Zaɓen Najeriya 2023: Abin da ya sa babu tambarin jam'iyyar Labour a wasu takardun kaɗa ƙuri'a

Asalin hoton, Getty Images
An gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokokin na tarayya a Najeriya, yayin da jam'iyyu huɗu ke kokowar samun kujerun majalisun dokoki, Jam'iyyar APC mai mulki da PDP da LP da kuma NNPP masu adawa.
To sai dai ƴan sa'o'i kafin fara kaɗa ƙuri'ar, an yi ta yaɗa wasu hotuna da bidiyo a shafukan sada zumunta da suke nuna cewa babu suna da alamar jam'iyyar LP a takardun kaɗa ƙuri'a na kujerun sanata da 'yan majalisun wakilai a wasu jihohin ƙasar.
Magoya bayan jam'iyyar sun yi zargin cewa da gangana aka yi hakan domin hana su zaɓen jam'iyyar.
Daga ina zargin ya samo asali?
Jam'iyyar ce ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Tuwita, wanda ke nuna wasu mutane da ake gani a matsayin jami'an zaɓe suna buɗa takardun kaɗa ƙuri'a domin nuna wa wakilan jam'iyyu.
A cikin bidiyon an jiyo wata murya na cewa ''babu sunan jam'iyyar LP a takardun kaɗa ƙuri'a na sanata a nan Legas. Amma akwai a takardun kaɗa ƙuri'a a na shugaban ƙasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Magoya bayan jam'iyyar da dama a shafin Tuwita da Facebook a faɗin duniya sun yi ta yaɗa bidiyoyi da hotuna daga rumfunan zaɓensu, suna masu cewa babu alamar jam'iyyar a takardun kaɗa ƙuri'a na majalisun dokokin.
An yi ta yaɗa zarge-zargen cewa da gangan INEC ɗin ta cire suna da alamar jam'iyyar a takardun kaɗa ƙuri'ar.
Wasu sun yi ta yaɗa cewar sun samu ganin alamar jam'iyyar a kan takardun, to sai dai babu sunan jam'iyyar, sun masu iƙirarin cewa da gangan INEC ta yi hakan domin ta ruɗar da masu kaɗa ƙuri'a.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wani mutum mai mafani da shafin Tuwita mai suna @blackduke89 ya ce ''sun cire alamar jam'iyar LP daga jikin takardun kaɗa ƙuri'a domin su rikitar da ni. Shugabanni suna ruɗar da ni
To sai dai alamar jam'iyyar LP ba ya ɗauke da sunan jam'iyyar, sai dai taken takenta na -"Forward Ever". Kuma INEC na buga takardun kaɗa ƙuri'a ne kamar yadda kowacce jam'iyya ta aike mata.
Shin da gaske ba a samu alamar jam'iyyar LP a takardun kaɗa ƙuri'ar ba?
Zainab Aminu Abubukar jami'a ce a hukumar zaɓen ta kuma shaida wa BBC cewa haƙiƙa babu alamar jam'iyyar ta LP a wasu takardun kaɗa ƙuri'a na majalisun dokoki.
Amma kuma a cewarta hakan ya faru ne sakamakon rashin bayar da sunayen 'yan takarar jam'iyyar a waɗannan mazaɓun.
Ta ƙara da cewa jam'iyyar ta kai hukumar zaɓen ƙara gaban kotu bayan da ta fuskanci babu alamarta a kan takardun kaɗa ƙuri'ar, inda ta buƙaci kotun da ta tilasta wa hukumar sanya alamarta a kan takardun kaɗa ƙuri'ar, duk kuwa da cewa ba ta bayar da sunayen 'yan takararta a waɗannan mazaɓu ba.
Haka kuma ta ce jam'iyyar ba ta bayar da bahasi kan buƙatar da INEC ɗin ta gabatar mata na bayar da sunayen ƴan takarar ba, har sai a lokacin fara zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2025, kamar yadda INEC ɗin ta bayyana.
Hajiya Zainab ta ce idan da a ce jam'iyyar ta samu wata hujja daga kotu ko da kwana guda ne kafin zaɓen, to da an dakatar da zaɓen 'yan majalisun dokokin a wuraren da lamarin ya shafa.
A wata sanarwa da sakataren jam'iyyar na ƙasa ya fitar, ya ce wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta karɓi sunayen 'yan takarar majalisun dokoki na jam'iyyar a wasu jihohin ƙasar.
To amma a cewar sanarwar da gangan hukumar INEC ta ƙi karɓarsu. Tana mai cewa an yi hakan ne kawai domin a yaudari masu zaɓe.
BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar jam'iyyar to amma zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani da muka samu.
Mene ne dalilin INEC na cire jam'iyya daga takardar kaɗa ƙuri'a?
Hukumar zaɓe takan cire jam'iyya daga kowacce takardar kaɗa ƙuri'a idan jam'iyyar ba ta gudanar da zaɓen fitar da gwani a kowacce kujera ba.
Haka kuma ko da ta gudanar da zaɓen fitar da gwani, amma ba ta gayyaci INEC domin sanya ido a zaɓen ba, Hukumar ba za ta saka jam'iyyar a kan takardar kaɗa ƙuri'a ba.
A ƙa'ida INEC na sanya lokaci ga jam'iyyu domin miƙa sunayen 'yan takararsu a kowaɗanne muƙamai.
Sannan kuma ko da INEC ta sanya ido a zaɓen fitar da gwani na jam'iyya, matuƙar ta kasa shigar da sunayen 'yan takararta cikin shafin yanar gizo na hukumar kafin ƙarshe wa'adin da hukumar ta sanya, to za ta iya rasa kanta a kan takardun kaɗa ƙuri'a, kuma ba za a sanya ta cikin jerin jam'iyyun da ke takarar wannan kujera ba.
Labaran ƙarya da ake yaɗawa game da INEC
Fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani sun yi ta yaɗa zarge-zargen cewa jam'iyyar APC mai mulki da hukumar zaɓen ƙasar na shirin tafka maguɗi a zaɓen na 2023, lamarin da ya sanya wa 'yan ƙasar shakku game da inganci da sahihancin zaɓen.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
An yi ta samun labaran ƙarya a shafukan sada zumunta da ke cewa INEC ta yi shirin amfani da na'urar BVAS ne domin yin maguɗin zaɓe.
Lamarin da ya sanya shakku a zukatan magoya bayan jam'iyyun adawa waɗanda suka yi barazanar shirya zanga-zanga matuƙar gwanayensu ba su samu nasara a zaɓen ba.
An samu rahotonnin samun matsalar tantance masu kaɗa ƙuri'a a wasu sassan ƙasar sakamakon wasu matsalolin rashin aikin na'urar da matsalar rashin intanet.

Magoya bayan jam'iyyun adawa sun yi zargin cewa mutane na shiga cikin shafin yanar gizo na INEC domin sanya sakamakon zaɓen da zai taimaki APC.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4

Karshen labarin da aka sa a X, 5
To amma an gano cewa wannan shafin ba na INEC ba ne wasu ne suka ƙirƙire shi ya kuma yi kama da shafin hukumar na ainihi, wanda kuma aka yi ta yaɗa shi.
Shafin na INEC tsararre ne ta yadda za a riƙa saka sakamakon zaɓen, a duk lokacin da ya kammala.