Yadda al'ummar gari guda suka tserewa hare haren 'yan bindiga a Sokoto

Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga garin Tozai a karamar hukumar Isa da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa baki-ɗayan al'ummar garin sun tsere zuwa jihohi makwafta saboda hare-haren 'ƴan bindiga da suka addabi yankin.
Rahotannin sun bayyana cewa a ƴan kwanakin da suka gabata, ƴan bindigar sun halaka mutane da dama, tare da sace wasu, ciki har da wata Amarya.
Wani mazaunin garin na Tozai da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa a baya-bayannan 'yan bindigar sun sace mutum 10 tare da halaka bakwai a garin.
Ya ce," A yanzu duk baki dayan mutanen garin sun gudu saboda hare haren 'yan bindiga inda wasu suka koma garin Isa wasu sun koma Zamfara, akwai wanda suka koma jihar Ondo wasu kuma sun gudu zuwa Auchi da ke jihar Edo."
"Kai akwai wadanda suka gudu zuwa Lokoja da kuma wanda suka koma Zaria, duka an barbazu zuwa jihohin Najeriya saboda irin halin ha ula'in da ake ciki a garin domin hare-haren sun yi yawa." In ji shi.
Mazauna garin dai sun roki gwamnatin jihar da ma hukumomin tsaro da su samar musu da jami'an tsaro na din-din-din a yankin domin al'umma su dawo don ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba a baya.
Mazaunin garin ya ce akwai jami'an tsaro a yankin to amma a cikin garin Tozai ne babu.
Ya ce," Babban abin takaicin shi ne ga damuna ta sauka lokacin da ya kamata mutane su yi noma to al'ummar gari duk sun watse ta yaya za a yi noma ke nan? Akwai matsala ke nan."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Idan har talaka bai samu abin da zai noma ba ai an shiga wani hali musamman bisa la'akari da irin yunwar da ake fama da ita yanzu a kasa." In ji shi.
Bashir Altine Guyawa, shi ne shugaban rundunar adalci ta jihar Sokoto ya shaida wa BBC cewa, gabaki dayan al'ummar gabashin jihar na cikin halin ni 'ya su.
Ya ce," Ko shakka babu wannan hari da yan bindiga ke kai wa gaskiya ne domin muna da sunayen wadanda aka kashe da suka hada da magidanta da dattijai, akwai kuma wadanda ke kwance a asibiti bayan raunin da suka samu sakamakon harin 'yan bindiga a garin Tozai din."
Bashir Altine, ya ce baya ga kashe mutane 'yan bindigar har sace mutane suke yi, don akwai garin da suka dauke amarya da 'yammatan amarya baki daya.
"A gaskiya al'ummar gabashin Sokoto sun galabaita haka suma na gabashin Shinkafi sun sha wuya." In ji shi.
Gabashin jihar Sokoto da ya hada da kananan hukumomin Isa da Sabon Birni na daga cikin yankunan da hare haren 'yan bindga yafi kamari a jihar ta Sokoto.










