke da abinci da magunguna ne ke jira don samun izinin shiga Gaza, a cewar shugaban hukumar.

    A ranar 20 ga watan Yuli, Falasɗinawan da ke zaman mafaka a wata makarantar ƴan mata da Unrwa ta tanada suka gudanar da zanga-zanga kan batun yunwa da suke ciki.

    Shugaban hukumar hukumar ya ce ɗaya cikin yara biyar a birnin Gaza na fama da rashin abinci mai gina jiki.

    A wani sako da ya wallafa a shafin X, Philippe Lazzarini ya ce "yawancin yaran da muka gani sun jigata sannan suna cikin fargabar iya mutuwa idan ba su samu kulawar da suke buƙata ba".

    "Iyaye na cikin yunwar da ba za su iya kula da ƴaƴansu ba", in ji shi, inda ya ƙara da cewa "wannan matsala da ake ciki tana shafar kowa".

    Jami'an lafiya na Unrwa na "rayuwa ne kan cin abinci sau ɗaya a rana," in ji shi, inda ya ce akwai wasu ma'aikatans da ke tsuma lokacin aiki.

  10. Kotu ta buƙaci a biya masu zanga-zangar EndSars diyyar miliyan 10

    ENDSars

    Asalin hoton, EPA

    Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bai wa Sufeto-Janar na ƴansandan Najeriya da kuma kwamishinan ƴansandan jihar da su biya masu zanga-zangar EndSars diyyar miliyan 10, saboda take ƴancinsu.

    Mai shari'a Musa Kakaki da yake yanke hukunci, ya ce an musgunawa masu zanga-zangar kuma an take musu ƴancin da kundin mulki ya ba su yayin da suke maci na tunawa da waɗanda aka kashe lokacin zanga-zangar ranar 20 ga Oktoban, 2024.

    "Duk da cewa jami'an tsaro na da ƴancin da kundin mulki ya ba su na tabbatar da doka da oda, amma bai kamata su yi amfani da ƙarfi fiye da ƙima ba wanda ya saɓa wa dimokraɗiyya da kuma doka," in ji mai shari'a Kakaki.

    Waɗanda suka shigar da ƙara a gaban kotun sun haɗa da Hassan Taiwo Soweto, Uadiale Kingsley, Ilesanmi Kehinde, Osopale Adeseye, Olamilekan Sanusi, da Miss Osugba Blessing da sauransu.

    Akwai wasu ƙungiyoyi kare hakkin ɗan'adam da dama da suka mara musu baya irinsu Education Rights Campaign, Take It Back Movement (TIBM), da kuma Campaign for the Defence of Human Rights.

  11. Rasha da Ukraine sun kai wa juna hari bayan tattaunawar tsagaita wuta

    ...

    Asalin hoton, DSNS Odesa

    Rasha da Ukraine sun kai wa juna hare-haren jirage marasa matuƙa inda aka kashe mutum biyu a Rasha da uku a Ukraine, bayan kammala zagaye na uku na tattaunawar tsagaita wuta da aka yi a Istanbul.

    A yankin Kharkiv da ke gabashin Ukraine, an samu gawarwaki uku daga ɓaraguzan wani gida da aka kai wa hari, yayin da wasu mutane da dama suka jikkata a biranen Cherkasy da Zaporizhzhia.

    Haka kuma, harin ya shafi wata kasuwa da ke Odesa, inda gobara ta tashi a sassa daban-daban na birnin.

    A nata ɓangaren, Rasha ta ce mutum biyu ne sun mutu a harin kuma 11 suka jikkata sakamakon a birnin Sochi da ke yankin Krasnodar.

    Wani sabon hari da Rasha ta kai Kharkiv da safe ya jikkata mutum 33.

    Wakilan ƙasashen biyu sun gana a Istanbul domin cimma tsagaita wuta amma ba a samu wani ci gaba ba amma dai sun amince da musayar fursunoni 1,200 da kuma miƙa gawarwakin sojojin Ukraine 3,000 da suka mutu.

    Kowane ɓangare ya zargi dayan da ƙin amincewa da shawarwarin da aka gabatar.

  12. An ceto mutum 12 a mahaƙar ma’adinai da ta rufta a DR Congo

    ...

    Asalin hoton, South Kivu Governor’s office

    Gwamnan Kivu ta Kudu, Patrick Busu bwa Ngwi Nshombo, ya bayyana cewa an ceto mutum 12 a wurin haƙar ma’adinai da ya rufta a Lomera da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo a ƙarshen mako.

    A cewarsa, har yanzu ana ci gaba da aikin ceto, amma ba a tantance yawan waɗanda suka mutu ko suka ɓace ba tukuna.

    “Muna ƙoƙarin gano yawan mutanen da har yanzu ba a gan su ba,” in ji gwamnan yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru a ranar Laraba.

    ...

    Asalin hoton, South Kivu Governor’s office

    Lamarin ya faru ne a wani wurin haƙar ma’adinai na zinare da hannu da ke Lomera, inda hukumomi ke ƙiyasta cewa aƙalla mutum 4,786 ne ke aiki a yanayi mai haɗari da tsanani.

    Tun daga lokacin da lamarin ya faru gwamnan ya ba da umarnin rufe dukkanin ramukan da abin ya shafa,

    ...

    Asalin hoton, South Kivu Governor’s office

  13. APC ta naɗa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugabanta

    ...

    Asalin hoton, X/Nentawe Yilwatda

    Kwamitin zartarwa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da nadin Farfesa Nentawe Yilwalda daga jihar Filato a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa.

    An cimma matsayar ne yayin taron kwamitin zartarwar na kasa da ya gudana a Abuja.

    Taron wanda ke gudana a fadar shugaban kasar, na samu halartar Shugaba Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam'iyyar.

  14. Mutum fiye da 1000 aka kashe wajen neman agaji - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla fiye Falasɗinawa 1,054 sojojin Isra'ila suka kashe a wajen neman abinci tun daga 27 ga watan Mayun 2025 lokacin da sabon shirin bayr da agaji da Amurka da Isra'ila ke gudanarwa ya fara aiki.

    Tsananin yunwa a Gaza na janyo mawuyacin hali a faɗin Gaza in ji MDD yayin da kuma Falasɗinawa ke shaida wa BBC cewa suna tsoron kada a harbe su idan sun je wajen karɓan kayan agaji.

    Ɗazu ne da ma'aikatar lafiyar Hamas ta faɗi addadin waɗanda suke mutu sakamakon yunwa a Gaza in da ta ce addadin yanzu ya haura zuwa 113.

  15. Ƴan jarida da ke aiki a Gaza na barazanar faɗawa cikin ƙangin yunwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafar yaɗa labarai ta BBC da wasu manyan kafafen yada labarai uku sun nuna damuwa kan ƴan jarida da ke aiki a Gaza, waɗanda suka ce na shan wahalar samun abin da za su ci.

    Waɗanda ke aiko da rahotanni kan rikicin na Gaza na fuskantar ƙangin yunwa "kamar sauran mutanen da ke yankin," in ji wata sanarwa da BBC ta fitar tare da kamfanin dillacin labarai na Faransa (AFP) da na Amurka (AP) da kuma Reuters na Birtaniya.

    "A tsawon watanni, wadannan ƴan jarida masu zaman kansu sun kasance idanu da kunnuwan duniya a Gaza", a cewar sanarwar.

    Kafafen yaɗa labarai na ƙasar waje sun dogara ne da ƴan jarida na cikin gida a Gaza, kasancewar Isra'ila ta haramta wa kafafen yada labarai, ciki har da BBC tura wakilansu zuwa Gaza.

    Hakan na zuwa ne yayin da sama da ƙungiyoyin bayar da agaji 100 da na kare hakkin bil'adama suka yi gargaɗin cewa akwai barazanar cewa mutane za su shiga mummunan hali a Gaza saboda yunwa.

    Sai dai Isra'ila, wadda ke iko da hanyoyin shigar da agaji a Gaza ta zargi ƙungiyoyin da "yaɗa farfagandar Hamas."

    Falasɗinawa 45 ne suka mutu sanadiyyar yunwa tun daga ranar Lahadin da ta gabata a yankin, kamar yadda ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hamas ta bayyana.

  16. Daga Bakin Mai Ita tare da Wasila Isma'il

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama domin kallon bidiyon.

    A wannan makon mun kawo muku tauraruwa Wasila Isma'ila wadda ta fara fitowa a wani fim mai suna Jinin Masosya a 1998.

    To sai dai tauraruwar wadda aka haifa kuma ta yi duk rayuwarta a Kaduna, ta fi shahara da sanuwa a wani fim mai suna Wasila.

    Wasila ta ƙara bayani kan dalilin da ya sa aka kwashe dogon lokaci ba a ganin ta inda ta kuma ce dole ce ta saka ta sake kamowa harkar fim saboda yanayin buƙatar iyalinta da suka haɗa da karatunsu da abincinsu da tufafinsu."

  17. ICC za ta hukunta waɗansu ƴan sa kai kan aikata laifukan yaƙi a Africa ta tsakiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun hukunta manya laifuka ta ICC na shirin yanke hukunci kan abubuwan da suka shafi laifukan yaƙi kan waɗansu ƴan yaƙin sa -kai su biyu a Jamhuriyar Africa ta tsakiya.

    Ana tuhumar Alfred Yekatom da Patrice Edouard Ngaissona da aikata laifukan cin zarafin bil’adama yayin rikicin Ƙabilanci da ya ɓarke a ƙasar a shekarar 2014.

    Su biyun, waɗanda suka musanta aikata laifukan, an kama su a shekarar 2018 bisa zargin jagorantar kungiyoyin da ke da rinjayen Kiristoci waɗanda ake zargi da kai hare-hare kan Musulmi.

    Shari'ar su ta fara gudana tun daga shekarar 2021.

    Kotun za ta yanke hukunci a yau, kuma idan aka same su da laifi, za a yanke musu hukunci.

  18. 'An samu ƙarin mutuwar mutum biyu saboda yunwa a Gaza'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ma’aikatar lafiyar Hamas ta fitar da sabuwar sanarwa kan yawan mutanen da suka mutu sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

    A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, An samu ƙarin mutuwar mutum biyu saboda matsanancin yunwa, lamarin da ya kai adadin mutanen da suka mutu a haka zuwa 113, a cewar sanarwar.

    A farkon makon nan, shugaban majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya bayyana cewa mutanen Gaza miliyan 2.1 na fuskantar matsanancin ƙarancin abinci da kayan buƙatu, inda ya ce yunwa na ƙaruwa sosai kuma

  19. Cutar kwalara ta hallaka mutum 13 a jihar Neja

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Cutar amai da gudawa wato kwalara ta ɓulla a ƙananan hukumomi shida a jihar Neja, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 13, yayin da sama da 236 suna jinya a asibiti.

    An fara samun rahoton bullar cutar ne a ƙaramar hukumar Shiroro, amma yanzu ta bazu zuwa Bosso da Minna da Magama Bida da kuma Munya.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa kwamishinan kiwon lafiya a matakin farko, Dr. Ibrahim Dangana ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa gwamnati ta ɗauki matakai daban-daban don daƙile yaduwar cutar.

    "Mun kafa wuraren keɓance marasa lafiya a kowanne daga cikin yankunan da abin ya shafa." in ji kwamishinan.

    Ya kuma ce ana gudanar da wayar da kai ga jama’a kan cutar da yadda za a kiyaye ta hannun ƙungiyoyin addini da masarautu takwas na jihar.

    Gwamnatin jihar ta kuma buɗe wuraren keɓance marasa lafiya a tsohuwar asibitin Idris Ibrahim Kuta da ke Minna.

    Daraktan lafiyar jama’a, Dr. Ibrahim Idris, ya tabbatar da cewa Minna da Bosso da Shiroro sune wuraren da cutar ta fi ƙamari.

  20. Amurka da Isra’ila za su tattauna a Italiya kan tsagaita wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Jakadan Amurka na musamman a Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, na ziyara a ƙasar Italiya domin ganawa da manyan jami’an Isra’ila da Qatar kan yiwuwar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.

    Rahotanni sun bayyana cewa za a tattauna shirin tsagaita wuta na kwanaki 60 da ƙarin damar kai agaji zuwa ga Falasɗinawa, da kuma sakin fursunonin Isra’ila da Hamas ke riƙe da su.

    Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Isra’ila ta tabbatar da karɓar martanin da Hamas ta bayar kan tayin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kuma tana nazarin abun da ke cikinta.

    Sai dai ba a bayyana cikakken bayani game da wannan sabon tayin ba tukuna.

    A farkon wannan watan, wasu jami’an Falasɗinawa da ke da masaniya kan tattaunawar sun shaida wa wakilin BBC da ke Gaza, Rushdi Abualouf, cewa shawarwarin da ake yi tsakanin Hamas da Isra’ila kan sabon yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin fursunoni na dab da rushewa.