Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a13 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Macron ya buƙaci ƙasashen Turai su ɗauki tsauraran matakan kare nahiyar

    Shugaba Macron na Faransa ya yi kira ga ƙasashen Turai su ɗauki tsauraran matakan kare nahiyari, yana mai kira ga sauran shugabannin nahiyar su yi watsi da kallon da wasu ke yi wa yankin na jan ƙafa a wasu fannoni ciki har da na yancin faɗin albarkacin baki.

    Yana mayar da martani ne kan iƙirarin da mataimakin shugaban Amurka, JD ya yi kan nahiyar a shekarar da ta gabata.

    Mista Macron ya shaida wa babban taron tsaron nahiyar Turai na bana cewa ƙasashen Turai na da asali da tarihin tabbatar da ƴanci, wadda ta kawar da adawa da yaƙe-yaƙen da aka kwashe ɗaruruwan shekaru ana yi.

    Ya ƙara da cewa dole ne nahiyar Turai ta ƙara ƙarfafa kanta domin bayar da kariya ga ƙawayenta.

  2. Jam'iyyar BNP na son a tasa ƙeyar Sheikh Hasina zuwa gida

    Sheikh Hasina

    Asalin hoton, Reuters

    Jim kaɗan bayan nasarar da ta yi a zaɓen ƙasar, jamiyyar Bangladesh Nationalist Party ta ce za ta matsa wa Indiya lamba don tisa ƙeyar hambararriyar firaminista Sheikh Hasina zuwa Bangladesh domin a yi mata shari'a.

    Shugaban jamiyyar, kuma Firaminista mai jiran gado, Tarique Rahman ya nuna godiyarsa ga magoya baya da masu yi masa fatan alkhiari a Dhaka, inda ya ce yana farinciki da soyayyar da suka nuna masa.

    Daga nan kuma ya tafi masallaci domin gudanar da sallahr Juma'a.

    Wani gagarumin abu da ke gabansa shi ne dawo da daidaito a fannoni masu muhimmanci - ciki har da masana'antar yin tufafi - bayan halin ha'ula'i da suka shiga tsawon watanni 18 bayan kifar da gwamnatin Sheikh Hasina da aka bayyana da mai mulkin kama karya.

    Tun da farko Shugaban hukumar zaɓen ƙasar ya ce Bangladesh ta samu gagarumin nasara, bayan gudanar da zaɓe mafi inganci a cikin shekaru wanda ya samar da sahihin sakamako.

  3. Amurka ta fara sassauta wa Venezueal takunkumai

    A wani mataki na sassauta takunkumai ga Venezuela tun bayan tumɓuke Shugaba Nicolas Maduro, gwamnatin Amurka ta sahale wa wasu manyan kamfanonin mai biyar su koma aiki haƙar man fetur da iskar gas a ƙasar.

    Ma'aikatar baitul malin ƙasar ta bayar da lasisi ga kamfanonin Chevron da BP da Eni da Shell da kuma Repsol.

    Haka ma ma'aikatar ta bayar da dama ga kamfanonin ƙasashen duniya daga ko'ina, su shiga zawarcin zuba jari a harkar man ƙasar, sai dai ta keɓe ƙasashen Rasha da China da kuma Iran.

    Venezuela ce ƙasar da fi kowace ƙasa a duniya manyan rumbunan man fetur jibge ƙarƙashin ƙasa da ba a tono ba.

    Kuma Shugaba Trump na cikin zaƙuwar tono shi ta hanyar amfani da kuɗin man ƙasar da Amurka ke iko da su.

  4. Kotu ta yanke wa Samha hukuncin ɗaurin wata shida

    Samha M Inuwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta yanke wa jarumar fina-finan Kannywood Samha M Inuwa hukuncin ɗaurin wata shida saboda samunta da laifin wulakanta naira.

    Makonni biyu da suka gabata ne jami'an hukumar EFCC, mai yaƙi da almundahanar kuɗi a Najeriya ta suka kama jarumar bayan ɓullar wani bidiyo da a ciki take face majina da takardar naira 1,000.

    Jaridar Daily Nigerian ta ce an gurfanar da matashiyar jarumar a gaban kotu bisa zargin, wanda EFCC ta ce ya saɓa wa sashe na 21 na dokar CBN ta 2007.

    Samha M Inuwa ta amsa lafin da ake zarginta da shi, tare neman sassauci daga kotun, tana mai cewa wannan ne karon farko da aka sameta da laifi.

    Daga nan ne kuma alƙalin kotun, Maishari'a M.S Shuaibu ya yanke mata hukuncin ɗaurin wata shida a gidan yari tare da zaɓin biyan tarar naira 200,000.

  5. Bikin kamun Kifin Argungu 2026: Hotunan yadda aka yi wasanni a rana ta uku

    Wasu ƴan mata
    Bayanan hoto, Wasu ƴanmata da suka gudanar da wasanni a bukukuwan da aka gudanar ranar Juma'a

    An ci gaba da gudanar da wasanni a rana ta uku na Bikin Kamun kifin Argungu da ke jihar Kebbi.

    Wasan tseren kwale-kwale

    A yau an gudanar da wasanni daban-daban da suka haɗa da na kamun kifin ƴanmata da tseren kwale-kwale da wasannin ninƙaya da sauransu

    wasu mutane

    Bikin - mai ɗimbin farin jini - ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen Najeriya

    Wasu mutane

    A gobe Asabar ne za a gudanar da mafi ƙololuwar wasa a bikin, wanda shi ne gasar kamun kifin da ya fi kowane girma, a gaban ɗimbin mutane.

    mutane
  6. Ukraine ta gano gawarwakin ƴan Najeriya da aka kashe cikin sojojin Rasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar leƙen asirin Ukraine, UDI ta bayyana cewa ta gano wasu ƴan Najeriya biyu da aka kashe a matsayin sojojin hayar Rasha a yayin farmakin da suka kai yankin Luhansk.

    Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya tare da hotunan mutanen, inda ta nuna su kafin mutuwarsu da kuma wani hoto da ya shafi iyalan ɗaya daga cikinsu.

    Wannan na zuwa ne makonni biyu bayan samun labarin rasuwar wani matashi a Kano wanda ake zargin ya shiga aikin sojin haya na ƙasar Rasha.

    Bayanan da jami’an leƙen asirin sojin Ukraine a yankin Luhansk suka fitar sun bayyana sunayen mutanen da Hamzat Kazeen Kolawole da kuma Mbah Stephen Udoka.

    Sanarwar ta ƙara da cewa mutanen biyu sun yi aiki a bataliyar sojin Rasha ta 423 mai kula da tankokin yaƙi.

    Rahotanni na cewa ba su kaɗai ba ne suka shiga aikin soja a Rasha, domin akwai ƴan Najeriya da dama, ciki har da wasu daga Kano.

  7. Ƙungiyar TPLF ta zargi Habasha da saɓawa yarjejeniyar zaman lafiya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Tigray People’s Liberation Front TPLF ta zargi gwamnatin tarayyar Habasha da sabawa yarjejeniyar zaman lafiya ta Pretoria ta hanyar sanya takunkumi kan ayyukan jin kai da sabunta rikici a yankin Tigray.

    Shugaban ƙungiyar, Debretsion Gebremichael, ya yi gargadi cewa ba za su zauna shiru ba idan kiran neman zaman lafiya ya ci tura.

    A wata sanarwa ga manema labarai da aka yi a ranar 12 Fabrairu 2026, Debretsion ya ce halin da ake ciki a Tigray ya yi kama da yi wa wurin kawanya da aka fuskanta a lokacin yaƙin 2020–2022.

    Ya yi kira ga cikakken aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta Pretoria, inda ya ce: “Idan gwamnati ta ki amincewa da kiran zaman lafiya, kuma halin ya ci gaba da tsananta, ba za mu zauna mu zuba ido ba.”

    TPLF ta ce manyan sassa na yarjejeniyar zaman lafiya ba a aiwatar da su ba a cikin shekaru uku da suka gabata, kuma ta zargi gwamnati da tayar da rikici.

    A cikin wata wasika da ta aika ranar 12 Fabrairu 2026 ga shugaban Kungiyar tarayyar Afrika AU, João Gonçalves Lourenço, shugaban Angola, da sauran shugabannin Afirka, ƙungiyar ta yi kira da a tabbatar da cikakken aiwatar da yarjejeniyar cikin gaggawa da gaskiya.

  8. INEC ta saka ranar zaɓen 2027

    ...

    Asalin hoton, Inec

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya Inec ta fitar da jadawalin manyan zaɓuɓɓukan kasar na shekarar 2027, inda ta bayyana muhimman ranakun zaɓe da na zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa da yakin neman zaɓe, da rajistar masu zaɓe.

    Hukumar ta ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya ranar Asabar, 20 ga Fabrairun 2027, yayin da zaɓen gwamna da na majalisun jihohi za su biyo baya bayan makonni biyu, wato ranar 6 ga Maris, 2027.

    Game da yakin neman zaɓe kuma, jam’iyyun siyasa da ‘yan takara za su fara yakin neman zaɓe na shugaban ƙasa da majalisar tarayya daga ranar 18 ga Nuwambar 2026 zuwa 19 ga Fabrairun 2027.

    Yakin neman yakin zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi zai fara daga ranar 15 ga Disambar 2026 kuma zuwa 5 ga Maris, 2027, awanni 24 kafin ranar zaɓe.

    Haka kuma, jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 1 ga Yuli da 30 ga Satumbar 2026, sannan su miƙa sunayen ‘yan takararsu a ranakun tsakanin 1 da 31 ga Oktobar 2026.

    Hukumar ta ƙara da cewa za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara na ƙarshe ranar 15 ga Nuwambar 2026,

  9. Wasiƙa zuwa ga Janar Murtala Mohammed

    ...

    Yau ne tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Murtala Mohammed ke cika shekara 50 da rasuwa.

    A ranar 13 ga watan Fabarairun 1976, wasu matasan hafsoshin tsaron Najeriya da suka kira kansu "masu son kawo canji" suka sanar da kifar da gwamnatin Murtala.

    Jagoransu, Bukar Suka Dimka wanda a lokacin yake da muƙamin laftanar kanal ne ya harbe shugaban ƙasa na lokacin, Murtala Muhammad a lokacin da yake tafiya a cikin mota.

    Albarkacin wannan rana mun kawo muku wata wasiƙa da muka samu daga wani marubuci, Mohammed Bala Garba Maiduguri, ya turo, lokacin yana karatu a Jami'ar Maiduguri.

    Mun wallafa wasiƙar ne shekara biyar da suka gabata, a lokacin da Janar Murtala Mohammed ya cika shekara 45 da rasuwa.

  10. INEC ta gabatar da kasafin kuɗi na naira biliyan 873 don zaɓen 2027

    ...

    Asalin hoton, Joseph Ayo Babalola University

    Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC ta yi hasashen kashe jimillar naira biliyan 873,778,401,602.08 wajen gudanar da zabukan gama-gari na shekarar 2027 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Wannan bayanin ya fito ne daga shugaban hukumar, Joash Amupitan, yayin da yake gabatar da kasafin hukumar na shekarar 2026 da kuma cikakken hasashen kuɗin gudanar da zabukan 2027 a gaban Kwamitin Hada-Hadar Zabe na Majalisar Dokoki.

    Amupitan ya bayyana cewa wannan kasafin na zaɓen 2027 daban ne daga kasafin hukumar na shekarar 2026 na naira biliyan 171,

    Shugaban INEC ya jaddada cewa tsara kasafin kuɗin zaɓ da wuri yana da muhimmanci domin tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye da kayan aiki da ake buƙata wajen gudanar da zaɓe na gaba suna nan a shirye, tare da rage matsalolin rashin isasshen kuɗi da za su iya kawo tsaiko ga gudanar da zaɓuka cikin nasara.

  11. Mataimakin shugaban Najeriya Shettima ya isa Addis Ababa don taron AU karo na 39

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa birnin Addis Ababa a ranar Alhamis domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron Majalisar Tsaro da wanzar da zaman lafiya ta Kungiyar Kasashen Tarayyar Afirka (AU) karo na 39.

    Shettima ya jagoranci wata tawaga daga Najeriya da ta sauka a filin jirgin sama na Bole kafin manyan abubuwan da za a gudanar a taron ranar 14 da 15 ga Fabrairu, 2026, kamar yadda Ministan Harkokin Waje, Jakada Yusuf Tuggar, ya sanar.

    Bayan isarsa, an tarbi Shettima da wasu manyan baƙi daga Najeriya da Ethiopia, ciki har da Ministan Kirkire-kirkire da Fasaha na Ethiopia, Dr. Belete Mola da Ministan Harkokin Wajen Ethiopia, Berhanu Tsegaye, da Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Waje, Dunoma Ahmed.

    Ministan Harkokin Waje ya bayyana wa Mataimakin Shugaban Kasa yadda taron zai gudana da kuma manufofin Najeriya a taron.

    Wannan shekarar, taron AU zai mayar da hankali kan samar da ruwa mai dorewa da ingantaccen tsaftar muhalli don cimma manufofin da aka tsara na 2063. Wannan yana da muhimmanci ga lafiya, noma, da ci gaban kasashen Afirka gaba ɗaya.

  12. Rasha ta ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Burkina Faso da Rasha sun rattaɓa hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da za ta karfafa hadin gwiwarsu, in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Burkina Faso a wani sako da ta wallafa a shafin Facebook dinsa.

    Ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu, Karamoko Jean Marie Traore na Burkina Faso da Sergey Lavrov na Rasha, sun sanya hannu kan wannan yarjejeniya da aka bayyana a matsayin “ta tarihi” yayin ziyarar tawagar Burkina Faso a birnin Moscow.

    An tsara yarjejeniyar ne don bayar da ingantaccen tsarin hadin gwiwa wanda ɓangarorin biyu suka bayyana a matsayin haɗin kai na dabaru.

    Ma’aikatar Burkina Faso ta ce wannan sabon tsarin zai maye gurbin tsarin da aka yi a baya, inda ya bayyana muhimman fannonin hadin gwiwa kuma ya nuna kusantar diflomasiyya da shugabannin Ibrahim Traore da Vladimir Putin suka fara a 2022.

    Lavrov ya sake tabbatar da goyon bayan Rasha ga yaƙi da ta’addanci a Burkina Faso, inda ya ce, “yaki da ta’addanci a yankin Sahel har yanzu yana da muhimmanci ga Moscow.”

    Ɓangarorin biyu sun kuma jaddada daidaitonsu a Majalisar Dinkin Duniya, sannan sun yi alƙawarin ƙarfafa hadin gwiwa wajen yaƙi da bayanan karya ta hanyar hadin gwiwar kafafen yaɗa labarai.

    Ana sa ran ziyarar jami’an Burkina Faso za ta haifar da karin yarjejeniyoyi, wanda zai ƙara zurfafa dangantakar ƙasashen biyu.

  13. China ta yi watsi da zargin Amurka na ruruta wutar rashin tsaro a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar China ta yi watsi da zargin da wasu mambobin majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ƙasar na tallafa wa ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Najeriya tare da biyan wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai domin kare muradun kasuwancinsu.

    Ofishin jakadancin China a Abuja ya bayyana zargin a matsayin “mara gaskiya wanda bai da tushe, kuma yana cutar da dangantaka tsakanin China da Najeriya.”

    Zargin ya samo asali ne daga wani ƙudirin neman a dauki mataki kan Najeriya bisa zargin musguna wa Kiristoci, wanda ya hada da batun cewa masu aikin haƙar ma’adinai na China a Najeriya na biyan kuɗaɗe ga wasu ƙungiyoyin masu dauke da makamai.

    Rahotanni daga shekarar 2023 sun nuna cewa wasu ‘yan ƙasar China da ke haƙar ma’adinai a wurare kamar Zamfara na iya kasancewa sun taimaka kai tsaye ko a kaikaice wajen tallafa wa ƙungiyoyin masu dauke da makamai da ke neman mallakar wuraren hakar ma’adinai masu riba.

    Ofishin jakadancin dai ya jaddada cewa yawancin kamfanonin hakar ma’adinai na China a Najeriya suna bin dokokin ƙasa, suna bayar da gudummawa ga al’umma ta hanyar samar da ayyukan yi da tallafa wa ci gaban cikin gida.

  14. Jam’iyyar BNP ta lashe zaɓen Bangladesh bayan zanga-zangar matasa

    ....

    Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

    Jam’iyyar Bangladesh Nationalist BNP ta samu gagarumar nasara a zaɓen kasar Bangladesh da aka gudanar, wanda shi ne na farko tun bayan zanga-zangar matasa ta shekarar 2024 da ta hamɓarar da tsohuwar firaminista Sheikh Hasina daga mulki.

    Sama da mutane miliyan 120 ne suka kaɗa kuri’unsu a zaɓen da ake ganin zai bude sabon babi na siyasa a kasar.

    Rahotanni sun ce zaɓen ya gudana cikin yanayi na sa ido daga cikin gida da wajen kasar, inda masu kaɗa kuri’a suka fito tun safiyar jiya Alhamis domin zaben sabuwar gwamnati.

    Wannan shi ne karo na farko da aka haɗa zaɓen majalisar dokoki da kuri’ar raba gardama a rana guda a tarihin kasar.

    Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce sakamakon nasarar jam’iyyar ta BNP na nuni da gagarumin sauyi a ra’ayin jama’a, musamman bayan shekaru 15 na mulkin da ake zargin ya takaita ‘yancin siyasa.

    Wasu ‘yan kasa na fatan sabon salon shugabanci zai mayar da hankali kan wakilci, adalci, da inganta tattalin arziki.

  15. EFCC sun gayyace ni - El-Rufai

    ...

    Asalin hoton, X/Nasir El-Rufai

    Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa hukumar EFCC ta aika masa da takardar gayyata zuwa ofishinta, kuma ya amince zai je.

    Ya bayyana haka ne a wata hira da BBC inda ya ce "Efcc sun rubuto min takadar gayyata zuwa ofishinsu, kuma na amsa musu zan je ranar Litinin mai zuwa"

    Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da ta ce jami’an tsaro sun ƙwace fasfon ɗin El-Rufai a Filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe jim kaɗan bayan dawowarsa daga Masar.

    Mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya wallafa a shafinsa na X cewa "jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama shi ne bayan dawowarsa gida daga ƙasar Masar."

    Da yake bayani kan bidiyon da ya bazu a shafukan sada zumunta, El-Rufai ya ce ba shi ne ke sa’in-sa da jami’an DSS ba, illa su ne suka tare shi a filin jirgi suka buƙaci ya bi su ofishinsu.

    A cewarsa "Ina sauka daga jirgin wani dan matashi ya zo ya ce min sun zo ne daga DSS, kuma suna son su gan ni a ofisihinsu sai na ce ina takardar gayyata, sai suka ce min akwai takarda, za a bani,"

    Ya ce da suka fito waje sai wasu manyan jami’an DSS suka sake tare shi, sai ya sake tambayarsu takardar gayyata.

    Ya ce ya shaida musu gidansa na kusa da ofishinsu, don haka su je su kawo takardar idan har akwai.

    Ya ƙara da cewa babu wata doka a Najeriya ko kundin tsarin mulki da ta ba da damar a tare mutum ba tare da takarda ba.

    El-Rufai, wanda ke cikin jagororin adawa a jam’iyyar ADC da ke shirin ƙalubalantar shugaban ƙasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa, ya zargi gwamnatin APC da yi wa ƴan adawar da suka ƙi sauya sheƙa zuwa jam'iyyar barazana ta hanyar kama su da sunan bincike kan ayyukan rashawa.

    Ya ce an kama kusan mutum huɗu da suka yi aiki tare da su a Jihar Kaduna, yana mai cewa yana ganin lokaci ne kafin a neme shi ma.

  16. Abin da ya sa na ƙi bin jami’an tsaron da suka so su kama ni - El-Rufai

    ....

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce babu wani nau'in bita da ƙulli da zai hana shi ci gaba da adawa da gwamnatin Najeriya, wadda ya ce ta jefa al'ummar ƙasar cikin mummunan yanayin da dole a tashi domin yaƙi da shi.

    A ranar Alhamis 12 ga watan Faburairun 2026 jami'na tsaron Najeriya suka yi yunƙurin kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja babban birnin Najeriya, jim kaɗan bayan saukar sa a Najeriya daga ƙasar Masar lamarin da ya janyo sa-in-sa a tsakanin su.

    A hirar shi ta farko da BBC bayan dambarwar, Nasir El-Rufai ya yi bayanin abin da ya faru lokacin da jami'an tsaro suka yi yunƙurin kama shi.

    Ya ce jayayyar ta taso ne lokacin da jami'an tsaron suka nemi ya bi su zuwa ofishin su domin ''ana son ganin shi'' a can, shi kuma ya nemi su nuna mashi takardar gayyata a hukumance, lamarin da kuma ya ci tura saboda babu takardar a tare da su.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da aka kira da juma'atu babbar rana.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.