Nawa jihohin Najeriya ke samu daga tarayya kuma yaya suke kashe kuɗin?

Tinubu

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya/X

Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya sun ci gaba da muhawara kan maƙudan kuɗaɗen shiga da matakan gwamnati uku suka raba a Najeriya cikin watan Janaurin da ya gabata.

Hukumar raba arzikin ƙasar, FAAC ta ce matakan gwamnatin uku, wato gwamnatin tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukukomi sun raba naira tiriliyan 1. 963 a watan da ya gabatan.

Cikin wata sanarwar darakta yaɗa labaran ofishin babban akanta na ƙasa , Bawa Mokwa ya fitar a farkon makon da muke ciki ya ce an samu nasarar tara kuɗaɗen ne ta hanyar harajin cikin gida da aka tara a watan na naira tiriliyan 1.08 da kuma naira biliyan 846.507 da aka tara daga harajin VAT, sai kuma naira biliyan 38.110 da aka tara daga harajin tura kuɗaɗe ta intanet.

Sanarwar ta ce bayan kasafta kuɗaɗe gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 653.500, yayin da jimillar jihohin ƙasar 36 da birnin Abuja suka samu naira biliyan 706.469, sai kuma ƙananan hukumomi da suka samu naira biliyan 513.272.

Sai kuma jihohin da ke samar da man fetur da aka basu naira biliyan 96.083 a matsayin kaso 13 da ake bai wa jihohin da suka fi tara kuɗin haraji (derivation).

Lamarin ya sake farfaɗo da muhawarar da ake yi a ƙasar kan yadda jihohin ke samun kuɗaɗen gudanar da ayyuka.

'Ƙaruwar kason jihohi bayan cire tallafin man fetur'

Tun bayan cire tallafin man fetur a 2023, Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙara wa jihohin ƙasar kuɗaɗen shiga domin gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Cikin wata hira da BBC a baya-bayan nan gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya tabbatar da cewa jihohin ƙasar na samun ''maƙudan'' kuɗi daga tarayya domin gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Gwamnonin dai na cewa suna amfani da kuɗaɗen wajen biyan albashin ma'aikata da ayyukan more rayuwa a jihohinsu.

To sai dai a gefe guda, wasu mutane kan soki gwamnonin da rashin gudanar ayyukann da suka kamata,

Inda wasu ke zargin gwamnonin da tara kuɗin yaƙin neman zaɓukansu a shekarar 2027.

Me gwamnonin ke yi da kuɗaɗen?

Tinubu

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

Dokta Murtala Abdullahi Ƙwara malami a tsangayar koyar da tattalin arziki na Jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua da ke Katsina ya ce galibi ayyukan yau da kullum gwamnonin ke yi da kuɗaɗen da suke samu daga asusun tarayya.

''Na farko akwai biyan albashi da yin wasu manyan ayyuka'', in ji shi.

Malamin Jami'ar ya ce da irin waɗannan kuɗaɗen ne gwamnoni ke amfani da su wajen gudanarwar yau da kullum da a turance ake kira ''Re-current expenditure''.

Ya ce mafi yawan jihohin arewacin ƙasar da ba su da hanyoyin kuɗin shiga da irin waɗannan kuɗaɗen ne suka gudanar da ayyukan gwamnati.

''Gudanarwar yau-da-kullum ya ƙunshi kuɗaɗen da ake kashewar wajen sayen man fetur da tayar da injuna da sayen takardu da abubuwan rubutu da biyan alawus da sauran ayyukan gudanarwa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Kuɗaɗen da jihohin ke samu na wadatarsu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dokta Abdullahi Ƙwara ya ce zai yi wahala a ce waɗannan kuɗaɗe suna wadatar jihohin.

''Idan kana maganar wadatuwa, za ka yi la'akari da abubuwa biyu, na farko yawan kuɗin da kuma girman jihar'', in ji shi.

Malamin jami'ar ya ce inda kuɗaɗen na isar jihohin to ya kamata a same su cikin wadatar al'amura, a samu arziki babu talauci da matsin tattalin arziki.

''Amma kullum gwamnonin jihohin suna kukan rashin kuɗin gudanar da manyan ayyuka to ka ga ai za a ce kuɗin ba sa wadatarwa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa a duk lokacin da aka tuntuɓi gwamnonin jihohin da ayyukan da suka shafi ci gaban al'umma kamar ƙarin albashi, za a ji suna ta ƙorafin rashin kuɗi.

Dokta Ƙwara ya ce wannan kuma ba abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da gwamnati, wadda dama ita buƙatunta na da matuƙar yawa.

Sai dai ya soki yadda wasu gwamnonin ke tafiyar da kuɗaɗen wata-watan da suke samu daga kaso tarayya.

Ya zargi wasu gwamnonin da ɓarnatar da kuɗaɗen wajen gudanar da ayyuka ko bayar da kwangila.

Jihohi za su iya ayyuka ba tare da kuɗin tarayya ba?

Ƙwararren masanin tattalin arzikin ƙasar ya ce kaso mafi yawa na jihohin Najeriya ba za su iya tsayuwa da ƙafarsu ba matuƙar babu wannan kaso na tarayya.

Wasu alƙaluma daga hukumar ƙiddigar ƙasar sun nuna cewa jihohin ƙasar bakwai ne suke da ƙarfin hanyoyin samun kuɗin shiga.

Dokta Ƙwara ya ce galibi waɗannan jihohin ba a arewacin Najeriya suke ba.

Don haka ne ya ce mafi yawan jihohin ƙasar a yanzu ba za su iya riƙe kansu ba matuƙar babu kason tarayyar.

Sai dai ya ce idan jihohin za su mayar da hankali su gyara tare da inganta hanyoyin samun kuɗin shigarsu, to lallai za su iya tsayawa da ƙafafunsu ko da babu kason tarayyar.

Me ya sa jihohi ke kukan rashin kuɗi?

Dokta Murtala Abdullahi Ƙwara ya ce mafi yawan gwamnonin jihohin sun fi fifita karkatar da kuɗaɗen don amfanin kansu, maimakon ci gaban jihar.

''Galibin gwamnonin suna tara kuɗin ne domin samun ƙarfi wajen yaƙin neman zaɓen gaba, ko karkatar da su don mallakin kansu'', in ji masanin tattalin arzikin.

Ya ce wannan ne dalilin da ya sa talakawa ba sa gani a ƙasa.

''Tabbas gwamnatin tarayya a yanzu na bai wa gwamnoni maƙudan kuɗaɗen da ba a taɓa gani ba a tarihi, amma gwamnonin ba sa gudanar da ayyukan yadda ya kamata''.

''In ma za su yi aikin to ya ta'allaƙa ne kan abin da za su fitar da kuɗaɗe su saka a aljihunsu, ko ɗan ƙaramin aiki a zuga masa kuɗaɗen da hankali ma ba zai ɗauka ba'', in ji malamin jami'ar.