Rufewa
Jama'a a nan kuma za mu rufe wannan shafin na labaran kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/11/25
Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Ja'afar da Umar Mikail
Jama'a a nan kuma za mu rufe wannan shafin na labaran kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
Jamus ta bayyana shirin fadada bangaren tsaron sojojinta ya zuwa falaki.
Kasar za ta kashe fiye da dala biliyan 40 a wani abin da ta kira karfafa matakan tsaro domin tsare kasarta da ma tashoshin da ta mallaka a sararin falaki.
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya yi gargadin cewa akwai hadari idan aka kaiwa tauraron dan adam da ke cikin sararin falaki hari, domin hakan na iya tsayar da kome a kasar.
Abin da gwamnatin ta bayyana da wani matakin da ya zama wajibi ta dauka da matukar muhimmanci.
Wani sabon rahoton binciken kudi ya ce akwai alamun an karkatar da biliyoyin daloli da Tarayyar Turai ta kashe domin yaki da matsalar yunwa a Afirka.
Rahotannin sun nuna cewa an karkatar da kudaden ne zuwa wasu hanyoyi na daban ko kuma ba su yi wani tasirin a-zo-a-gani ba ta hanyar isa ga wadanda aka ware kudaden domin su.
Wata cibiya mai binciken yadda aka kashe kudaden ta ce tun farko ba a dauki matakan da sua dace ba ta yadda hakan ya kasa magance tushen matsalolin da ke haifar da yunwa a Afirka.
Tun a shekarar 2014 Kungiyar Tarayyar Turai ta kashe dalabiliyan goma sha uku domin yaki matsalar karancin abinci da kusan mutum miliyan 250 ke fuskanta a Afirka.
Ɗanwasan ƙungiyar PSG ta Faransa da tawagar ƙasar Moroccco Achraf Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗanƙwallon kafa na Afirka na 2025.
Mohamed Salah na Masar da ƙungiyar Liverpool ne ya zo na biyu, sannan Victor Osimhen na tawagar Super Eagles ta Najeriya da ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya ya zo na uku.
Hakimi ya samu nasarar lashe gasar cin kofin zakarun turai a ƙungiyar PSG ta kakar 2025, sannan ya lashe gasar Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup.
Wani sabon rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kusan duk mace daya a cikin uku ta taba fuskantar muzgunawa a gida ko cin zarafi ta hanyar lalata.
Shugaban hukumar ta WHO Tedros Ghebreyesus ya bayyana cin zarafin mata a matsayin dadadden abu, kuma wanda al'umma ke matukar kawar da kai gare shi.
A wata ƙididdiga da wakiliyar BBC ta ce kimanin mata miliyan dari takwas da arba'in sun fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata a rayuwarsu.
Hukumar Lafya ta Duniya ta tattara wadannan alkalumma daga kasashen duniya dari da sittin da takwas a tsakanin shekarar 2023.
A cewar rahoton matakin rage tallafin kudadde domi yaki da matsalar cin zarafin mata a duniya zai kara dagula lamarin ne kawai.
Jami'an kungiyar samar da tsaro ga fararen hula ta Hamas a Gaza sun ce hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza sun kashe akalla mutun sha daya.
Kakakin kungiyar ta Civil defense a Gaza ya shaidawa BBC cewa mutum biyar ciki har da mata da kananan yara ne suka mutu a yayin harin da Israilar ta kai a wurin ibada sai kuma karin wasu mutu uku da suka mutu.
An kai harin ne a wani filin wasa da Majalisar Dunkin Duniya ke tafiyarwa a birnin na Gaza.
Sojojin Isra'ila sun kai harin ne a wani wuri da ta kira maboyar 'yan ta'adda a Gaza bayan da mayakan Hamas suka bude musu wuta a yankin Khan Younis.
A jamhuriyar Nijar, rikicin shugabancin da ke rarraba kawuna a babbar kungiyar kwadago ta kasar ta CNT ya dauki sabon salo.
Yanzu dai kungiyar ta kori kungiyar malaman makaranta 'yan kwantragi ta Synaceb mai magoya baya sama da dubu 70 a cikinta, duk da cewa ita dai Synaceb din ta ce ba ta koru ba.
A wani bangare kuma ƙungiyoyin ƙwadago mambobin CNT sun sake ƙalubalantar shugabar ƙungiyar a gaban kotu…
Poland ta sanar da aniyarta ta rufe ofishin jakandancin Rasha na ƙarshe da ke kasarta.
Ministan harkokin wajen Poland Radoslaw Sikorski, ya ce za su rufe ofishin jakandanci da ke birnin Dansk a matsayin martani ga wani harin jirgin kasa da aka kai a kudancin birnin Warsaw a farkon makon nan.
A cewar Sikorski, wannan karon harin ya wuce na karkatar da hankali kamar yadda aka saba yi a baya, face aikin ta'addanci ne ƙarara da aka so ya yi muni.
Kuma wannan shi ne irin martanin da zasu mayarwa Rasha a 'yan makonni nan.
Gwamnatin Poland na zargin wasu 'yan asalin Ukraine biyu ne da ke yi wa Rasha leken asiri suka kai harin.
Hukumomi a jihar Kebbi sun musanta kalaman da wani ɗan majalisar Amurka ya yi cewa akwai yiwuwar ɗaliban da aka sace a jihar mabiya addinin Kirista ne.
Shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, inda lamarin ya faru, Hon Hussaini Bena, ya tabbatar da cewa dukkanin ƴan matan da aka sace, da mai gadin makarantar da aka harbe duk Musulmai ne.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, ɗan majalisar Amurkar Riley Moore ya buƙaci magoya bayansa su taya shi yi wa ƴan matan da aka sace da mutumin da aka kashe addu'a.
A cewarsa '' duk da ba mu da cikakken bayani game da lamarin, amma mun san an kai harin ne a wani yanki da ke da kiristoci da yawa a Arewacin Najeriya, wajibi ne gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen wannan zaluncin''.
A ranar Litinin da asuba ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka shiga wata makarantar kwana da ke garin Maga a jihar Kebbi, inda suka sace ɗalibai 25, amma biyu daga cikin suka samu nasarar kuɓuta.
Hukumomi a Ukraine sun ce aƙalla mutum 25 ne suka mutu, ciki har da ƙananan yara uku bayan hare-haren da Rasha ta kai wasu sabbin hare hare cikin dare kan gidajen jama'a a birnin Ternopil da ke yammaci.
Shugaban yankin Kharkiv ya ce hare-haren da jirage marasa matuƙa suka kai sun jikkata mutum fiye da 73 a harin wanda yake cikin wadanda suka fi muni.
Rahotannin sun bayyana harin ya kuma shafi tashoshin samar da wutar lantarki waɗanda su ne harin ya fi mayar da hankali kai musamman a yammacin Ukraine.
Shugaba Zelensky ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar har yanzu akwai mutanen da suka maƙale a cikin ɓaraguzai.
Ya ce Moscow ta kai harin ne da ɗaruruwan jirage marasa matuƙa, da aƙalla makamai masu linzami hamsin.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗage tafiyar da ya shirya yi a yau zuwa Afirka ta kudu da kuma Angola, a yayin da ya ke jiran sauraron rahoto game da sace ɗalibai da aka yi a Kebbi da harin da aka kai kan wani coci a Kwara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yauwansa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaban ya umurci a aika ƙarin jam'ian tsaro karamar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara inda lamarin ya faru kamar yadda gwamnan jihar ya buƙata, tare kuma da bai wa ƴansanda umurnin farauto ƴan bindigar da suka kai hari kan masu ibadar.
A yau Laraba ne shugaban ya tsara barin ƙasar domin halartar taron shugabannin ƙasashe ashirin masu ƙarfin tattalin arziƙi (G20) karo na ashirin da za a yi a Afirka ta Kudu, daga nan kuma zai ƙarasa Luanda da ke Angola domin halartar karo na bakwai na taron ƙungiyar Tarayyar Afirka da ta Tarayyar Turai.
Sanarwar ta kuma ce a yanzu Tinubu na zaman sauraron rahoto daga mataimakinsa Kashim Shettima, wanda ya kai ziyarar jaje zuwa Kebbi a madadinsa, da kuma rahotanni daga ƴan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya DSS kan harin coci a Kwara.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce yana takaicin sace ƴan matan da aka yi a Kebbi, da kuma alhinin mutuwar Birgadiya Janar Musa Uba da gwarazan sojojin da suka mutu a jihar Borno.
A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce ya shiga matuƙar damuwa kan mutuwar sojojin ƙasar da ke bakin aiki.
Ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da kuma saƙon jaje da iyayen ɗaliban da aka sace, inda ya ce yana ci gaba da yi musu addua.
'' Ina cikin damuwa sosai kan yadda ƴan bindiga suka katse wa ƴan matan nan karatunsu, na umurci jam'ian tsaro su yi gaggawar dawo da ƴan matan gida'' '' Ina sane da ƙaruwar rashin tsaro a wasu sassan ƙasar, kuma na bai wa jami'an tsaro umurnin daƙile matsalolin cikin gaggawa''. a cewar shugaban.
Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar da su taimaka wa jam'ian tsaro wajen basu haɗin kai da kuma bayanai masu muhimmanci, inda ya sha alwashin hukunta masu yi wa tsaron ƙasar barazana.
Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce ƙaruwar hare-hare da ake samu na baya-bayan nan a ƙasar ya kai matakin da ke buƙatar matakin gaggawa daga hukumomi, musamman daga gwamnatin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce wajibi ne gwamnatin Najeriya ta sauke babban nauyin da ke kanta na kare rayukan al'umma, ta hanyar ƙarfafa wa jam'ian tsaron ƙasar gwiwa.
''Da farko, sace ɗalibai ƴanmata 25 a Kebbi abin damuwa ne da ke sanya fargabar ko za a maimaita abin da ya faru a baya, sai sacewa da kuma kashe Birgadiya janar M Uba da ƴan ta'adda suka yi a Borno, wanda yana daga cikin lokuta mafi muni a yaƙin da ƙasar ke yi da ta'addanci,'' in ji shi.
Ya kuma nuna damuwa game da sace gwamman mutane a Zamfara, da kuma ƙaruwar harin da ƴan bindiga ke kai wa a ƙananan hukumomin Shanono da Ghari a jihar Kano.
''Ina kira a yi gaggawar ceto waɗanda aka sace, domin hare-haren baya-bayan nan na nuna koma baya a yaƙin da ake yi da matsalar tsaro,'' a cewar sa.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International ta zargi hukumomi a Kenya da amfani da fasaha wajen daƙile matasa masu zanga-zanga.
A wani sabon rahoton da ta fitar, ƙungiyar ta ce wasu hukumomin gwamnati sun shafe shekara guda suna kitsa yadda za su bibiyi matasan, su ci zarafin su a intanet, su kuma sauya duk wani zancen da matasan ke tattaunawa kai a shafukan sada zumunta.
Rahoton ya ruwaito shaidun da wasu mutane suka bayar waɗanda ke cikin shirin, inda suka ce an biyasu ɗaruruwan daloli su rinka karkatar da zancen da ake yi a shafukan sada zumunta da kuma cin zarafin masu sukar gwamnati.
Ministan harkokin cikin gida na Kenya ya musanta zargin.
Masu zanga-zangar, waɗanda akasari matasa ne, sun fito nuna adawa ne da karin harajin da gwamnati ta yi, sai dai sun gamu da mumumman martani daga gwamnatin.
China ta haramta shigar da kifi da sauran halittun ruwa ƙasarta daga Japan, a yayin da dangantaka tsakanin ƙasahen biyu mafiya girman tattalin arziƙi a yankin Asiya ke ƙara yin tsami.
A baya bayan nan ne China ta ci gaba da sayan kifin da sauran dangoginsa daga Japan ɗin bayan wani haramncin da aka sanya kan shigar da su a 2023.
Sake dawo da haramcin shi ne mataki na baya bayan nan da China ta ɗauka bayan kalaman da Firaministar Japan Sanae Takaichi ta yi kan cewa ƙasar ta za ta mayar da martani idan har China ta kai wa Taiwan hari.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kare Yarima mai jiran gado na Saudiyya kan kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi da jami'an Saudiyya suka yi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar da ke birnin santanbul shekara bakwai da suka gabata.
Mista Trump ya dage kan cewa Mohammed Bin Salman bai san komai game da kisan ba, ikirarin da ya saɓawa binciken hukumomin leƙen asirin Amurka.
Mohammed Bin Salman wanda ke ziyararsa ta farko a Washington tun bayan kisan,ya yi alkawarin zuba jarin dala tiriliyan daya a Amurka.
Rasha ta kai sabbin hare hare cikin dare kan birane da cibiyoyin samar da makamashi na Ukraine.
Shugaban yankin Kharkiv ya ce zafafen hare haren da jirage marasa matuƙa sun jikkata mutum fiye da talatin, ciki har da ƙananan yara.
An kuma kai harin kan yankunan Lviv da Ternopil da ke yammacin kasar.
Magajin garin Ternopil ya ce lamarin ya rutsa da mutane da dama, saboda harin ya shafi gidajen alumma.
Ministan makamashi na Ukraine ya ce an samu katsewar lantarki a wasu yankuna da dama.
A gefe guda kuma Shugaban Ukarine ɗin Volodymyr Zelensky ya isa Turkiyya domin tattaunawa da takwaransa na can Recep Tayyip Erdogan.
Ƴan sanda a jihar Kwara da ke kudu maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa an kai hari kan wani coci a birnin Eruku a yammacin Talata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da sace da dama.
Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ruwaito cewa wasu mutane ɗauke da makamai, sun shiga cocin Christ Apostolic da ke Oke Isegun a ƙaramar hukumar Ekiti a lokacin da ake ibadar yamma, suka harbe limamin cocin kuma suka tasa ƙeyar masu ibada da dama.
Ƴan sanda sun kuma ce sun gano gawar mutum na biyu a cikin wani daji, hakazalika wani jami'in sa kai ya jikkata sakamakon harbin bindiga, kuma tuni aka garzaya da shi asibiti.
Hukumomi a jihar sun ce ƴan sanda da ƴan sa kai sun bazama farautar maharan waɗanda suka tsere cikin dazukan da ke kusa.
Wani bidiyo da ake kyautata zaton na kyamarar CCTV ne na cocin da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna masu ibadar a tsorace suna neman mafaka, ciki har da tsofaffi da ke ta ƙoƙarin tserewa.A shekarun baya bayan nan, an samu rahotannin irin waɗannan hare haren da ƴan bindiga ke kai wa a jihar, musamman yankunan da ke kusa da iyakokin jihohin Neja da Kogi.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai farmaki kan mayakan Hamas da ta ce suna gudanar da atisaye a wani sansanin 'yan gudun hijirar Falasdinawa da ke Lebanon.
Ma'aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon ta ce akalla mutane goma sha uku ne suka mutu sa'annan wasu da dama suka jikkata.
Wakilin BBC ya ce bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna motocin ɗaukar marasa lafiya suna tafiya a guje kan titunan sansanin da ke cike da cunkoson jama'a yayin da hayaƙi ya turnuƙe wurin da aka kai harin.
Rundunar sojin Isra'ilar ta ce, 'yan kungiyar Hamas na amfani da sansanin ne wajen samun horo domin shiryawa hare-haren da za su kai kai mata, duk da dai bata gabatar da wata shaidar da ke tabbatar da hakan ba.
Masu bibiyar shafin BBC Hausa na kai-tsaye, barkanmu da Hantsin Laraba.
A yau kamar kullum za mu kawo muku labaran irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Za kuma ku iya bibiyar mu a shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook da Instagram da Youtube da kuma X, domin tafka muhawara a kan labaran da muke wallafawa da kuma kallon bidiyo.