Zaɓen Najeriya 2023: Jadawalin ƙalubalen da ke gaban shugaban Najeriya da za a zaɓa

Asalin hoton, Getty Images/KOLA SULAIMON
Kasancewarta mafi girman tattalin arziƙi kuma mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka - mutum miliyan 214 - duk wani abu da ya faru a Najeriya yana da tasiri a faɗin nahiyar.
Masu kaɗa ƙuri'a za su zaɓi sabon shugaban ƙasa bayan kwashe shekara takwas ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, sai dai duk wanda ya yi nasara akwai wasu manyan ƙalubale da zai yi fama da su.
A wannan labarin mun kawo maku jadawali ƙunshe da wasu abubuwan da suka fi damun masu kaɗa ƙuri'a.


A shekarar da ta gabata - kamar sauran al'ummar duniya - ƴan Najeriya sun fuskanci matsalar hauhuwar farashin kayan abinci saboda rikicin Ukraine. To amma farashin ya fara tashi ne tun kafin yaƙin Ukraine, bayan da gwamnati ta rufe iyakokin ƙasar domin hana shigar da wasu kayayyaki. Sai kuma matsalar ƙarancin dala.
An kiyasta cewa an samu tashin farashi a shekara ta 2022 da kimanin kashi 19 cikin ɗari mafi muni ke nan da aka samu cikin shekara 20. Garin rogo na ɗaya daga cikin abubuwan da tashin farashin bai shafa ba sosai, to har yanzu iyalai na jin raɗaɗin tashin farashin abubuwa kamar tumatir da man girki.


Idan sabon shugaban ƙasar na son ya taimaka wa mutane kan rage raɗaɗin farashin abubuwan buƙatu na yau da kullum, to zai fuskanci ƙalubalen cewa yanzu haka gwamnati na kashe fiye da abin da take samu.
Ana kashe maƙudan kuɗaɗe kan tallafin man fetur, kuma ƙasar mai arziƙin man fetur ta gaza cin gajiyar tashin farashin mai a duniya kasancewar ba ta iya tace mai na a-zo-a gani a cikin gida, dole ne sai ta sayo tataccen man fetur daga waje.
Masu sharhi na damuwa kan ko ƙasar za ta iya ci gaba da biyan bashin da ake binta, ganin cewa a wasu lokutan cikin shekarar 2022 kuɗin ruwa kawai na bashin da ake binta ya fi ƙarfin abin da take samu.


A matsayinta ta ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fitar da ɗanyen mai a nahiyar Afirka, Najeriya na dogaro da ɗanyen man ne wajen samun kuɗaɗen shiga da kuma kuɗin ƙasashen ƙetare. Sai dai ƙasar ta kasa cin gajiyar kuɗaɗen da take samu daga ɗanyen man - an sace yawancin kuɗin, wasu kuma an yi wadaƙa da su.
Haka nan kuma yawan man da ƙasar ke haƙowa na raguwa a cikin shekara 10 da ta wuce. A 2022 yawan man da ake fitarwa ya yi ƙasa fiye da kowa ne lokaci a cikin shekara 30.
An ɗaro mafi yawan laifin a kan satar ɗanyen mai da masu farfasa butun mai. Hakan ɗori ne a kan shekarun da aka kwashe ba tare da zuba isasshen jari a ɓangaren ba, wanda hakan ya sa ƙasar ke komawa baya cikin jerin ƙasashen Afirka da ke fitar da man fetur a nahiyar Afirka.


Kasancewar rabin yawan al'ummar Najeriya matasa ne ƴan kasa da shekara 18, sabon shugaban Najeriya zai fuskanci ƙalubalen yadda zai ci gajiyarsu.
Suna bukatar bayar da gudummawa wajen taimaka wa bunƙasar tattalin arziƙi da kuma burace-buracen al'ummar mai tasowa.
Duk da cewa akwai mutane da dama waɗanda shekarunsu ba su kai na zaɓe ba, kashi 40% na masu kaɗa ƙuri'ar suna da shekaru ƙasa da 35 ne. Samun goyon bayansu zai iya yin tasiri a sakamakon zaɓen.


Abu na farko da matasan Najeriya suke so shi ne aikin yi.
Yanzu haka kashi uku cikin huɗu na al'ummar Najeriya ba su da aiki. A ɓangaren matasa, sama da rabi na ƴan shekara 15 zuwa 24 suna neman aikin yi.
Tabbas matakan yaƙi da cutar korona sun taka rawa, to amma yawan marassa aikin yi a ƙasar na ƙaruwa tun kafin ɓullar cutar korona.
Tattalin arzikin ƙasar na samun ci-gaba tun 2015, sai dai ba ya bunƙasa da sauri ta yadda zai samar da aiki ga duk masu neman aikin.
Ana ɗora wani ɓangare na laifin rashin bunƙasar tattalin arziƙin a kan rashin tsaro, amma masana tattalin arziƙi na ganin cewar ƙarancin kuɗaɗen ƙetare da rufe iyakokin ƙasar sun sanyaya wa masu zuba jari gwiwa.


Akwai ƙarancin wadatuwar abubuwan buƙatu na yau da kullum waɗanda za su iya bunƙasa rayuwa da harkar kasuwanci.
An daɗe ana suka kan ƙarancin lantarki na ƙasar, alƙaluman Bankin Duniya sun nuna cewa ƙasa da kashi 55% na al'ummar ƙasar ne ke samun wutar lantarki.
Idan aka zo ɓangaren masu amfani da intanet kuwa, kashi 36% ne kacal na al'ummar Najeriya suke iya shiga intanet, wanda hakan ya sa ta zamo daidai da sauran ƙasashen Yammacin Afirka.

Magance ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya shi ma babban ƙalubale ne ga sabon shugaban ƙasar.
Lokacin da aka zaɓi Shugaba Buhari karon farko a 2015, babbar matsalar tsaro da ake fuskanta ita ce ta Boko Haram wadda ke addabar arewa-maso-gabas. Duk da cewa yanzu Boko Haram ba ta riƙe da wani yanki na ƙasar, ƙaruwar garkuwa da mutane, da hare-hare masu alaka da siyasa, da rikicin manoma da makiyaya, da na ƴan bindiga, da kuma amfani da ƙarfi fiye da ƙima daga jami'an tsaro na sanyaya gwiwar al'umma game da ikon gwamnati na tsaron lafiyarsu.
A yanzu matsalar ta yaɗu zuwa faɗin ƙasar, ba arewa-maso-gabas kawai ba.
Akwai yiwuwar wayarku ba za ta iya nuna wannan zanen ba

Ɗaya daga cikin yara biyar waɗanda ba sa zuwa makaranta a faɗin duniya daga Najeriya suke, kamar yadda Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana.
Kasancewar kusan kashi 40% na yara ƴan shekara 5 zuwa 11 ba sa zuwa makaranta lamari ne mai tayar da hankali.
Wannan matsala ce da ta shafi kowane ɓangare na ƙasar, to amma ta fi ƙamari ne a arewacin ƙasar. Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da suka ta'azzara lamarin, sai dai talauci da kuma bambancin jinsi na taka muhimmiyar rawa.













