Gane Mini Hanya: Tare da Manjo Hamza Al-Mustapha

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Tare da Manjo Hamza Al-Mustapha

Tsohon babban dogarin Marigayi Sani Abacha ya bayyana damuwa a kan lalacewar al'amura a Nijeriya ƙarƙashin mulkin dimokraɗiyya musamman idan an kwatanta da zamanin mulkin soji.

Manjo Hamza Almustapha mai ritaya ya ce tarihi da abubuwan da ya shaida a zamanin sojoji har komawa ga tsarin dimokraɗiyya, na alaƙanta rikicewar al'amura da ƙazancewar tsaro kan raunin shugabanci da rashin iya alkinta arziƙin man fetur.

Ya yi zargin cewa ana amfani da wasu tsirarun mutane domin a rusa Najeriya, yayin da 'yan ƙasar ke kukan cewa jiya ta fi yau.

Yayin zantawa da abokiyar aikin mu Ummaimah Sani Abdulmumin, a filinmu na Gane Mini Hanya, Manjo Almustapha ya soma ne da tsokaci kan dimokraɗiyya yanzu haka a Nijeriyar.