Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 01/01/2026

Wannan shafi na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye dangane da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 01/01/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Ana zargin Abiy Ahmed da hana shigar da kayan agaji sansanin ƴan gudun hijra a Tigray

    Jam'iyya mai mulkin yankin Tigray na Habasha ta zargi gwamnatin Abi Ahmed da hana shigar da agaji sansanonin 'yan gudun hijira.

    Jam'iyyar TPLE ta ce ci gaba da hakan na barazana ga dubban 'yan gudun hijirar da ke tsananin bukatar taimako, wadanda yunwa ta tagayyara. Kuma hakan ya take yarjejeniyar Pretoria da aka cimma ta kawo karshen yakin shekaru biyu a yankin na Tigray.

    Ta kara da cewa kusan 'yan gudun hijira miliyan daya ba za su iya komawa yammacin Tigray ba, wanda sukai ikirarin gwamnatin Habasha ce ke iko da shi.

    TPLF ta yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da kungiyar Tarayyar Afurka su sa baki kan lamarin.

  2. Harin ƴan tawayen M23 ya kashe fararen hula 1,500 a DR Congo

    A jamhuriyar Dimukradiyyar Congo an kashe farar hula 1500 a sabbin hare-hare da 'yan tawayen M23 da Rwanda ke marawa baya a kudancin yankin Kivu.

    Wata sanarwa da gwamnatin Congo ta fitar, ta ce sojoji da jami'an tsaro ne suka fitar da adadin, duk da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan Disamba da ya wuce a Amurka.

    Kinshasa ta ce sama da farar hula dubu 500 sun rasa muhallansu, sakamakon kazamin fadan da ya rincabe tsakanin sohin gwamnati da na 'yan tawaye a yankuna daban-daban na ƙasar.

    Tun da fari 'yantawayen M23 sun janye daga gabashin yankin Uvira, inda suka ce matakin na cikin yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranta, to amma da alama fada ya sake dawowa.

  3. Ƴansanda sun kama direban motar da Anthony Joshua ya yi hatsari

    Ƴansanda a Najeriya sun ce suna tsare da direban da ke tuka motar da zakaran damben nan ɗan Birtaniya, amma ɗan asalin Najeriya Anthony Joshua ke ciki a lokacin da sukai mummunan hatsari a babban titin Lagos zuwa Ogun, wanda ya yi ajalin mutum biyu.

    Rundunar ƴansandan jihar Ogun ta ƙara da cewa sun tafi da shi ne bayan an sallame shi daga asibiti, domin fara binciken abin da ya jawo hatsarin, wanda ya yi ajalin abokan Joshua biyu da suka zo Najeriya tare.

    Binciken farko-farko ya nuna cewa akwai yiwuwar gudun wuce ƙima da yunƙurin ratse ne suka sa motar da ƙwace, ta yi karo da babbar motar ɗibar kaya da ke tsaye a bakin hanya.

    Joshua ya ji rauni a hatsarin, yayin da abokansa, Sina Ghami da Latif Ayodele, da ake yi wa lakabi da Latz suka rasu nan take.

  4. Likitoci a Sudan sun ce an bude asibiti na uku a birnin Khartoum

    Kungiyoyin likitoci a Sudan sun ce an sake bude asibiti na uku da yaki ya daidaita a birnin Khartoum.

    Kungiyar likitocin ta ce an tun a shekarar farko ta yakin aka lalata fannin kiwon lafiya a birnin, dole yawancin asibitoci manya da kanana suka dakatar da aiki sakamakon rashin magunguna da sauran kayan bukatu.

    Ta ce ana sa ran za a kara bude karin asibitoci da cibiyoyin lafiya a wannan watan na Junairu.

    Hakan ya samu bayan karbe ikon birnin Khartoum da sojojin Sudan suka yi daga hannun 'yan tawayen RSF.

  5. Rasha ta zargi Ukraine da kisan Rashawa 24

    Rasha ta zargi Ukraine da kisan aƙalla mutane 24 ciki har da yaro a harin jirgi maras matuki a wani Otal da ta ke iko da shi a kudancin Ukraine, sai dai sojin Kyiv ba su yi martani kan zargin ba.

    Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce harin da aka kai ma ta laifin yaki ne, kuma Ukraine tajima ta na shirin kai shi wanda ta kai kan farar hula. Jami'an Rasha sun sha alwashin mai da martani.

    Hotunan da Rasha ta yada da ba a tabbatar da sahihancinsu sun nuna girman barnar harin.

    Sun nuna yadda wuta ke cin wani gini, da gawar da aka rufe da farin kyalle da abin da ya yi kama da jirwayen jini a kasa.

  6. Mutane da dama sun mutu sakamakon gobara a Switzerland

    'Yansandan Switzerland sun ce ana fargabar gwamman mutane sun mutu lokacin da gobara ta tashi a wurin shakatawa na Ski resort of Crans- Montana.

    Sun ce sama da mutum 100 sun jikkata, yawancinsu cikin mawuyacin hali. Gobarar ta tashi ne da safiyar yau Alhamis a mashayar da ke wurin shakatawar wadda ke cike da mashaya da ke bikin shiga sabuwar shekara.

    Mathias Reynard shi ne gwamnan yankin ya kuma yi wa manema labarai karin bayani, ta bakin tafinta;

    Yace mu na mika sakon ta'aziyya ga iyalan da ke cikin alhanin mutuwar 'yan uwansu a wannan gobara, kamata ya yi wannan lokaci ya zama na murnar shiga sabuwar shekara, amma ya koma na alhini.

    Ganau sun ce sun ji karar fashewar wani abu, amma har yanzu ba a kai ga gano abin da ya haddasa gobarar ba, amma hukumomi sun ce ba harin ta'addanci ne ba.

  7. An rantsar da Zohran Mamdani a matsayin Magajin garin birnin New York

    A ranar 1 ga watan Janairun nan na sabuwar shekarar 2026 aka rantsar da Zohran Mamdani a matsayin Magajin garin New York, inda ya kafa tarihin zama Musulmi na farko da ya riƙe ofishin sannan kuma mafi ƙarancin shekaru da ya riƙe kujerar a fiye da ƙarni.

    Ya kasance Magajin garin na New York na 111 kuma alƙalin alƙalan birnin, Letitia James ce ta jagorancin bikin rantsarwar a farkon daren ranar 1 ga sabuwar shekarar 2026.

    A watan Nuwamba ne dai matashin mai shekaru 34 ya kafa tarihi inda ya lashe zaɓen zama Magajin garin na birnin New York.

    Zaɓen bana ya jawo hankalin jama'a sosai. Mamdani, mai shekaru 34, wanda dan majalisar dokoki ne a jihar New York inda ya fara shekarar ba tare da sanin jama'a sosai ba, amma daga baya ya zama sananne.

    Wannan nasara tana nuna sabon salo ga masu ra'ayin cigaba, kuma tana nuna sauyin tunanin siyasa a birnin.

  8. Zalensky ba ta shirya ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya ta mako ɗaya da Rasha ba

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce Ukraine ba ta shirya sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ta mako guda da Rasha ba wadda ya ce babu abin da zata haifar sai kara rura wutar rikicin da ke tsakaninsu.

    Cikin sakonsa na sabuwar shekara daya gabatar ga al'ummar kasar, Mr Zelensky ya ce Ukraine na son a kawo karshen yakin to amma ba wai ta kowanne hali ba.

    Ya ce yanzu haka an amince da kashi 90 ciki na kunshin yarjejeniyar a yayin tattaunawar da aka yi da wakilan Amurka da kuma shugabannin kasashen Turai a makonni da suka wuce.

    Ya ce sauran kashi 10 cikin 100 na yarjejeniyar ya kunshi makomar Ukraine da kuma kasashen Turai ne.

    Tun da farko, babbar jami'ar diplomasiyya a kungiyar Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta bayyana goyon bayanta ga Ukraine inda ta yi watsi da ikirarin Rasha na cewa Ukraine ta kai hari da jirgi marar matuki kan gidan shugaba Putin da ke Novgorod.

  9. Yadda sabon harajin Najeriya zai shafe ku a 2026

    A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka wa hannu domin amincewa ta zama doka.

    An dai ta tunanin cewa za a dakatar da fara aiwatar da harajin kafin sabuwar shekara sakamakon zarge-zargen cushe da aka yi wa dokar ta haraji, wadda aka ce ta bambanta da asalin wadda majalisar dokoki ƙasar ta amince da ita.

    A ranar 30 ga watan Disambar 2025 ne shugaba Tinubu ya sanar da cewa babu buƙatar dakatar da fara aiwatar da harajin domin hakan zai katse wa Najeriya burinta na samar da cigaban da ake buƙata.

    Sai dai ya ce yana sane da irin zarge-zargen da ake yi dangane da cushe a dokar kuma yana aiki da majalisar dokokin ƙasar wajen samar da mafita.

    Yanzu dai abin da al'ummar Najeriyar ke son sani shi ne ta yaya wannan haraji zai shafe su daga ranar 1 ga watan Janirun sabuwar shekarar 2026? BBC ta yi nazarin dokar harajin ga kuma bayanan da ta tattara.

  10. Amurka ta kai hare-hare kan jiragen ruwan Venezuela

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta ƙaddamar wasu jerin hare-hare a cikin kwanaki biyu akan wasu jiragen ruwa da ta zargi na safarar miyagun kwayoyi ne a tekun Venezuela inda ta kashe akalla mutum takwas.

    Rundunar ta ce hari na farko ta kai shi ne kan wasu jiragen ruwa uku da suka yi jerin gwano suna tafiya a tekun inda ta kashe wadanda ta kira masu safarar miyagun kwayoyi a daya daga cikin jiragen.

    Rundunar ta ce hari na biyu kuwa ta kai shi ne a daren sabuwar shekara inda ta kashe mutum biyar.

    Masu tsaron tekun Amurka sun ce suna neman wadanda suka tsira, to amma sun ce basu sani ba ko akwai wanda ya tsiran.

    Gwamnatin Trump ta kai hare-hare fiye da 30 akan mutanen da ta ke zargi suna safarar miyagun kwayoyi a yankin Pacific da kuma Karebiya tun daga watan Satumbar daya gabata inda ta kashe kusan mutum 120.

  11. Dokar hana bulaguro shiga Amurka daga ƙasashe 40 ta fara aiki

    Dokar hana balaguro zuwa Amurka da ta shafi kusan ƙasashe 40 ta fara aiki daga yau 1 ga Janairu.

    Fadar White House ta ce ta ɗauki matakin haramcin ne da ya shafi ƙasashen Afrika da dama saboda dalilai na tsaron ƙasa.

    Fadar White House ta ce haramcin na balaguro zuwa Amurka ya biyo bayan damuwa kan tsarin tantancewa da kuma matsalar ƴan kama wuri zauna waɗanda ke zarce wa'adin bizarsu.

    Sai dai ƙasashen Mali da Burkina Faso da ke ƙarƙashin ikon soji kuma da ke cikin jerin ƙasashen da haramcin ya shafa sun ce su ma za su haramta wa Amurkawa shiga ƙasashensu.

    Tuni dai ƙwararru suka ce wannan yunƙuri zai haifar da rashin tabbas ga 'yan ciranin da yanzu haka ke a Amurka da kuma ƙara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da wasu ƙasashe na Afirka.

  12. Shugaban Taiwan Lai Ching-le ya lashi takobin kare ƙasar daga China

    Shugaban Taiwan Lai Ching-te, ya lashi takobin kare 'yanci da martarbar yankinsa bayan China ta kaddamar da wani atisayen soji a kusa da yankin wanda China ke iƙrarin cewa nata ne.

    Cikin saƙon sabuwar shekarar da ya gabatarwa ƴan ƙasar, Mr Lai ya yi alƙawarin ƙarfafa tsaron yankinsa.

    Ya ce ƙasashen duniya na ganin ko al'ummar Taiwan za su iya kare kansu, inda ya nemi su yi aiki tare wajen ƙarfafa dakarunsu a daida lokacin da suke fuskantar barazana.

    Mista Lai Ching-le ya kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi kasuwanci da haɗin kai tare da Amurka.

  13. Trump ya bayar da umarnin janye sojoji daga birane uku

    Shugaba Trump ya bayar da umarnin janye dakaru daga birane uku da jam'iyyar Democrats ke mulki inda aka kai su domin su magance matsalar kwararar bakin haure da kuma aikata muggan laifuka.

    Cikin wani sako daya wallafa na shafinsa na sada zumunta, shugaban ya ce dakarun zasu iya komawa biranen da suka hada da Chicago da Los Angeles da kuma Portland, muddin aka ci gaba da aikata muggan laifuka.

    Sanya dakarun akan titunan biranen ya janyo daukar matakin shari'a dukkan biranen uku.

    Shugabannin biranen da ma 'yan jam'iyyar Democrats sun zargi Mr Trump da zuzuta abubuwan da ke faruwa a biranen.

  14. Idan muka yi haƙuri za mu ga alfanun sabuwar dokar haraji - Tinubu

    Shugaba Tinubu na Najeriya ya ce idan ƴan Najeriya suka yi haƙuri za a samu rayuwa mai inganci ta hanyar alkilta arziƙin ƙasa yadda ya kamata abin da zai sa ƙasar ta yi fice a duniya a wannan sabuwar shekara ta 2026.

    Tinubu ya shaida hakan ne a saƙon sabuwar shekara da ya fitar ranar Alhamis inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa ci gaba da gini a kan abin da ta fara na sauye-sauye masu alkairi ga ƴan Najeriya.

    "Duk da irin ƙalubalen da duniya ke fuskanta ta fuskar tattalin arziƙi, mun samu gagarumar nasara a 2025 musamman a fannin tattalin arziƙi".

    Dangane kuma da sabuwar dokar haraji da ta fara aiki, Tinubu ya nemi ƴan Najeriya da su ƙara hakuri domin nan gaba kaɗa za su ga alkairin tsarin.

    Ya kuma ce ɗaya daga cikin dailan aiwatar da wannan sabon tsarin harajin shi ne kawo sauyi wajen tatsar ƴan Najeriya harajin da ya wuce ƙima.

    "Muna kuma son kawo ƙarshen biyan haraji da yawa inda dukkan matakan gwamnati kan karɓi haraji. Na yaba wa jihohin da suka amince da shiga tsarin harajin na bai ɗaya domin sauwaƙe wa jama'a yawan haraje-haraje a kan al'umma da kayan abinci."

    "Sabuwar shekarar ta fara da aiwatar da sauye-sauyen harajin da aka yi domin dasa harsashin Najeriya mai adalci da kuma ƙarfi a fannin kudaɗen shiga," in ji Tinubu.

  15. Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya ta sanar da fara zanga-zanga kan sabuwar dokar haraji

    Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya, NANS ta fara shirin wayar da kan ɗalibai domin gudanar da zangaz-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin amince wa da aiwatar da sabuwar dokar haraji da ta fara aiki a ranar 1 ga watan nan na Janairun 2026.

    Shugaban ƙungiyar, Olushola Oladoja ya ayyana ranar 14 ga watan Janairun 2026 a matsayin ranar ɗaukar mataki kan dokar a Najeriya .

    A wata sanarwa Oladoja ya nuna rashin dacewar aiwatar da dokar a ranar 1 ga watan na Janairu a daidai lokacin da kiraye-kiraye suka yawaita kan a dakatar da ita saboda zargin cushe.

    Ya ƙara da cewa ƙaddamar da dokar harajin "ba wai kawai abin takaici ba ne wani abu ne mai haɗari ga gwamnatin da take ikrarin aiwatar da tsare-tsare na jama'a da kuma bin ƙa'idodjin dimokraɗiyya."

  16. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin sashen hausa na BBC kai tsaye barkan mu da shiga sabuwar shekarar 2026.

    Da fatan Allah ya ba mu alkairan da ke cikinta. Ya kuma kare mu daga dukkan sharrin da ke wannan shekara. Allah ya ba mu lafiya da imani da wadata da kuma tsawon ran ganin ta baɗin baɗaɗa.

    Ga ƴan Najeriya masu bibiyar mu, muna yi muku tuni cewa za ku iya duba wannan labarin domin sanin yadda sabon harajin da kuka wayi gari da shi zai shafe ku.

    Da fatan za a ci gaba da kasancewa da shafin namu domin samun sahihan labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a Najeriya da ma saurna sassan duniya. Mun gode!