Ƙungiyoyin da ke adawa da Hamas sun nemi shiga sabuwar gwamnatin Gaza

Mambobin ƙungiyar Yasser Abu Shabab masu ɗauke da makamai suna sauraron jawabin mataimakin kwamandansu, Ghassan al-Dhahini (16 Nuwamba 2025)

Asalin hoton, Yasser Abu Shabab/Facebook

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin mayaƙan sa kai, Popular Forces, na gudanar da ayyukanta a kusa da birnin Rafah da ke kudancin Gaza
    • Marubuci, Lucy Williamson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ana ci gaba da gabatar da muhimman tambayoyi game da wasu ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da suka fito don yaƙar Hamas a Gaza cikin ƴan watannin nan.

Sun haɗa da ƙungiyoyin da ke da alaƙa ta dangi da juna da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma sabbin mayaƙan sa-kai - wasu daga cikinsu suna samun goyon bayan Isra'ila, kamar yadda firaministan ta ya amince da hakan a cikin kwanan nan.

An yi imanin wasu mutane da ke cikin Hukumar Falasdinawa - wacce ke mulkin wasu sassan Gaɓar yamma Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye kuma abokiyar hamayyar Hamas ce ta siyasa - su ma suna aikewa da tallafi a ɓoye.

To sai dai waɗannan mayaƙan sa-kai- da kowannensu ke aiki a yankinsa na cikin kashi 53 cikin ɗari na zirin Gaza da sojojin Isra'ila ke iko da su a halin yanzu - ba a shigar da su a hukumance cikin shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump ba.

Shirin na Trump ya buƙaci a kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa da kuma sabuwar rundunar ƴansandan Falasdinawa da ta samu horo don tabbatar da tsaron Gaza a mataki na gaba na yarjejeniyar.

Ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin mayaƙan sa kai na ƙarƙashin jagorancin, Yasser Abu Shabab, wanda ƙungiyarsa ta Popular Forces ke aiki a kusa da birnin Rafah da ke kudancin ƙasar.

A cikin wani bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta cikin kwanakin nan, mataimakinsa ya yi magana game da aiki tare da kuma haɗin gwiwa tare da kwamitin sulhu.

Hossam al-Astal ne ke jagorantar dakarun yaƙi da ta'addanci a kusa da birnin Khan Younis

Asalin hoton, Hossam al-Astal/Facebook

Bayanan hoto, Hossam al-Astal ne ke jagorantar dakarun yaƙi da ta'addanci a kusa da Khan Younis

Hossam al-Astal, wanda ke jagorantar dakarun sa-kai da ake kira Dakarun yaƙi da ta'addanci a kusa da birnin Khan Younis na kudancin ƙasar, ya shaida wa kafafen yaɗa labaran Isra'ila a wannan makon cewa "Wakilan Amurka" sun tabbatar da cewa ƙungiyarsa za ta taka rawa a cikin rundunar ƴansandan da za ta kasance a Gaza a nan gaba.

Wani jami'in Amurka ya ce ba su da wani abin da za su bayyana a halin yanzu.

A farkon wannan watan, Astal ya yi murmushi lokacin da na tambaye shi ko ya yi magana da Amurkawa game da makomar yankin, ''kuma ya shaida mun zai ba da cikakken bayani nan ba da jimawa ba''.

Na tambayi ko waɗancan tattaunawar sun sanya shi farin ciki.

"Eh" in ji shi yana murmushi.

Hoton da aka ɗauka daga bidiyon Hossam al-Astal da ke nuna kayan lambu da aka shigar Gaza

Asalin hoton, Hossam al-Astal

Bayanan hoto, Wani bidiyo da Hossam al-Astal ya wallafa ya nuna kayan abinci da aka kai birnin tantin da mayaƙan ke iko da shi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hossam al-Astal ya taɓa yin aiki da Hukumar Falasdinu.

Ƙungiyarsa ƙarama ce - amma tana ƙara samun ƙwarin gwiwa, kuma ta na iko da wani gari mai tantuna da ke kusa da Khan Younis.

Astal ya yi murmushi lokacin da na tambaye ta ko Isra'ila ce ke kawo masa kaya.

"Amma muna haɗa kai da ɓangaren Isra'ila don kawo abinci da makamai da sauransu."

Na tambayi yadda ya ke biyan su.

"Mutane a duk faɗin duniya suna tallafa mana," in ji shi.

"Ba duka daga Isra'ila ba ne, suna da'awar cewa Isra'ila ce kaɗai ke tallafa mana kuma mu wakilan Isra'ila ne, mu ba wakilan Isra'ila ba ne."

Ya shaida mun cewa dubban iyalai sun zo zama a sabon wurin nasa, kusa da layin da aka shata wanda ke nuna yankin da Isra'ila ke iko da shi a halin yanzu a ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta - kuma mutane da yawa suna zuwa kowane mako.

"Mu ne sabuwar Gaza," in ji shi.

"Ba mu da wata matsala wajen haɗa kai da gwamnatin Falasɗinawa da Amurkawa, da duk wani wanda ke da alaƙa da mu. Mu ne madadin Hamas."

Sai dai da yawa daga cikin mutanen Gaza - ciki har da waɗanda suka yanke ƙauna da Hamas - ba su ji daɗin sabon ikon da aka bai wa waɗannan ƙananan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ba.

Saleh Sweidan, wanda a halin yanzu yake zaune a birnin Gaza ya ce "Mutane ƙalilan ne waɗanda ba su da addini imani, ko ɗa'a ne suka shiga cikin waɗannan miyagun mutanen masu aikata laifuka."

"Gwamnatin Gaza ita ce ke mulkin mu, kuma duk da cewa akwai nauyi da yawa kan fararen hula, amma kowace irin gwamnati ta fi ƙungiyoyin masu aikata laifuka."

Zaher Doulah, wani mazaunin Gaza ya ce "Waɗannan ƙungiyoyin da ke ba da haɗin kai da mamayar [Isra'ila] su ne abu mafi muni da yaƙin ya haifar."

"Shiga ƙungiyarsu haɗari ba ne kaɗai, amma babban cin amana ne."

Ashraf al-Mansi ya karanta wata sanarwa a gaban wasu mutane ɗauke da makamai a ranar 14 ga Oktoba, 2025

Asalin hoton, Ashraf al-Mansi

Bayanan hoto, Ashraf Mansi, shugaban ƙungiyar People Army - Northern Forces, ya gargadi Hamas a cikin wani bidiyo a watan Oktoba cewa kada su kusanci arewacin Gaza inda mayaƙansa ke gudanar da al'amuransu.

Montaser Masoud ɗan shekaru 31 da haihuwa ya shaida min cewa ya shiga sabon birnin Tanti na al-Astal watanni biyu da suka gabata tare da matarsa ​​da ƴaƴansa huɗu.

Sun kuma tsallaka iuyakar da sojojin Isra'ila suka shata da daddare don guje wa Hamas, kuma suka samu goyon bayan sojojin Isra'ila.

Sai dai ya ce ƴan'uwansa ​​da suka tsaya a baya a yankunan da Hamas ke iko da su na sukar matakin.

Ya ce da ni, "Sun yi ta tursasa mu, suna cewa abin da mu ke yi ba daidai ba ne kuma ba shi da makoma."

Ya ci gaba da cewa a yayin da mu ke magana ta wayar tarho, ƙarar harbe-harbe da aka yi a kusa da shi ya ci karo da hirarmu.

"Rundunar sojojin [Isra'ila] ce a kusa," in ji shi.

"Amma wannan ba matsala ba ce domin mun san ba mu ne ake hari ba."

Yasser Abu Shabab

Asalin hoton, Yasser Abu Shabab/Facebook

Bayanan hoto, Yasser Abu Shabab ne ke jagorantar mayaƙan ƙungiyar Popular Forces da ke Rafah

Yanzu haka dai ƙungiyoyi da dama masu ɗauke da makamai suna tunkarar Hamas, inda suke da alaka mai sarƙaƙiya da juna.

Misali ana zargin ƙungiyar Abu Shabab da aukawa motocin agaji da aka aika zuwa Gaza a lokacin yaƙin, kuma rahotanni a Isra'ila sun nuna cewa wasu mambobinta biyu suna da alaƙa a baya da ƙungiyar IS.

"Me matasalar haka?" Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya faɗa a watan da ya gabata yayin da yake mayar da martani kan labarin cewa ƙasarsa na goyon bayan ƙungiyoyin ƴan bindiga a asirce.

"Abu ne mai kyau. Yana ceton rayukan sojoji."

Ya ce fitar da wannan bayanan , "ya taimaka wa Hamas ne kawai".

Maj-Gen Anwar Rajab kakakin jami'an tsaron hukumar Falasdinu
Bayanan hoto, Manjo Janar Anwar Rajab na hukumar Falasɗinawa ya ce ba za a iya shigar da ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai cikin sabuwar rundunar ƴan sandan Gaza ba.

Netanyahu ya nace cewa Gaza ba za ta kasance ƙarƙashin Hamas ko kuma abokiyar hamayyarta, hukumar Falasdinu ba.

A ƙarƙashin shirin wanzar da zaman lafiya na Amurka, kwamitin da ba na siyasa ba, na Falasdinawa zai tafiyar da Gaza cikin ƙanƙanin lokaci ƙarƙashin kulawar ƙasashen duniya, har sai an kammala sauye-sauyen a hukumar Falasdinawan.

Sai dai wani babban jami'in Falasdinu ya yi watsi da iƙirarin Astal na cewa mayaƙansa za su kafa wani ɓangare na rundunar ƴan sanda a nan gaba.

Maj-Gen Anwar Rajab, kakakin hukumar tsaron Falasdinu, ya shaidawa BBC cewa ba za a tattaro mutane kai-tsaye daga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai na Gaza ba, waɗanda wasunsu ke samun goyon bayan Isra'ila.

"Isra'ila za ta iya neman haɗewar waɗannan mayaƙa, saboda cimma wasu muradun siyasa da tsaro na Isra'ila," in ji shi a wata hira da aka yi da shi a birnin Ramallah da ke gaɓar yamma da kogin Jordan.

"Amma buƙatun Isra'ila ba lallai ba ne su amfanar da Falasdinawa ba, Isra'ila na son ci gaba da jadadda ikonta ta wata hanya ko wata a zirin Gaza."

 Foton da ke nuna membobin ƙungiyar People's Army - Northern Forces suna sintiri a arewacin Gaza a ranar 30 ga watan Satumba 2025

Asalin hoton, ab.kaser/TikTok

Bayanan hoto, Membobin ƙungiyar People's Army - Northern Forces suna sintiri a arewacin Gaza

Har yanzu dai ba a amsa tambayar me zai faru da sabbin mayaƙan na Gaza a ƙarƙashin shirin zaman lafiya mai ɗorewa ba.

Matakin da Isra'ila ta ɗauka na marawa maƙiyan maƙiyansu baya a Gaza, alama ce da ba su yi koyi da tarihi ba, a cewar Michael Milshtein, tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Falasdinawa ta Isra'ila.

"Wannan shi ne irin kasadar da Amurkawa suka yi a Afghanistan shekara 30 da suka gabata," in ji shi.

"Sun goyi bayan ƴan Taliban a kan ƴan Sobiet, sannan Taliban ta ƙwace makaman da suka samu daga hannun Amurkawa suka yi amfani da su a kan Amurkawa."

Ya ce a halin yanzu Isra'ila ta dogara ne da ƙungiyoyin da a ke kokwanto kan asalinsu da fatan za su kasance madadin Hamas a fannin siyasa ko aƙida .

"Akwai wani lokaci da za su juya bindigoginsu - bindigogin da suka samu daga Isra'ila - a kan IDF [Rundunar Tsaron Isra'ila]," in ji shi.

Michael Milshtein
Bayanan hoto, Tsohon jami'in leƙen asirin sojin Isra'ila Michael Milshtein, ya ce Isra'ila na yin kasada ta hanyar mara wa mayaƙa ƴan sa -kai na Falasdinawa baya

Baya ga taimakawa wajen raunana Hamas, goyon bayan da Isra'ila ke bai wa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai zai iya sauƙaƙa raba kan Falasdinawa ƴan adawa da Isra'ila, da kuma ci gaba da yin tasiri a cikin Gaza da zarar dakarunta sun janye.

Wasu masu sukar lamirin sun ce bai wa irin waɗannan ƙungiyoyin makamai zai zai kawo cikas a yunƙurin da ake yi na kwance damarar Hamas.

Sai dai haɗarin da Isra'ila ke fuskanta shi ne cewa ƙungiyoyin da su ek marawa baya a yau, gobe za su kasance abokan hamayyarta.

Shekaru 40 da suka gabata, ta ƙarfafa wa wata ƙungiya mai tsaurin ra'ayin Islama a Gaza gwiwa domin ta taƙaita ƙarfin ikon shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat.

Ƙungiyar ce ta zama Hamas.