Mu kwana lafiya
Karshen rahotannin ke nan a wannan shafi na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/01/2026.
Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin ke nan a wannan shafi na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Kotun Ƙolin ƙasar Guinea ta tabbatar da zaɓen shugaban ƙasar, inda jagoran juyin mulkin ƙasar Mamady Doumbouya ya lashe da tazara mai yawa.
Bayan wannan hukuncin na kotu, yanzu tsohon hafsan sojin ƙasar zai mulki ƙasar na tsawon shekara bakwai a ƙasar mai arzikin ma'adinai.
A ranar 28 ga Disamba ne aka yi babban zaɓen ƙasar, inda Kanal Doumbouya ya samu kashi 86.72 na ƙuri'un da aka kaɗa, duk da cewa akwai zargin jam'iyyun sun ƙi shiga zaɓen, sannan suka soki zaɓen.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa wanda ya zo na biyu Abdoulaye Yero Baldé ya janye ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar sakamakon zaɓrn.
Mr Baldé ya zo na biyu da kashi 6.59 na ƙuri'un da aka kaɗa a cikin ƴan takara takwas da suka shiga zaɓen.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
An ranstar da Delcy Rodríguez a matsayin shugabar riƙo na ƙasar Venezuela.
Ɗan uwanta Jorge Rodríguez ne ya rantsar da ita, wanda shi ne shugaban majalisar dokokin ƙasar.
Yayin bikin rantsuwar, ta ce ta zo ne domin karɓar ragama na riƙo cikin "raɗaɗi saboda irin wahalar da aka jefa al'ummar Venezuela bayan mamayar Amurka a cikin ƙasar".
Ta kwatanta Maduro da matarsa a matsayin "zaƙaru" kuma ta sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

Asalin hoton, EPA
Sakatare-janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya buƙaci Iran ta mutunta yancin masu yin zanga-zanga na yin zanga-zanga cikin lumana.
An yi ta samun tashin hankali a kwanaki tara da aka shafe ana zanga-zanga kan tsadar rayuwa da karyewar darajar kuɗin ƙasar, inda aka kashe gomman mutane.
Kakakin majalisar ƙasar Mohammed Bagher Ghalibaf, a yau litinin ya ce wajibi ne a saurari buƙatun masu zanga-zangar, kuma a yi amfani da buƙatun wajen kawo sauyi, sai dai ya ce akwai zanga-zanga da ake yi bisa tsari da wadda ake yi domin kawo rarrabuwa.
A jiya Lahadi ne gwamnati ta sanar da cewa za a riƙa ba ƴan ƙasar wani ɗan alawus duk wata domin sauƙaƙa musu tsadar rayuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotannin da jami'an tsaron Najeriya suka fitar, sun ce aƙalla sojoji tara ne suka mutu lokacin da jerin gwanon motocinsu suka taka wani abin fashewa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Wasu sojojin da dama kuma sun jikkata a harin da ya afku a ranar Lahadi.
Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.
Sai dai lamarin ya faru ne a yankin da masu iƙirarin jihadi na ISWAP ke gudanar da ayyukansu da kuma kai munanan hare-hare.

Asalin hoton, NEMA Nigeria/X
Aƙalla mutum biyar ne suka mutu, ciki har da wata uwa da yara huɗu bayan rugujewar wani gini a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a unguwar Binta Suga da ke birnin Maiduguri, inda ya jefa mazauna yankin cikin jimami.
Wani mazaunin unguwar mai suna Babagana Usman ya shaida wa BBC cewa ginin ba shi da wani lahani kafin ruftawarsa.
"Mutane na wucewa kan hanya gefen wani gida kwatsam sai gidan ya faɗi a kansu. Bayan faɗuwar ginin sai muka ji wata ƙara inda nan da nan muka fito don kawo ɗauki. Mun cire mutum kusan shida a ƙarkashin ɓaraguzan ginin.
"Mutum biyar ne suka mutu sannan ɗaya na karɓar kulawa a asibiti," in ji Babagana.
Ya ƙara da cewa tuni aka yi jana'izarsu a safiyar yau Litinin.
Mahaifin yara biyu cikin waɗanda suka rasu, Usman Abdullahi, ya ce sun shaku sosai da yaransa.
"Babban wanda ya rasu mai suna Abdulmalik shekararsa 11, sai mabiyinsa wanda suka kasance ƴan uwa. Abin da zan riƙa tunawa da su shi ne karanta al-Qur'ani duk lokacin da suka dawo daga Sallah," in ji Usman.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan China sun su fara biyan harajin kashi 13 na magunguna da kayan hana ɗaukar ciki ne daga farkon Janairu, amma sai aka cire haraji kan kula da yara a asibiri a ƙasar China.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sabon kundin harajin ƙasar da aka sanar a ƙarshen shekarar da ta gabata, inda a ciki aka yi gyara kan dokar haihuwar mutum ɗaya kacal da ƙasar ta ɗabbaƙa a shekarar 1994.
Sai dai kuma a sabuwar dokar an cire harajin kayayyaki a kan abubuwan da ake buƙata domin kula da dattawa da haraji na kayan aure.
Latsa nan don karanta cikakken labarin...

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana wa kotun New York cewa shi mutum ne mai nagarta, kuma bai aikata laifin komai da ya cancanci a tsare shi a Amurka ba.
Maduro ya bayyana haka ne a gaban kotu, inda ya ce, "ban aikata laifi ba. Ni mutumin kirki ne, kuma shugaban ƙasata," in ji shi kamar yadda tafinta ya fassara.
Maduro ya bayyana haka ne a matsayin martani bayan an zayyana masa tuhume-tuhume guda huɗu da ake zargin ya aikata.
Sai dai ya musanta aikata duka laifukan, sannan matarsa ma ta musanta aikata laifuka.
Laifukan da ake tuhumarsa da su sun haɗa da safarar miyagun ƙwayoyi da mallakar makamai da sauransu.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Gomman masu zanga-zanga sun taru a wajen kotun da za ta saurari ƙarar shugaban Venezuela Nicolas Maduro da maiɗakinsa.
Suna ta rera waƙoƙi cikin yaren Sifaniya, inda masu zanga-zangar goyon bayan Maduro suka kusa ninƙa waɗanda ba sa goyon bayansa.
Yawancin waɗanda suka taru suna riƙe da tutoci da kuma alamomin Venezuela.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Madeline Halpert/BBC

Asalin hoton, EPA/Shutterstock

Asalin hoton, Aminu Alhusaini Amanawa
Wata mummunar gobara ta yi barna a kasuwar masu gyaran motoci da ke Buzaye, a jihar Sokoto.
Wutar ta tashi ne sanadiyyar fashewar wani janareto, a cewar shugaban ƙungiyar Kanikawa reshen jihar ta Sokoto, Muhammad Raba.
"An yi asara mai ɗimbin yawa a kasuwar, kuma akwai aƙalla shaguna 84 da suka ƙone," in ji shi.
Wani wanda gobarar ta shafa ya ce ba ya kasuwar lokacin da abin da ya faru.
"Ina zaune kawai na ga kiraye-kirayen cewa gobara ta tashi a bayan shagunan mu, kafin na iso wutar ta ci abin da za ta ci. Ba zan iya kiyasta abin da na rasa ba," in ji shi.

Asalin hoton, Aminu Alhusaini Amanawa

Asalin hoton, EPA
Hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun hallaka wasu Falasɗinawa biyu, ciki har da wata yarinya da kuma jikkata wasu mutum huɗu, a birnin Khan Younis da ke kudancin yankin, a cewar jami'an asibiti.
Sojojin Isra'ila sun ce an kai harin da nufin far wa wani ɗan Hamas wanda ke barazana ga dakarunta.
Ma'aikatar lafiya a Gaza - wadda ke karkashin ikon Hamas - ta ce an kashe Falasɗinawa 422 tun bayan da yarjejeniyar zaman lafiya ta fara aiki a watan Oktoba.
An kashe sojojin Isra'ila uku tun watan Oktoban da ya wuce.

Asalin hoton, Getty Images
Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nuna damuwa cewa ba a mutunta dokokin ƙasa da ƙasa ba kan abin da Amurka ta aikata a Venezuela.
António Guterres ya bayyana haka ne a wani sako da aka karanta a taron gaggawa da majalisar ta kira kan batun na Venezuela.
"Abin damuwa ne matuka kan rashin mutunta dokar ƙasa da ƙasa a Venezuela.
"Lamarin zai iya janyo rashin daidaito a ƙasar, tasiri mara kyau a yankin da kuma yadda batun zai iya sauya yanayin dangantaka tsakanin ƙasashe," in ji Guterres.
Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kira wani taron gaggawa don tattauna abubuwan da ke faruwa a Venezuela.
Taron wanda ke gudana yanzu haka zai kuma tattauna kan "barazana ga tsaron duniya da kuma tsaro".
Hakan na zuwa ne bayan da sojojin Amurka karkashin umarnin shugab Donald Trump suka kutsa ƙasar tare kama shugaban ƙasar Nicolas Maduro da maiɗakinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Cuba ta bayyana cewa ‘yan ƙasarta 32 ne suka rasa rayukansu yayin harin da Amurka ta kai kan Venezuela wanda ya kai ga kama shugaban ƙasar, Nicolás Maduro.
Gwamnatin ta ce waɗanda suka mutu mambobin sojoji ne da ma’aikatan tattara bayanan sirri, inda aka ayyana kwanaki biyu a matsayin ranakun jimami da zaman makoki na ƙasa baki ɗaya.
Ba ta fayyace ainihin rawar da ‘yan Cuban suka taka a Venezuela ba, amma ƙasashen biyu suna da dangantaka ta dogon lokaci, inda Cuba ke ba da tallafin tsaro a madadin mai.
Shugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel, ya ce ‘yan ƙasarsa suna ba da kariya ga Maduro da matarsa bisa buƙatar Venezuela.
Venezuela dai har yanzu ba ta bayyana yawan mutanen da suka mutu yayin harin Amurka da aka kai a gidan shugaban ƙasar Maduro da ke Caracas ba a ranar Asabar.

Asalin hoton, Getty Images
Wata Kotu a Paris ta kama mutum 10 da laifin cin zarafin matar shugaban Faransa Brigitte Macron ta intanet.
Mutanen sun yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa jita jita inda suke nanata cewa matar shugaban ƙasar ba ita bace ba ɗanuwanta ne Joe Michel da aka yi wa sauyin jinsi.
Haka kuma, sun zargi matar shugaban ƙasar da aikata cin zarafi ta hanyar lalata kan Emmanuel Macron sakamakon cewa kwai bambancin shekaru 24 a tsakaninsu.
Sun wallafa ƙarairayin ne a shafukan intanet inda dubban daruruwan mutane suka karanta.
Kotun ta bayyana cewa ƙarairayin da suka wallafa sun bazu sosai a intanet, inda dubban mutane suka karanta su. A hukuncinta, kotun ta yanke musu gargadin ɗaurin watanni takwas tare da tilasta musu neman ilimi kan kaucewa cin zarafi ta intanet.

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa fadar shugban ƙasa ta wallafa wani hoton shugaba Bola Tinubu da takwaran aikinsa na Rwanda Paul Kagame, wanda aka haɗa da ƙirƙirarriyar basira, wato AI.
Babban abin da ya janyo ce-ce-ku-cen a shafukan sada zumunta shi ne yadda aka ga tambarin fasahar AI na kamfanin Twitter, wato Grok a jikin hoton da aka wallafa na Tinubu a jiya Lahadi.
Wani mai taimaka wa Najeriya kan yaɗa labarai, Temitope Ajayi ya ce ba haɗa hoton aka yi da ƙirkirarriyar basira ba, sai dai an yi amfani da fasahar ce wajen "inganta kyawun hoton."
Ya bayyana cewa an ɗauki hoton ne da wayar hannu, kuma sai hoton ya kasance bai da inganci, wanda hakan ya sa aka yi ƙoƙarin inganta shi.
A ranar Lahadi ne mai taimaka wa shugaban Najeriya kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya wallafa hoton a shafinsa na X tare da rubuta cewa: "Shugaba Bola Tinubu a wurin cin abincin rana tare da shugaban Rwanda Paul Kagame, suna tattauna lamurran duniya da batun ciyar da Afirka gaba."
Sai dai jim kaɗan bayan wallafa hoton ne aka samu martani daga masu amfani da shafukan sada zumunta waɗanda suka lura da tambarin fasahar AI ta Grok a ɓangaren dama daga ƙasan hoton.

Asalin hoton, Getty Images/CNSP
A ranar Litinin ne gwamnatin Jamhuriyar Benin da ke Yammacin Afirka ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai na Jamhuriyar Nijar, a wani abu da masana ke bayyanawa da taɓarɓarewar alaƙa tsakanin ƙasasashen biyu.
A cewar hukumomin ƙasar ta Benin, sun ɗauki matakin ne bayan wasu lamurra da suka fi ƙarfinsu, kodayake ba ta fitar da wani ƙarin bayani a hukumance kan lamarin ba.
A nata ɓangare ita ma Jamhuriyar Nijar ta mayar da martani kan wannan mataki, in da ta umarci jami'in diflomasiyyar Benin ya saka hannu kan takardar dakatar da aiki, sannan ya bar ƙasar cikin sa'o'i 48.

Asalin hoton, Reuters/Adam Gray
Shugaban Venezuela Nicola Maduro da mai ɗakinsa na kan hanyarsu ta isa wata kotu a birnin New York, kwanaki biyu bayan da sojojin Amurka suka kama su a wani hari da suka kai Caracas.
Za a yi musu shari'ah ne bisa zarginsu da safarar muggan ƙwayoyi da kuma ta'addanci, laifukan da a baya suka musanta
A Venezuela kuwa, anjuma a yau ne za a rantsar da Delcy Rodriguez a matsayin shugabar riƙo ta Venezuela.
Gabanin taron shan rantsuwar a majalisar dokokin ƙasar, Miss Rodriguez ta wallafa a shafinta na sada zumunta cewa gwamnatinta na da niyyar ƙulla alaƙa ta mutuntaka da haɗaka da Amurka.
Sai dai mista Trump ya sake jaddada cewa a yanzu haka Amurka ce ke da iko da Venezuela.
Ga wasu hotunan da ke nuna yadda aka kai shugaban Venezuela Nicolás Maduro da matarsa, Cilia Flores gaban kotu a birnin New York cikin jirgi.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images
Iran da China sun yi kira ga Amurka da ta gaggauta sakin shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, da matarsa, Cilia Flores, yayin da martani daga ƙasashen duniya ke ƙaruwa kan lamarin.
Ma’aikatar harkokin wajen China ta bayyana cewa matakin Amurka "ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙa’idojin asali na hulɗar ƙasashen duniya" kuma tana ci gaba sa ido kan yanayin tsaro a Venezuela cikin kulawa.
Haka kuma, ta yi kira ga Washington da ta "daina ƙoƙarin rushe gwamnatin Venezuela, sannan ta warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da sulhu."
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baqaei, ya ce: "Abin da Amurka ta yi ba abu ne da za a yi alfahari da shi ba; bai dace ba."
Ya ƙara da cewa: "Kamar yadda mutanen Venezuela suka jaddada, dole ne a saki shugaban ƙasarsu."
Bugu da ƙari, Iran itama ta fuskanci barazana daga Donald Trump a makon da ya gabata, inda ya gargaɗi cewa Amurka za ta shiga tsakani idan har an ci gaba da kashe masu zanga-zangar lumana a Iran.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Manchester United ta kori mai horas da ƴan wasanta Ruben Amorim bayan faɗi tashin da ƙungiyar take yi a gasar Firimiyar Ingila.
A watan Nuwamban 2024 ne aka naɗa Amorim a matsayin mai horas da ƙungiyar, inda ya jagoranci ƙungiyar zuwa wasan ƙarshe na kofin Europa a watan Mayun da ya gabata, inda suka fafata da Bilbao.
Yanzu haka Manchester United ce ta shida a teburin Premier, duk da haka hukumomin ƙungiyar sun yi ta kawar da kai kan kiraye-kirayen sallamar kocin, har sai a wannan lokaci.
A cikin sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta ce "wannan shi ne lokaci mafi dacewa na kawo sauyi. Hakan zai bai wa ƙungiyar damar kammala kakar gasar Premier a mataki mafi dacewa.
"Ƙungiyar ta gode wa Ruben bisa ga gudumawar da ya bai wa ƙungiyar kuma tana masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.
"Darren Fletcher ne zai ja ragamar ƙungiyar a matakin riƙo a wasanta na gaba da ƙungiyar Burnley a ranar Laraba," kamar yadda sanarwar da ƙungiyar ta tabbatar.