Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na yau, inda muka kawo muku labaran abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya.
Muna fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya. Sai kuma Allah ya nuna mana gobe Lahadi.
Isra'ila ta kashe mutum 8 a kusa da cibiyar rabon abincin agaji - Masu aikin ceto
Masu aikin ceto a Gaza sun ce sojojin Isra'ila sun sake kashe mutum takwas - da ke zaman jiran abincin taimako a kusa da wajen da wuraren da ake rabon.
Yawancinsu an ce an harbe su ne a tsakiyar Gaza, yayin da sauran aka kashe su a kusa da Khan Younis da ke kudanci.
A nata ɓangaren, hukumomin sojin Isra'ila sun ce suna bincike kan hare-haren biyu.
Hamas ta ce mutanen su ne na baya-bayan nan cikin Falasɗinawa sama da 400, da Isra'ila ta kashe a lokacin da suke neman taimakon abinci, daga cibiyoyin da ƙungiyar agaji ta Gaza - Gaza Humanitarian Foundation, ke gudanarwa.
Waɗanda aka kashe a Iran sun haura 400 - Ma'aikatar lafiya
Asalin hoton, Getty Images
Sama da mutum 400 ne hare-haren Isra'ila suka kashe a Iran tun bayan ɓarkewar yaƙin a ranar 13 ga Yuni, kamar yadda kakakin ma'aikatar lafiya ta Iran ya bayyana.
Hossein Kermanpour, ya rubuta a shafinsa na X cewa mutum 3,056 ne suka jikkata.
Ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kashe ɗin, akwai mata 54, da ma'aikatan jinya 5, sannan ya ce mafi yawan waɗanda aka kashe ɗin, "fararen hula ne."
Wannan ne karo na farko da aka fitar da ƙididdigar waɗanda aka kashe a hukumance tun daga ranar 15 ga Yuni lokacin da hukumomi suka sanar da cewa an kashe mutum 224, an jikkata 1,200.
Tun da farko, kamfanin dillancin labarai na Nour ya sanar da cewa aƙalla mutum 430 aka kashe, sannan aka jikkata 3,500 a Iran.
An sako mijin jagorar ƴan hamayya na Belarus daga gidan yari
Asalin hoton, EPA
Jagorar ƴan hamayya ta Belarus da ke gudun hijira, Svetlana Tikhanovskaya, ta haɗu da mijinta, bayan da kwatsam, ba zato ba tsammani aka sake shi daga gidan kaso.
Maigidan nata - Sergei Tikhanovsky, na daga cikin tsararru goma da aka saki yayin ziyarar da wakili na musamman na Amurka, Keith Kellogg, ya kai Minsk. Daga cikin waɗanda aka sakin akwai ƴan ƙasashen Japan da Poland da kuma Sweden.
Mr Tikhanovsky na daga cikin jagororin zanga-zangar tabbatar da dimukuraɗiyya da aka yi a Belarus a shekarar 2020.
Matarsa ta maye gurbinsa a matsayin ɗantakarar shugaban ƙasa bayan da aka kama shi. Har yanzu ana ganin akwai fursunonin siyasa wajen 1000 da ke garƙame a gidan yari a ƙasar. A yanzu dai Mr Tikhanovsky, yana Lithuania.
Gwamnatin Kano ta ɗauki alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center
Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa
Gwamnatin jihar Kano ta yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar, ya ce bayan ziyarar gani da ido da gwamnan ya yi a ranar Juma'a, ya ɗauki matakin sake gina kasuwar tare da sabunta ta da zamanantar da ita, aikin da da ya ce "gwamnan zai kashe naira biliyan 2."
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya ce, "Wannan yunƙuri ba kawai saboda gobarar ba ce, za mu yi amfani da wannan damar ne domin inganta tattalin arzikin jihar, da samar da ayyukan yi," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta saya ƙarin fili domin faɗaɗa kasuwar, inda za ta samu damar gina abubuwan da ake buƙata a kasuwa na zamani, ciki har da gina sashen masu kashe gobara domin jiran kar-ta-kwana.
"Ba kasuwa kawai za mu gina ba, cibiyar kasuwanci za mu gina domin jawo ƴankasuwa daga ƙasashen duniya," in ji shi.
Iran ba za ta taɓa mallakar makaman nukiliya ba, in ji Macron
Asalin hoton, EPA
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce ya samu kiran waya daga takwaransa na Iran Masoud Pezeshkian.
Macron ya ce ya amince ya shiga tattaunawa tsakanin shugabannin Turai da kuma Iran kan shirinta na nukiliya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban na Faransa ya ƙara da cewa: "Ina buƙata: Iran ba za ta taɓa mallakar makaman nukiliya ba, kuma ya rage gare ta don bayar da tabbacin cewa manufofinta na zaman lafiya ne."
Ya karkare da cewa ya amince "akwai hanyar kawo karshen wannan yaƙi da kuma kauce wa faɗawa babban hatsari".
Domin cimma haka, ya ce "Za mu tabbatar an yi tattaunawa cikin sauri da Iran wanda Faransa za ta jagoranta da takwarorinta na Turai.
Iyalan tsohon shugaban Zambia sun sanar da shirinsu na jana'izar shi a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, Photothek via Getty Images
Iyalan
marigayi tsohon shugaban Zambiya sun sanar da shirinsu na yin jana'izar shi a
Afirka ta Kudu, inda Edgar Lungu ya rasu a farkon wannan watan.
Akwai
ɓaraka tsakanin Iyalin nasa da
gwamnatin Zambiya ta yanzu game da tsare-tsaren da aka tanada na jana'izarsa a ƙasarsa.
An
tsara cewa abokin hamayyar Mista Lungu kuma shugaban ƙasar
Zambiya a yanzu, Hakainde Hichilema ne zai tarbi gawar marigayin sannan kuma ya
jagoranci yi masa jana'iza sai dai iyalin Mista Lungu sun yi watsi da hakan.
Ƴansanda na binciken musabbabin "fashewar da ta kashe mutum biyar" a Kano
Asalin hoton, Getty Images
Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya fashe a jihar Kano, wanda ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum, sannan wasu mutum 15 suka jikkata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a ranar Asabar, wanda ya jefa tsoro da fargaba a yankin da ya faru.
Kwamishinan ƴansandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya ziyarci wajen jim kaɗan bayan fashewar, ya ce abin suna tunanin fashewar daga wata mota ce da ta taso daga jihar Yobe.
"Da aka kira sai na tafi wajen cikin gaggawa, da na isa sai na fahimci cewa wani abu ne - wataƙila bom ne - ya fashe. Aƙalla mutum 5 sun rasu, sannan 15 suka jikkata," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "mun fara bincike asalin musabbabin aukuwar lamarin, amma muna tunanin motar da ta ɗauko abin fashewar daga jihar Yobe take.
"Binciken farko-farko ya nuna cewa wata motar tirela ce ta kwaso wasu abubuwa masu fashewa. Amma zuwa yanzu ba mu da tabbacin ko kayan sojoji ne, ko na kuma ta ƴan kwangila," in ji shi.
"Amma za mu fayyace komai da zarar mun kammala bincike."
Aƙalla ƴan ɗaurin aure 12 ne aka kashe a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu, sannan kuma an jikkata wasu mutum 11 a lamarin wanda aka yi a ranar Juma'a.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan ɗaurin su 31 da suka taso daga garin Basawa da ke ƙaramar hukumar Zaria a jihar Kaduna, ne ciki har da mata a ƙananan yara kuma suna tafiya ne a motar bas mallakin Jami'ar ABU Zaria, kuma faɗa hannun maharan ne da misalin ƙarfe 8 na dare a hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar Qua'an Pan da ke jihar Filato.
Babban limamin masallacin Juma'a na JIBWIS, Sheikh Suleiman Haruna ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce sun ajiye gawarwakin a babban asibitin Mangu.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Ibrahim Umar ya ce, "mun je auren ɗan'uwanmu ne, sai muka ɓace hanya. Da muka tsaya domin mu yi tambaya, kawai sai suka mana ƙawanya suka fara cewa a kashe mu. Nan suka fara kashe direban, sannan suka kashe wasu, sannan suka ƙona motar. Allah ne ya tseratar da mu."
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Filato, DSP Alfred Altau ya ce ƴansanda sun samu labarin aukuwar lamarin, kuma za su fitar da sanarwa nan gaba.
Aƙalla mutum takwas sun mutu a hatsarin babban balan-balan a Brazil
Asalin hoton, Eddie White
Aƙalla mutum takwas ne suka mutu a wani hatsarin babban balan-balan a Brazil, a cewar gwamnan jihar Santa Catarina, Jorginho Mello.
Mutum 21 ne ke cikin babban balan-balan ɗin lokacin da ya yi hatsari a birnin Praia Grande a safiyar yau Asabar, kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafin X.
Mello ya ce mutum 13 sun tsira, yayin da takwas suka mutu.
Ya ce jami'an agaji na can suna bincike a wajen da lamarin ya faru don neman sauran.
"Mun kaɗu matuka da lamarin.
"Jami'an mu na ci gaba da bayar da kulawa ga dukkan iyalan waɗanda lamarin ya shafa," in ji gwamnan.
Ya ce za su ci gaba da sa ido a lamarin.
Za ku iya samun ƙarin labarai a tasharmu ta WhatAspp
Me ya sa Kannywood suka rage sanya waƙoƙi a fina-finan Hausa?
Asalin hoton, Rahama Sadau TV
Daina ganin waƙoƙi da raye-raye a finafinan Hausa sun fara jan hankali masu kallo, inda wasu suke fargabar ko dai an daina saka waƙoƙin ne, lamarin da masana suke ganin ci gaba ne mai kyau ga masana'antar.
Tun farkon finafinan Kannywood, masana'antar ta yi fice wajen amfani da waƙa a matsayin wani muhimmin jigo na labari.
Ana dai amfani da waƙoƙin ne ko don nuna soyayya, ko nuna baƙin ciki, ko kuma don ƙarfafa wani saƙo, wanda bai rasa nasaba da kamanceceniyar da finafinan Hausa ke da shi da finafinan Indiya.
Sai dai a wani sabon yanayi, yawancin sabbin finafinai ko dai babu waƙa, ko kuma an yi amfani da waƙar ne kawai domin sharar fage.
Yaƙin Isra'ila da Iran: Hotunan ɓarnar da ɓangarorin biyu suka yi
Kamar yadda muka ruwaito, sojojin Isra'ila sun ce sun kaddamar da ƙarin hare-hare kan "wuraren soji" a kudu maso yammacin Iran.
Wannan ne kuma rana ta tara da ɓangarorin biyu ke faɗa da juna, tun bayan kaddamar da hari ran 13 ga Yuni da Isra'ila ta yi.
Kamfanin dillancin labarai na Nour, ya ruwaito ma'aikatar lafiya a Iran na cewa aƙalla mutum 430 aka kashe sannan an jikkata 3,500 tun soma rikicin.
Isra'ila ta ce an kashe mata mutum 25, inda aka kuma jikkata 2,517.
Ga wasu hotuna na irin ɓarnar da ɓangarorin biyu suka samu.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Masu aikin ceto a Isra'ila na duba wani gini wanda ya koma ɓaraguzai bayan harin Iran a birnin Beit She'an
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Wani ɗan Iran lokacin da ake yi masa jinya a asibitin Imam Khomeini bayan harin Israila a birnin Tehran
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila da masu aikin ceto na aikin duba wuraren da suka lalace lokacin da Iran ta kai harin sama a Beit She'an
An ji ƙarar fashewar abu a kudancin Iran
Isra'ila ta kaddamar da ƙarin hare-hare kan "wuraren soji" a kudu maso yammacin Iran, a cewar mai magana da yawun dakarun ƙasar.
Avichay Adraee ya wallafa a shafin X cewa: "jiragen yaƙi na ci gaba da kaddamar da hare-hare kan wuraren soji a kudu maso yammacin Iran." Bai yi wani ƙarin bayani ba kan haka.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an ji ƙarar fashewar abubuwa a Ahvaz da kuma Bandar-e Mahshahr, a lardin Khuzestan da ke kudu maso yammacin Iran.
Gane Mini Hanya: Tare da Manjo Hamza Al-Mustapha
Tsohon babban dogarin Marigayi Sani Abacha ya bayyana damuwa a kan lalacewar al'amura a Nijeriya ƙarƙashin mulkin dimokraɗiyya musamman idan an kwatanta da zamanin mulkin soji.
Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya ce tarihi da abubuwan da ya shaida a zamanin sojoji har komawa ga tsarin dimokraɗiyya, na alaƙanta rikicewar al'amura da ƙazancewar tsaro kan raunin shugabanci da rashin iya alkinta arziƙin man fetur.
Ya yi zargin cewa ana amfani da wasu tsirarun mutane domin a rusa Najeriya, yayin da 'yan ƙasar ke kukan cewa jiya ta fi yau.
Yayin zantawa da abokiyar aikin mu Ummaimah Sani Abdulmumin, a filinmu na Gane Mini Hanya, Manjo Almustapha ya soma ne da tsokaci kan dimokraɗiyya yanzu haka a Nijeriyar.
'Mutumin da ya so zuwa wurin Tinubu lokacin taro a Kaduna na da lalurar kwakwalwa'
Asalin hoton, Kaduna Police Command
Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta yi ƙarin haske kan wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zaumunta wanda ya nuna wani matashi ya tinƙari wajen da shugaba Tinubu yake lokacin da ya kai ziyara jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, DSP Mansir Hassan ya fitar, ta ce matashin mai suna Umar Mohammed wanda ke zaune a anguwar Muazu, yana da lalurar ƙwaƙwalwa.
"Binciken mu ya gano cewa matashin masoyin shugaba Tinubu ne da kuma gwamna Uba Sani. Saɓanin abin da ya faru - an tantance shi kafin shiga cikin fiin taron a Murtala Square, yana sanye da karamar riga ɗauke da hoton Tinubu da Uba Sani.
"Yana tsaye cikin wajen da aka keɓe wa magoya bayan jam'iyyar APC, sai kwatsam ya shata shingen tsaro sannan ya yi ƙoƙarin kutsawa zuwa wajen da Tinubu yake saboda yana cike da murnar ganinsa," in ji sanarwar ƴansandan.
Sai dai nan take jami'an tsaro suka kama matashin, inda bincike ya gano cewa ba shi da wata manufa illa farin cikin ganin shugaban ƙasa da kuma gwamna Sani.
Sanarwar ƴansandan ta ce an gudanar bincike sosai a kansa, kuma babu wani makami da aka samu a jikinsa.
Don haka kwamishinan ƴansandan jihar, CP Rabiu Muhammad ya gargaɗi al'umma da kuma masu yaɗa labarai marasa tushe da su guji yaɗa karya ko kuma siyasantar da al'amuran tsaro don cimma manufarsu ta siyasa.
Ƴansandan sun kuma ce an jirkita bidiyon matashin da nufin sauya masa ma'ana.
"Muna ci gaba da bincike kan lamarin kuma za mu gayyaci duk waɗanda ke yaɗa labaran karya don yi musu tambayoyi da kuma hukunta su idan muka same su da laifi," in ji sanarwar.
Isra'ila ce babban cikas ga zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya - Erdogan
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce hare-haren da Isra'ila ke kai wa Iran kafin yin sabuwar tattaunawa da Amurka kan shirin nukiliyar ƙasar "zagon ƙasa" ne ga tattaunawa.
Da yake jawabi a wani taron diflomasiyya a birnin Istanbul, wanda ministan harkokin wajen Iran yake halarta, Erdogan ya yi Alla-wadai da hare-haren Isra'ila, inda ya zargi ƙasar da ƙoƙarin wargaza Gabas Ta Tsakiya.
Gwamnatin Netanyahu na nuna wa ƙarara "ita ce babban cikas ga zaman lafiya a yankin", in ji shugaban na Turkiyya.
Ya ƙara da cewa: "gwamnatin Netanyahu na zagon ƙasa ga shirin tattaunawa ta hanyar fara kai hari ranar 13 ga Yuni."
Babu barazana ga Tinubu a zaɓen 2027 - gwamna Uba Sani
Asalin hoton, Uba Sani/FB
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce shirin kafa jam'iyyar haɗaka da ake son yi, ba barazana ba ce ga shugaba Bola Tinubu.
Ya ce hakan bai nuna cewa akwai wata barazana da za ta tinkari jam'iyyar APC ba.
"Zan faɗa muku, sannan ku je ku rubuta. Babu wata barazana da Tinubu ke fuskanta," kamar yadda gwamnan ya bayya a shirin siyasa na Politicis Today na gidan talabijin na Channnels ranar Juma'a.
Gwamnan yana mayar da martani ne kan kafa wata ƙungiya mai suna National Opposition Coalition Group, wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark ke jagoranta.
Ya ƙara da cewa yawancin waɗanda ke goyon bayan haɗakar ba su san irin ƙoƙari da masu fafutuka suka yi ba wajen ganin tabbatuwar dimokraɗiyya da kuma shugabanci na gari a Najeriya.
"Mutanen da ke magana a yau, ina suke lokacin da ake fafutikar samun dimokraɗiyya, adalci, shugabanci na gari da kuma doka? Ba su san komai game da hakan ba.
Gwamnan ya kuma ce ba ya fargabar ƴan adawa a jihar ta Kaduna saboda irin yadda gwamnatinsa ke yin ƙoƙari.
Jiragen Iran marasa matuki takwas sun shiga Isra'ila - IDF
Sojojin Isra'ila sun ce jirage marasa matuki guda takwas daga Iran sun ratsa cikin sararin samaniyar ƙasar cikin sa'a ɗaya a safiyar yau.
Dakarun ƙasar sun ce sun gano jiragen sun shiga ƙasar ne tsakanin karfe 10:16 zuwa 11:27 agogon ƙasar - sun fito ne daga yankin Eliat a kudanci zuwa arewacin ƙasar da ke iyaka da Syria.
A cewar dakarun, an kakkaɓo biyar daga cikinsu, yayin da ake ci gaba da sa ido kan sauran.
Me ya sa Syria ta bari ana amfani da sararin samaniyarta wajen kai wa Iran hari?
Asalin hoton, Getty Images
Kafofin yaɗa labarai na Syria da ma wasu na yankin Gabas ta Tsakiya sun koka kan yadda sabuwar gwamnatin Syria ta yi gum da bakinta tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran.
Haka nan wasu na mamakin yadda jiragen saman Isra'ila ke ratsawa ta sararin samaniyar Syriya domin kai hare-hare a cikin Iran.
Amfani da sararin samaniyar Syria da jiragen Isra'ila ke yi da kuma amfani da sararin na Syria da Iran ke yi tana harba makamai zuwa Isra'ila ya haifar da asarar rayuka daga dukkanin ɓangarorin biyu, kuma duk da haka gwamnatin ta Syria ba ta ce uffan ba.
Jaridu da dama a yankin sun yi sharhi kan lamarin, yayin da wasu masana ke cewa rashin tsoma bakin Syriya na nufin mataki ne na tsayawa a tsakiya, wasu kuma na ganin ƙasar na kallon dukkanin ƙasashen biyu ne a matsayin maƙiyanta.