Me ya sa Syria ta bari ana amfani da sararin samaniyarta wajen kai wa Iran hari?

Asalin hoton, SYRIA TV
Kafofin yaɗa labarai na Syria da ma wasu na yankin Gabas ta Tsakiya sun koka kan yadda sabuwar gwamnatin Syria ta yi gum da bakinta tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran.
Haka nan wasu na mamakin yadda jiragen saman Isra'ila ke ratsawa ta sararin samaniyar Syriya domin kai hare-hare a cikin Iran.
Amfani da sararin samaniyar Syria da jiragen Isra'ila ke yi da kuma amfani da sararin na Syria da Iran ke yi tana harba makamai zuwa Isra'ila ya haifar da asarar rayuka daga dukkanin ɓangarorin biyu, kuma duk da haka gwamnatin ta Syria ba ta ce uffan ba.
Jaridu da dama a yankin sun yi sharhi kan lamarin, yayin da wasu masana ke cewa rashin tsoma bakin Syriya na nufin mataki ne na tsayawa a tsakiya, wasu kuma na ganin ƙasar na kallon dukkanin ƙasashen biyu ne a matsayin maƙiyanta.
Wani babban jami'in gwamnatin Syriya ya yi watsi da zargin cewa Syriyar na barin Isra'ila na amfani da sararin samaniyarta wajen samun bayani kan makaman da Iran ke harbawa.
Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da ɓarna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba.
Shafin Intanet na kafar Enab na ƙasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin Syriya ta yi kan karakainar da jiragen yaƙi da makamai masu linzami ke yi a sararin samaniyar ƙasar.
Wani mai sharhi ya faɗa wa Enab cewa gwamnatin Syriya ta yanke shawarar tsayawa tsakiya kan lamarin ne kasancewar tana ɗaukar Isra'ila da Iran a matsayin abokan gabarta.
Ya ce: "Babu ɗaya daga cikinsu da za ka bayyana shi a matsayin abokin al'ummar Syriya, kuma dukkaninsu sun taka rawa wajen lalata ƙasar Syriya."
Iran na daga cikin manyan ƙasashen da suka taimaka wa tsohon shugaban Syriya Bashar al-Assad, ita kuma Isra'ila ta ƙaddamar da ɗaruruwan hare-hare ta sama kan Syriya, kuma ta jibge sojojinta a yankunan tudun mun tsira tun cikin watan Disamba bayan tuntsurar da gwamnatin Assad.
Ya ce gwamnatin Syria a yanzu ta shagalta ne da ƙoƙarin daidaita lamurra a cikin gida da kuma ƙarfafa daƙon dangantakarta da Turkiyya da kuma ƙasashen yankin Gulf.
Jaridar da ke kare muradun yankin Larabawa ta 'Middle East Eye' ta ruwaito cewa shugaban Turkiyya Receb Tayyib Erdogan ne ya shawarci sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa cewa kada ya tsoma kansa cikin rikicin.

Asalin hoton, Getty Images
Saɓa ƙa'idar sararin samaniya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kafar yaɗa labarai ta Syria ta buga rahotanni da dama tana cewa Isra'ila da Iran na karya ƙa'idojin amfani da sararin samaniyarta, inda ta ce jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami da dama sun faɗa cikin ƙasar.
Kafar yaɗa labarai ta Syria - SANA - ta ruwaito cewa wani jirgi maras matuki ya fada kan wani gida a birnin Tartus, kuma daga baya an tabbatar da cewa matar ta rasu sanadiyyar raunukan da ta samu.
Haka nan kafar yaɗa labaran ta SANA ta ruwaito cewa wasu jirage marasa matuƙa sun faɗa kan gidajen al'umma a birnin Daraa kuma wani makamai mai linzami ya fada gefen Damascus, babban birnin ƙasar, inda makamin ya bar wani ƙaton rami.
Sai dai shirun da gwamnatin Syria ta yi kan wannan lamari ya ja hankalin kafafen yaɗa labarai a cikin ƙasar da kuma ƙasashen Larabawa. Yawancin jaridun sun ja hankalin al'ummar kasar cewa kada su kusanci wauraren da makaman ke faɗawa.
Sai dai wata majiya ta gwamnati ta karyata ikirarin jaridar Al-Watan, wadda ta ce Ahmed al-Sharaa ya amince wa Isra'ila ta yi amfani da sararin samaniyar Syria wajen samun bayanai kan tafiyar makaman da Iran ke harbawa.
Gidan talabijin na Syria TV da ke da mazauni a Turkiyya ya tattauna da wani mai sharhi, wanda ya ce ya kamata Syria ta kai ƙorafin wajen Majalisar Dinkin Duniya, sannan kuma ta yi amfani da ƙasashe ƙawayenta wajen hana karya ƙa'idojin amfani da sararin samaniyarta.
Gidan talabijin ɗain ya ce yakin na Iran da Isra'ila ya yi cikas ga zirga-zirgar jirage zuwa ƙasar da kuma datse kai tallafi ga al'ummar ƙasar masu buƙata.
Wata jarida ta yankin Larabawa, Al-Quds Al-Arabi ta ce akwia damuwa kan cewa yaƙin zai ƙara raunana tattalin arziƙin Syria wanda ba ya da ƙarfi, inda ta ce darajar kuɗin ƙasar ta Syria ya fadi da kashi 10 cikin ɗari tun bayan fara yaƙin.











