Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Asalin hoton, X/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.
A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.
"Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al'ummar jihar hakkinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.
''Na yi iyakar bakin kokarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.''
Tinubu ya bayyana cewa babu wani shugaban ƙasa nagari da zai zura ido yana kallon abin da ke faruwa ba tare da bin matakan da kundin tsarin mulki ya tanada ba wajen ganin an shawo kan matsalar ta jihar Rivers.
A cikin jawabin da ya gabatar ta kafafen talabijin na ƙasar, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce: ''Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
"A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025."
"Da wannan bayani, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Mrs Ngozi Odu da kuma dukkanin zaɓaɓbun ƴanmajalisar dokokin jihar Rivers, an dakatar da su na wata shida, a matakin farko."















