Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Laraba 8/4/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 8 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Dole Amurka ta zaɓa ko tsagaita wuta ko yaƙi ta hannun Isra'ila

    A

    Asalin hoton, MARTIAL TREZZINI/EPA/Shutterstock

    Dole Amurka ta zaɓa tsakanin tsagaita wuta ko a ci gaba da yaƙin ta ƙarƙashin Isra'ila in ji ministan harkokin wajen Iran bayan wasu jerin hare-hare kan Lebanon.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Seyed Abbas Araghchi ya ce abubuwan da ke cikin yarjejeniyar a buɗe suke kuma a fayyace.

    Firaministan Iran ɗin ya wallafa sanarwar tasa haɗe da ta yarjejeniyar tsagaita wutar da Firaiministan Pakistan Shehbaz Sharif, ya na nuna yadda sharrif din ya ayyana cewa yarjejeniyar za ta haɗa Lebanon.

  2. "Isra'ila ta kashe mutum 254 a harin da ta kai Lebanon"

    a

    Asalin hoton, Mohammad Abushama / Anadolu via Getty Images

    Hukumar kare fararen hula ta Lebanon ta ce aƙalla mutane 254 ne suka mutu, yayin da sama da 1,100 suka jikkata, sakamakon mafi munin hare-haren da Isra’ila ta kai tun bayan sake ɓarkewar yaƙin da ƙungiyar Hezbollah.

    An kai hare-haren ne sa’o’i kaɗan bayan da Amurka da Iran suka sanar da tsagaita wuta na makonni biyu.

    A cewar wata likitar ƙungiyar agaji ta MSF, sun karɓi iyalai da dama da suka garzayo asibiti ɗauke da munanan raunuka, awanni ƙalilan bayan dawowarsu daga gudun neman tsira.

    Isra’ila dai ta dage cewa Lebanon ba ta cikin yarjejeniyar tsagaita wutar, wani matsayi da Shugaban Amurka Donald Trump ya goyi baya.

    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hari kan wuraren Hezbollah kusan 100 cikin mintuna 10 kaɗai.

    Kungiyar Hezbollah ta ce tana da cikakkiyar ‘yancin mayar da martani.

  3. Shugaban INEC ya ja kunnen kafafen yaɗa labarai

    a

    Asalin hoton, inec x

    Shugaban hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Joash Amupitan ya gargaɗin gidajen yaɗa labarai kan yaɗa labaran bogi, yana gargaɗin cewa sahihancin zaɓen 2027 na wuyan yadda kafafen yaɗa labaran Najeriya suke bayyana abubuwan da ke faruwa.

    Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron kafafen yaɗa labarai Najeriya karo na 81 da ya gudana a yau Laraba, inda ya nanata cewa fagen yaɗa labarai ya zama wani sabon dandalin yaƙin neman zabe na zamani.

    Yana cewa babu wata barazana kan gudanar da sahihin saɓe, sai dai yadda kafafen yaɗa labarai marasa sahihanci kan haifar da barazanar hakan ta hanyar yaɗa labaran ƙanzon gurege.

    Farfesa Amupitan ya nanata buƙatar bin dokar aikin watsa labaran siyasar ta 2026, wadda idan aka bi ta za a samu saukin abubuwan da ke faruwa.

    A

    Asalin hoton, INEC X

  4. Tattaunawar ADC da PDP a Abuja cikin hotuna

    Jam'iyyun biyu na tattaunawa ne kan yiwuwar haɗin gwiwa domin tunkarar matsalar shugabanci da ta dabaibaye su, da kuma fuskantar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

    A

    Asalin hoton, PDP X

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Oyo Sheyi Makinde da Atiku Abubakar da kuma shugaban jam'iyyar ADC David Mark
    A

    Asalin hoton, PDP x

    Bayanan hoto, Tsohon ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami da Tsohon gwamnan Neja Babangida Aliyu da Tsohon ɗan takarar Shugabancin Najeriya Peter Obi
    A

    Asalin hoton, PDP X

    Bayanan hoto, Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da Tambuwa da Babangida Aliyu da Peter Obi da Malami da Sauransu
    A

    Asalin hoton, PDP X

    Bayanan hoto, Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubkar yayin da yake gaisawa da wasu mahalarta taron da aka yi a Abuja
    A

    Asalin hoton, PDP X

    Bayanan hoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da mabobin ADC da PDP mahalarta taron
  5. Farashin ɗanyen mai ya faɗi a duniya bayan tsagaita yaƙin Iran da Amurka

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen mai ya sauka ƙasa da dala $95 a kasuwar man tun safiyar Laraba bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.

    Farashin ɗanyen man na duniya ya faɗi da kashi 13 inda yake tsakanin dala 94 zuwa 95 kowacce ganga, wanda shi ne saukar farashin mafi sauri da aka gani a shekarun bayan nan, bayan tashin farashin da aka ganin sanadiyyar rikicin da aka kwashe makonni ana yi.

    Sauyin na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da shirin tsagaita wuta na makonni biyu, wanda ya dakatar da hare-haren soji da kuma buɗe mashigar Hormuz mai mahimmanci.

    Sai dai har ya zuwa yanzu ana ci gaba da samun hare-hare daga Isra'ila wadda ta ce ita ba ta cikin wannan yarjejeniya.

  6. Shugabanin ADC na tattaunawa da PDP bayan kammala zanga-zanga

    A

    Asalin hoton, PDP X

    Shugabannin ADC da na PDP ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki na wata tattaunawar sirri a Abuja.

    Cikin waɗanda suke halartar taron akwai Sanata David Mark shugaban ADC na ƙasa da kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso, da tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar Labour Peter Obi.

    A

    Asalin hoton, PDP X

    Akwai kuma tsohon Ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami da tsohon sakataren gwamnati Babachir Lawal, da tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi da Sanata Aminu Tambuwal

    A ɓangaren PDP akwai Gwamnan Oyo Seyi Makinde da Shugaban tsagin jam'iyyar PDP na ƙasa Turaki Farfesa Jerry Gana da tsohon shugaban jamalisar dattijai Adolphus Wabara, Tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da wasu sauran Mambobi.

    A

    Asalin hoton, PDP X

  7. Za mu fice daga yarjejeniyar tsagaita wuta idan Isra'ila ba ta daina kai wa Lebanon hari ba - IRGC

    Rundunar sojin juyin juya hali ta Iran ta yi barazanar katse yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma saboda hare-haren da Isra'ila ke kai wa Lebanon.

    Rundunar ta ce idan dai har hare-haren na Isra'ila ba su dakata ba to za su kai hare-hare kan Isra'ila.

    A wani saƙo ta Instagram, rundunar ta ce "muna yin kakkausan gargaɗi ga Amurka da Isra'ila.

    Idan har hare-hare a kan Lebanon ba su dakata ba cikin gaggawa to za mu kai hare-haren ramuwar gayya a yankin Gabas ta Tsakiya."

    In a message on Telegram, the outlet says: "We have a stern warning to the oath-breaking United States and its Zionist partner in slaughter.

    Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya rawaito rundunar na cewa " kai hari kan Hezbollah tamkar hari ne kan ƙasar Iran."

  8. Shugaban APC na ƙasa ya je Kano zawarcin Shekarau

    A

    Asalin hoton, X Nentawe

    Shugaban jam'iyyar APC mai mulki Nentawe Yilwatda ya kai ziyara kano domin zawarcin tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau.

    Shugaban ya kai ziyarar ne a yau Laraba a wani mataki na ƙoƙarin jam'iyyar na zawarcin manya-manyan 'yan siyasar jihar yayin da ake tsaka da yin haɗakar jam'iyyu gabanin zaɓen 2027 mai zuwa.

    Cikin waɗanda suka halarci zaman a gidan tsohon gwamnan akwai Senator Bello Hayatu Gwarzo.

    Da yake bayani yayin ziyarar, Nentawe ya nemi 'yan siyasar biyu da su koma APC, inda ya bayyana kansa a matsayin ɗansu wanda yake buƙatar taimakonsu da shiryarwarsu.

    "Ku zo ku taimaka mani, ni ɗanku ne, ina buƙatar goyon bayanku, ina son bin tafarkin da kuka bi. Ina roƙonku kuzo ku taimaka mani," in ji Shugaban.

    Ya kuma yi kira ga mambobin jam'iyyar da su ƙara ƙaimi wajen fahimtar da shugabannin da su sake komawa APC inda ya ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin 'yan siyasar arewaci.

    A nasa ɓangaren Malam Shekaru yace ziyarar suna kallonta a matsayin maƙurar nuna girmamawa da maida hankali kan abin da aka sa gaba.

  9. Zimbabwe za ta fara sanya takunkumin yawan sinadarin lithium da ake fitarwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Zimbabwe ta ce za ta fara sanya takunkumin yawan sinadarin lithium da ake fitarwa, tare da buƙatar kamfanoni su ƙara zuba jari a sarrafa shi a cikin gida, kafin a ba su damar fitar da shi kasashen waje.

    Hukumomi sun kuma buƙaci kamfanonin haƙar ma’adanai su riƙa bayyana kudaden shiga da suka samu, tare da bin ka’idojin aiki da tsaro.

    Masu zuba jari daga China na sanya hanun jarin biliyoyin daloli ga sabbin kamfononi sarrafa sinadarin lithium, wanda ake gani a matsayin matakin farko na bunkasa tattalin arziki tin daga tushe.

    Zimbabwe, wadda ita ce kasar da ta fi samar da sinadarin lithium a Afirka, ta sanya dokar hana fitar da shi a watan Fabrairu domin bunkasa sarrafa shi a cikin gida. Karshen labaran duniyar kenan daga nan sashen Hausa na BBC.

  10. Sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare mafi muni a Lebanon

    Ministan lafiya na Lebanon ya ce daruruwan mutane ne suka jikkata wasu kuma suka mutu a sassan kasar, bayan da sojojin Isra’ila suka kaddamar da mafi munin hare-hare, tun bayan ɓarkewar sabon rikici tsakanin su da ƙungiyar Hezbollah.

    Ministan ya ce asibitoci sun cika makil da waɗanda suka jikkata.

    An kai hare-haren ne a yankuna da suka haɗa da Beirut da Sidon, inda rundunar sojin Isra’ila ta ce farmakin ya kasance mafi kyau da aka kai kan cibiyoyin Hezbollah da kayayyakin soji sama da Ɗari.

    Babban hafsan sojin Isra’ila ya ce rundunar IDF za ta ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah, duk da cewa Pakistan wadda ta shiga tsakani wajen samar da tsagaita wuta da Iran, ta ce wannan bangaren na yakin shi ma za a dakatar da shi.

    A baya dai, ƙungiyar Hezbollah ta bukaci magoya bayanta da su kara hakuri da juriya da kuma jajircewa.

  11. Kalli yadda mutanen Iran ke murna bayan yarjejeniyar tsagaita wuta

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Mutane sun taru a Tehran suna kaɗa tuta da rera waƙoƙi bayan Iran da Amurka sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Iran ta amince ta bar jiragen ruwa su riƙa wucewa ta mashigar Hormuz idan Amurka ta daina kai mata hari.

    An cimma yarjejeniyar ne bayan sama da wata daya da aka kwashe ana gwabza yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.

  12. Najeriya za ta fara shari'ar mutum 500 da ake zargi da ta'addanci

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya na ci gaba da shari’ar fiye da mutum 500 da ake zarginsu da hannu a hare-haren ‘yan ta-da-ƙayar-baya da suka janyo mutuwar dubban mutane, a ɗaya daga cikin shari’o’in ta’addanci mafi girma a ƙasar.

    Ministan Shari’ar ƙasar, Lateef Fagbemi ya ce shari’ar ta fara ne da gurfanar da mutum 227 da ake zargi a gaban alƙalai guda goma.

    Ana zargin waɗanda ake ƙarar da hannu wajen kai hare-hare akasari a sassan arewacin Najeriya, inda ayyukan tarzoma masu alaƙa da ‘yan ta-da-ƙayar-baya suka yi sanadin kashe fiye da mutum dubu biyu da raba ɗumbin wasu da gidajensu.

    Sauran na fuskantar tuhume-tuhume a kan goyon bayan ‘yan ta-da-ƙayar-baya ta hanyar ba su kuɗaɗe da kai musu makamai da sauran kayan buƙatun rayuwa.

    Ministan shari’ar ya ce girman wannan shari’a ya nuna ƙudurin gwamnatin Nijeriya na tabbatar da ganin an bi ƙa’ida yayin da ake ƙoƙarin ganin hukunci ya yi aiki a kan masu hannu a ayyukan ta’addanci.

    An tsaurara matakan tsaro da suka haɗa da na sojoji da ‘yan sanda da jami’an leƙen asiri.

    Masu sa-ido na duniya ciki har da ƙungiyoyin kare ‘yancin ɗan’adam da ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya sun hallara a kotun.

    A ranar Talata ne aka yanke wa mutum biyar hukuncin ɗaurin shekaru daban-daban a gidan yari bayan sun amsa laifi kan tuhume-tuhumen da suka haɗar da sayar da dabbobi da kai kayan abinci da tsegunta bayanai ga ‘yan ta-da-ƙayar-baya.

    Hukumomi sun ce za a ci gaba da shari’o’in kashi-kashi, lamarin da ke nuna cewa an kama hanyar ɗaukan wani ƙwaƙƙwaran mataki game da rikicin ta-da-ƙayar-bayan da ya daɗe yana tagayyara sassan Nijeriya.

  13. Ƙasashen Kuwait da UAE sun ce har yanzu suna fuskantar hare-hare daga Iran

    Ƙasashen Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce har yanzu suna fuskantar hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka harba daga Iran, duk da tsagaita wutar da aka cimma.

    Rundunar sojin Kuwait ta ce garkuwar tsaron sararin samaniyarta na kakkaɓe wani yunƙuri na jirage marasa matuka daga Iran, inda wasu daga ciki ke nufar wuraren haƙar mai da tashoshin wutar lantarki.

    Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce tana tinkarar wata barazanar makamai masu linzami.

    Ƙasashen yankin Gulf sun yi maraba da tsagaita wutar, sai dai Oman wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga Tsakani, ta jaddada bukatar gudanar da tattaunawa mai mahimmanci domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

  14. Tsagaita wutar Amruka da Iran wata dama ce ta samun zaman lafiya na gaskiya - Hegseth

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta wata muhimmiyar dama ce ta kai wa ga zaman lafiya na gaskiya da kuma cimma yarjejeniya mai ma’ana.

    Ya ambaci wasu manyan jami’an Iran da aka kashe a yakin, ciki har da tsohon jagora Ali Khamenei, wanda ya ce an kashe shi a farkon sa’o’in fara yakin.

    Hegsett ya ƙara da cewa Donald Trump tun daga farko ya bayyana ƙarara cewa Iran bai kamata ta mallaki makaman nukiliya ba, kuma a ƙarƙashin yarjejeniyar da ake tattaunawa, duk wani sinadarin nukiliya da Iran “bai kamata ta mallaka ba” za a fitar da shi daga kasar.

    Sakataren tsaron ya jaddada cewa tsagaita wutar na ba da dama wajen samun “zaman lafiya na gaskiya da yarjejeniya ta gaskiya,” yana mai cewa Ma’aikatar Tsaro ta Amurka ta riga ta “yi nata aiki a halin yanzu,” amma a shirye take ta tabbatar Iran ta bi duk sharuɗɗan da suka dace.

    A ‘yan watannin baya, shugaban Amurka ya sha sukar ƙungiyar NATO, ciki har da Firaministan Birtaniya Keir Starmer kan ƙin taimaka mata a yaƙin da take yi da Amurka

  15. Atiku, Obi da Kwankwaso sun jagoranci zanga-zangar adawa da matakin Inec

    ....

    Asalin hoton, Esther Omoh

    Fitattun ‘yan jam’iyyar haɗaka ta ADC da suka haɗa da Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ne suka jagoranci zanga-zangar nuna adawa da matakin hukumar zaɓe mai zaman kanta Inec kan jam'iyyar da suka kira da “Ceto Dimokuradiyyar Najeriya” a yau, Laraba.

    Sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka shiga zanga-zangar sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mar da, tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola, da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal, da sauran su.

    Magoya bayan jam'iyyar da dama daga jihohin ƙasar da mambobin Kwankwasiyya su ma sun halarci taron zanga-zangar domin miƙa wata wasika da ke kunshe da korafe- korafen su ciki har da maganar yin kira ga shugaban hukumar INEC da ya yi murabus.

    Zanga-zangar ta fara ne daga Maitama Roundabout a Abuja, inda ta ƙare a hedikwatar INEC.

    Masu zanga-zangar na zargin hukumar zaben da yin aiki tare da jam’iyyar APC mai mulki domin kawo cikas ga dimokuradiyyar kasar.

    An ga Amaechi yana cikin wata mota yana yi wa masu zanga-zangar jawabi yayin da suke tafiya a titunan babban birnin ƙasar.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya nuna hotuna da bidiyo yayin da yake tare da sauran masu zanga-zangar.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  16. Za muyi aiki kafaɗa da kafaɗa da Iran - Trump

    ...

    Asalin hoton, YURI GRIPAS/POOL/EPA/Shutterstock

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasar za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Iran.

    Ya kara da cewa Iran ba za ta ci gaba da bunkasa uranium ba, kuma Amurka za ta yi aiki tare da Tehran domin kwashe ɓaraguzan makaman da jirgin Amurka na B-2 ya jefa a Iran a shekarar da ta gabata.

    Ya kuma bayyana cewa, "Babu wani abu da aka taɓa tun ranar harin. Muna, kuma za mu ci gaba da tattaunawa kan sassauta haraji da takunkumi tare da Iran."

  17. Jiragen ruwa sun fara ratsawa ta mashigar Hormuz - rahoto

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani shafi da ke bibiyar jiragen ruwa na MarineTraffic ya nuna a safiyar yau cewa "jiragen ruwa sun fara ratsawa ta mashigar Hormuz bayan Iran ta rufe hanyar na ɗan lokaci.

    Shafin ya ce jirage biyu ne suka bi ta mashigar da suka haɗa da na Girka da kuma wanda aka yi wa rajista a Liberia.

    BBC ba ta tabbatar da waɗannan rahotanni ba.

    Mashigar Hormuz dai ta kasance a rufe baya fara yaƙi da Iran wanda hakan ya haifar da rikici a ‘yan amma yarjejeniyar da aka cimma na dakatar da faɗa na mako biyu na bukatar Iran ta buɗe hanyar.

    Wasu ƙasashe sun riga sun cimma yarjejeniya da Iran don jiragensu su ci gaba da amfani da hanyar mashigar ciki har da Pakistan, Indiya da Philippines.

  18. Kuwait ta ce Iran ta kai mata hari bayan yarjejeniyar tsagaita wuta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kuwait ta ce Iran ta kai mata hari da jiragen sama marasa matuƙa bayan sanarwar dakatar da wuta

    Kuwait ta bayar da rahoton ne inda ta ce harin ya faru a safiyar yau, bayan ‘yan sa’o’i da sanar da cimma yarjejeniyar dakatar da wuta tsakanin Iran da Amurka.

    A cikin sanarwar sojin Kuwait a tashar X-Channel, an ce: "Tun daga ƙarfe 8 na safiyar yau, Kuwait ta fuskanci hare-hare daga Iran amma kuma an yi nasarar kakkaɓo jirage marasa matuƙa 28 da aka kai harin da su."

    Sanarwar ta ƙara "duk da cewa an kakkaɓo makaman da aka kai wa harin da su, hare-haren sun janyo babban lalacewa ga matatun mai da tashoshin wutar lantarki, da kuma tashoshin tsarkake ruwa."

  19. 'Barazanar Trump kan Iran ta kusa jefa duniya cikin mummunar hali'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Spain, José Manuel Álvarez, ya ce barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na lalata Iran ta kusan jefa duniya cikin mummunar hali.

    A cikin wata hira a rediyo, Álvarez ya bayyana cewa wa’adin Trump "abu ne da ba za a taba tunanin irin sa ga bil’adama ba."

    Duk da haka, ya ce har yanzu lokaci bai yi ba a tantance ko rikicin ya ƙare gaba ɗaya.

    "Duk lokacin da shugaban ƙasa mai karfin soja ya yi irin waɗannan barazanar, ina ɗaukar su da muhimmanci," in ji ministan harkokin wajen Spain.

    A jiya ne Trump ‘yan sa’o’i kafin yarjejeniyar dakatar da wuta ya yi barazanar cewa za a iya lalata Irandaba ɗaya a rana guda.

  20. An kai hari kan matatar man Iran bayan yarjejeniyar tsagaita wuta

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin ƙera da rarraba man fetur na ƙasar Iran (NIOR) ya tabbatar da harin da aka kai wa matatar mai ta Lavan.

    A cikin wata sanarwa, kamfanin ya ce, "A kusan ƙarfe 10 na safiyar yau, Laraba, an kai harin ban tsoro ga matatar mai ta Lavan dake Tsibirin Lavan."

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "Ƙungiyoyin tsaro da kashe gobara na aiki domin kashe gobarar da tabbatar da tsaron wurin."

    Haka zalika, Kamfanin Labarai na Mehr ya ruwaito wasu fashe-fashe a tsibiran Lavan da Siri a Tekun Fars.

    Waɗannan fhare-hare sun faru ne a daidai lokacin da Iran da Amurka suka amince da yarjejeniya ta dakatar da wuta na tsawon makonni biyu.