'Rasha ba ta shirya tattaunawar zaman lafiya da Ukraine ba' - von der Leyen

Asalin hoton, EPA
Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana halin da ake ciki a yaƙin Ukraine a matsayin "mai cike da tashin hankali" kuma "mai matuƙar hatsari" tare da zargin Rasha da cewa ba ta da niyyar shiga tattaunawar sulhu.
Kalaman na ta sun zo ne jim kaɗan kafin mai magana da yawun Kremlin Dmitry Peskov ya ce "ya yi wuri" a fara maganar ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya.
Von der Leyen ta ce Ukraine za ta buƙaci ƙwaƙƙwaran tabbacin tsaro da zai iya hana aukuwar duk wani hari nan gaba, ta na mai cewa har yanzu Rasha na tunani irin na zamanin yaƙin duniya na biyu kuma tana kallon nahiyar Turai a matsayin wurin da za ta iya mamayewa.
Ta yi jawabi ne a Majalisar tarayyar Turai a Strasbourg yayin da Amurka ta ƙara zage damtse wajen tabbatar da yarjejeniya tsakanin Kyiv da Moscow.
Bayan tattaunawar da aka yi a wannan makon a Geneva da kuma Abu Dhabi, Ukraine ta amince da wani daftarin yarjejeniyar zaman lafiya, bayan da aka yi kwaskwarima kan wani shiri na farko da ke kunshe da sharuɗɗa 28, wanda ya sha suka bayan an yi zargin cewa ya fifita muradun Rasha.
Shugaban Ukraine Vlodymyr Zelensky ya ce sabon daftarin yana nuni da "hanyar da ta dace" - amma har yanzu akwai manyan batutuwan takaddama da Rasha kuma Kremlin ta yi watsi da batun cewa an kusa sasantawa.


















