Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya
Usman Minjibir, Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Tinubu/Twitter
Gwamnatin Najeriya ta ce tattaunawa ta yi nisa domin kwaso ƴan ƙasar guda 15,0000 da suke gudun hijira a ƙasashen Kamaru da Nijar da Chadi da wasu ƙasashen cikin mutunci.
Kwamishinan hukumar kula da ƴangudun hijira ta Najeriya, Alhaji Tijani Ahmed ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a Abuja a ranar Juma'a kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce akwai aƙalla ƴan Najeriya miliyan shida da ke zaman gudun hijira a cikin ƙasar, sannan akwai wasu dubbai da suke zaune a wasu ƙasashen na duniya.
"Akwai ƴan Najeriya 15,000 da suke so su dawo da kansu; haka kuma muna da ƴan ƙasashen waje aƙalla 100,000 da suke zaman gudun hijira a ƙasar nan.
"Dukkan mutanen nan suna da alhaki a hukumarmu na ba su kulawar da ta dace," in ji shi.
Ahmed ya yi godiya ga Shugaban Bola Tinubu bisa gudunmuwar da yake ba ma'aikatar jinƙai, sannan ya nanata ƙudurinsu na tabbatar da kwaso ƴan ƙasar da suke zaune a wasu ƙasashen.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴansanda a jihar Legas sun kama wani mutum mai suna Samson Oghenebreme ɗauke da kawunan mutane.
An kama matashin ne ɗan shekara 25 a anguwar Odomola bayan da jami'an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami'an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba.
Ƴansandan sun yi zargin cewa Samson yana kai kawunan jihar Edo wajen wani boka - wanda yake amfani da su don yin kuɗi, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.
Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar ta Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ya ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Kwamishinan ƴansandan jihar Olohundare Jimoh ya yaba wa jami'an ƴansanda da na bijilanti kan ɗaukar matakin da ya dace da sauri.
Ya kuma buƙaci dukkan ƴan jihar Legas da su riƙa sa ido da kai rahoton abin da ba su yarda da shi ba zuwa ga ofishin ƴansanda mafi kusa.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu mahara sun tare wata babbar hanyar a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, inda suka kashe aƙalla mutum uku, sannan suka jikkata wasu da dama.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Henry Okoye ne ya bayyana haka a ranar Asabar a zantawarsa da AFP, inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar Alhamis.
Ya ce suna zargin "ƴan ƙungiyar IPOB ne suka tare babbar hanyar Owerri zuwa Okigwe suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi suka kashe mutum uku, suka jikkata wasu, sannan suka ƙone wasu motoci."
Sai dai ƙungiyar Amnesty International ta wallafa a shafinta na X cewa waɗanda aka kashe sun kai 30.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka da China na cigaba da tattaunawa kan yunƙurin samun maslaha a takun-saƙar kasuwanci da ke tsakanin ƙasashen biyu masu ƙarfin tattalin arziki.
Kafar watsa labarai ta China ta ruwaito cewa tattaunawa ta 'fara nisa' kuma za a samu daidaitu a kan ɓambace-bambacen da ke tsakaninsu.
Wakilan ƙasashen biyu sun gana na tsawon awanni a gidan ambasadan Swizerland a Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma ana sa ran tattaunawar za ta cigaba har zuwa ranar Lahadi.
Tun bayan da Shugaba Donald Trump ya ɗare kan karagar mulki ne ƙasashen biyu suka fara lafta wa juna haraje-harajen kayayyaki har sama da kashi 100, lamarin ya ja hankalin kasuwanci da cinikayya na duniya.

Asalin hoton, @GovernorInuwa
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta ce duk da cewa tana yabawa da ƙoƙarin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar, tana so a ƙara ƙaimi domin a cewarta an fara mayar da hannun agogo baya.
Ƙungiyar ta ce yadda Boko Haram ke ƙoƙarin dawo da ayyukanta a wasu sassan arewa maso gabas, da kashe-kashe a arewa ta tsakiya ne ya sa suke kira da a yi garambawul a ɓangaren tsaro, tare da yin kira da a ƙara samun haɗin kai tsakanin jami'an tsaron gwamnatin tarayya da na jihohi da ƴan sa-kai.
Shugaban ƙungiyar, Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a sanarwar bayan taron na ƙungiyar gwamnonin da sarakunan gargajiya da aka yi ranar Asabar a Kaduna.
"Ƙungiyar za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da ƙungiyar gwamnonin Najeriya domin samar da hanyoyin taimakon jami'an tsaron gwamnatin tarayya wajen magance matsalar da ƙasar ke fuskanta," in ji ƙungiyar, sannan ta ƙara da cewa za ta kafa kwamitin haɗin gwiwar domin samar da tsarin bao-ɗaya na tsaro domin sa ido kan tsaron iyakokin jihohi.
Haka kuma ƙungiyar ta saka nanata goyon bayan da kafa ƴansandan jiha, inda gwamnonin suka yi kira ga majalisar ƙasar da ta gaggauta ɗaukar matakin yin doka domin tabbatar da ƙirƙirar ƴansandan na jiha.

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kama ƴan jarida guda uku da suke aiki da wani gidan rediyo mai zaman kansa a ƙasar.
Dukkan ƴan jaridar guda uku suna aiki ne da gidan rediyon Sahara FM mai zaman kansa, kuma an tsare su ne a birnin Agadez.
An tsare su ne bayan sun yi rahoton da ke zargin cewa ƙasar ta kawo ƙarshen yarjejeniyar da ke tsakaninta da Rasha kan tsaro, kamar yadda shugaban rukunin kafafen watsa labarai na Air Info, Ibrahim Manzo Diallo ya shaida wa AFP.
Nijar dai tana fama da matsalar rashin tsaro musamman daga ƙungiyoyi masu alaƙa da Al-Qaeda duk da kasancewarta a ƙarƙashin mulkin soji, waɗanda suka ƙwace mulki a watan Yulin 2023.
Ƙungiyoyi masu zaman kansu sun yi zargin cewa cin zarafin fararen hula na ƙaruwa a ƙasar tun bayan da sojoji suka fara mulki.
Ya ce ƴanjaridar da aka kama su ne muƙaddashin babban edita Hamid Mahmoud da Mahaman Sani wanda ya gabatar da shirin sai mace guda ɗaya Massaouda Jaharou.
Diallo ya ce bayan an kai su kotu, alƙali ya sake su a ranar Alhamis, sai kuma ƴansanda suka sake kama su a ranar Asabar.

Asalin hoton, Isma'il Misilli
Gwamnonin arewa da kuma sarakunan gargajiya na gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin.
Taron wanda ke gudana a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, zai kuma tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al'amura da suke damun yankin.
Gwamnonin jihohin Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da kuma Zamfara na cikin waɗanda ke halartar taron.
A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.

Asalin hoton, Getty Images
Harin makami mai linzami da kuma ruwan alburusai da dakarun RSF suka kai wani sansanin ƴan gudun hijira kusa da birnin El Fasher, ya hallaka mutane da dama.
Jami'an agaji sun ce an kashe mutum 14 ƴan gida ɗaya waɗanda ke zaune a sansanin.
Daga bisani shaidu sun bayyana cewa dakarun na RSF sun far wa wani gidan yari a yankin El-Obeid da sojoji ke iko da shi, inda suka kashe aƙalla mutum 19 da jikkata gommai.
Fararen hula na ci gaba da shiga uƙuba tun soma yaƙi tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF - inda kowa ke neman iko.
RSF ta sha kai hari kan sansanin ABu Shouk, inda dubban mutanen da aka ɗaiɗaita ke rayuwa.
A baya-bayan nan ma, sun kashe ɗaruruwan mutane lokacin da suka kai hari sansanin, har ta sace komai a sansanin Zam Zam.
Suna koƙarin ganin sun hana mutane rayuwa ko kuma hana gudanar da jagoranci a yankunan da sojojin gwamnati ke iko da su.
Jami'an lafiya sun ce RSF sun tayar da wani gidan yari da dubban fursunoni ke ciki a birnin El-Obeid da ke kudancin ƙasar.

Asalin hoton, PA Media
Shugabannin wasu ƙasashen Turai da ke ziyara a Ukraine, sun buƙaci Rasha ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ko ta fuskanci sabo kuma gagarumin takunkumi kan ɓangaren banki da kuma makamashi.
Wannan na daga cikin sakon da shugabannin ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Poland suka aika wa Rasha lokacin da suke ganawa da shugaba Zelensky na Ukraine, a wani mataki na nuna goyon baya ga ƙasar.
Sun buƙaci tsagaita wuta na kwana 30 wanda zai fara aiki daga ranar Litinin.
"Wannan ƙoƙarin ƙasashen Turai ne," in ji Keir Starmer na Birtaniya. "Dukkanmu muna kira ga Putin ya amince da yarjejeniyar. Idan yana son ganin an samu zaman lafiya, to yanzu ne ya kamata ya nuna haka."
Sai dai har yanzu Rasha ta kafe cewa dole ne Turai ta dakatar da taimakon soji ga Ukraine, kafin ta amince da batun tsagaita wuta. Sai dai hakan abu ne mai wuya.

An zargi wani mutum da laifin kisa da kuma fashi, bayan mutuwar wani mai shekara 87 a arewacin Landan.
An kira jami'an ba da agajin gaggawa zuwa wani gida da ke titin Goodchild da misalin karfe shida na yamma ranar Talata, inda suka samu tsohon da munanan raunuka - sannan aka garzaya da shi zuwa asibiti.
An kama Peter Augustine mai shekara 58, daga lardin Hornsey ranar Alhamis.
An tsare shi bayan gurfana a gaban kotun majistre a Willesden - kuma zai sake bayyana a Old Bailey ranar 13 ga watan Mayu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Indiya da Pakistan sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta nan take.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce: "Bayan tattaunawa ta tsawon dare da Amurka ta shiga tsakani, ina farin cikin sanar da cewa Indiya da Pakistan sun amince da tsagaita wuta nan take.
"Ina yi wa duka ƙasashen murna saboda amfani da hankali wajen amincewa da tsagaita wuta," in ji Trump.

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kare matakin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka, inda ya ce ya yi haka ne domin ƙasar ta samu ci gaba.
Shugaban ya bayyana haka ne ranar Juma'a a fadarsa da ke Abuja, lokacin da yake karɓar bakuncin jakada na musamman daga ƙasar Qatar, Dakta Mohammed bin Abdulaziz Al-Khulaifi.
Tinubu ya ce tsare-tsare da ake ɗauka na inganta harkar haraji a Najeriya, ya sa mutane daga ƙasashen waje na samun saukin zuba-jari da kuma kasuwanci a ƙasar.
"Muna ƙoƙari don inganta tsarin harajin mu. Wajibi ne mu ɓullo da sabbin tsare-tsare idan muka duba abubuwan da suka faru a baya na wahalhalu da aka fuskanta.
"Na ɗauki matakai masu tsauri saboda mu samu ci gaba. Sannu a hankali kwalliya za ta biya kuɗin sabulu," in ji shugaban.
Ya ce za a inganta haɗin-kai tsakanin Najeriya da Qatar ne ta hanyar duba batun wadatar abinci da kuma ci gaban tattalin arziki.
"Ba za ka samu abokin hulɗa fiye da Najeriya ba. Na kasance ina bibiyar abubuwan da ke faruwa a duniya da kuma ƙoƙarinku. Ya kamata ku ƙara himma a Najeriya don yaƙi da talauci da kuma ayyuka jin-ƙai," kamar yadda Tinubu ya faɗa wa jakadan na ƙasar Qatar.

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayar da umarnin haramta sayar da man fetur a karamar hukumar Bama na jihar, ciki har da garin Banki.
Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne ayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke na daƙile ayyukan ƴan ta-da ƙayar baya.
"Na bayar da umarnin haramta sayar da da man fetur a garuruwan Bama da Banki da kuma wasu sassa na karamar hukumar Bama nan take," in ji gwamna Zulum.
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana saɓa umarnin zai fuskanci hukunci mai tsanani.
"Babu wanda doka za ta kyale, sannan babu shafaffe da mai - za mu hukunta kowaye.
Gwamnan ya bai wa hukumomin tsaro damar kama duk wani gidan mai ko kuma mutum da ya take wannan umarnin.
Ya ƙara nanata zimmar da gwamnatinsa ke yi na dawo da zaman lafiya ma ɗorewa a jihar, inda ya yi kira ga al'ummar jihar da su ba da haɗin-kai a yaƙi da ƴan ta-da ƙayar baya da ake ci gaba da yi.

Asalin hoton, Reuters
Shugabannin ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Poland za su kai wata ziyarar ba-zata zuwa Ukraine.
Ana ganin ziyarar a matsayin ta karfafa gwiwa da goyon baya ga shugaba Volodymyr Zelensky.
Sun yi kira ga Rasha ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 30, ba tare da wani sharaɗi ba.
![She]hbaz Sharif](https://ichef.bbci.co.uk/ace/ws/640/cpsprodpb/vivo/live/images/2025/5/10/be995d0c-68d0-4c17-9591-1cc9dcd91bd0.jpg.webp)
Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Pakistan, She]hbaz Sharif ya ce ƙasarsa ta mayar wa da India bikin da ta yi mata.
"Yau mun mayar wa da India bikin da ta yi mana domin ɗaukar fansar jinanen al'ummarmu da ba su ji ba su gani ba." In ji Shehbaz.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani hari da Pakistan ɗin ta kai yankin Rakesh Gupta wanda ake zargin an yi ne domin kai hari kan fararen hula.
Burtaniya ta ce tana bin tsamin dangatakar tsakanin ƙasashen biyu sau da ƙafa.
Zaman tankiya tsakanin ƙasashen biyu ne dai ya zafafa tun bayan wani hari a watan da ya gabata inda India ke zargin Pakistan da mara wa ƴan ta'adda baya da ke kai hare-hare cikin yankunanta - zargin da Pakistan da musanta.

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya soki ƴan siyasar da ke sauya sheƙa bayan sun gama cin moriyar jam'iyyar, abin da ya bayyana da babban kuskure a siyasance.
Sanata Kwankwaso wanda ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake karɓar wasu ƴan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa NNPP daga ƙaramar hukumar Takai, a gidansa da ke Miller road a birnin Kano.
A baya-bayan nan ne dai raɗe-raɗi suka yi ta yawo cewa Kwankwason zai koma jam'iyya mai mulki ta APC.
Rabi'u Kwankwaso ya ƙara jaddada irin juriya da haɗin kai da ke tafiyar Kwankwasiyya duk kuwa da cewa an ta ƙoƙarin ganin an kawar da hankalin mabiya.

Asalin hoton, NAHCON/X
Hukumar alhazan Najeriya ta ce ya zuwa ranar misalin ƙarfe 8:02 ta yi jigilar maniyyata 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki.
Hukumar ta bayyana a shafinta na X cewa jirgin MaxAir ya tashi daga birnin Bauchi zuwa Madina, inda ya kwashi maniyyata 384 da kuma jami'i guda ɗaya.
Wannan dai shi ne cikamakin jirgi na biyar da suka yi jigilar maniyyatan daga ranar da aka ƙaddamar da jigilar wato ranar Juma'a.
Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Asabar. Da fatan an wayi gari lafiya. Kamar kullum yau ma mun sake dawowa da shafinmu na kai tsaye mai kawo muku labarai da rahotanni dangane da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin. Mun gode