Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Umar Yahaya Malumfashi: 'Yan Kannywood na jimamin rasuwar Bankaura
'Yan fim da furodusoshi da daraktoci da masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood sun yi ta bayyana jimami da alhinin rasuwar fitaccen dan wasan nan Umar Yahaya Malumfashi da aka fi sani da Bankaura ko Ka fi Gwamna.
A daren Talata 27 ga watan Satumba ne, Allah ya yi wa fitaccen jarumin rasuwa a wani asibiti da birnin Kano a arewacin Najeriya, bayan fama da rashin lafiya.
Umar Malumfashi da aka fi sani da sunan Bankaura a cikin tsofaffin finan-finan Hausa tun kafin kafa masana'antar Kannywood, yayin da a wannan zamanin kuma ake kiransa da sunan Yakubu ka fi gwamna, saboda rawar da ya ke takawa a shirin Arewa24 mai dogon zango wato Kwana Casa'in.
Bankaura ya taka muhimmiyar rawa domin ciyar da masana'antar Kannywood gaba, yana daya daga cikin 'yan wasan da suka dade a wannan fagge.
Ya yi zamani da manyan iyaye mata da maza a masana'antar, irin su marigayiya Hajiya Amina Garba (Hajiya Dumba, ko Hajiyar falo), da marigayiya Hawwa Ali Dodo (Biba) da marigayiya Jamila Haruna, da su Hajara Usman, Saratu Gidado (daso) da sauran su.
An yi amanna da cewa yana daya daga cikin wadanda ke tafiya da zamani a masana'antar Kannywood, karamin misali shi ne rawar da ya taka a shiri mai dogon zango na Kwana Casa'in.
Tuni abokan sana'arsa da makusanta suka bazama shafukan sada zumunta domin bayyana alhini da ta'aziyyar rasuwarsa.
Alhaji Ado Gidan Dabino na daya daga cikinsu, musamman ganin ya na daya daga cikin wadanda sukai wa marigayin gani na karshe.
Gidan Dabino ya wallafa hotonsa tare da marigayin, a wurin daukar shirin Kwana Casa'in suna duba wasu takardu, ya wallafa
''Allahu Akbar. Allah ya jikan Umar Yahaya Malumfashi, Bankaura, Yakubu Ka Fi Gwamna a cikin shirin Kwana 90, Allah ya gafarta masa ya sa ya huta. Ya sa aljanna ce makomarmu baki daya.
"Shekaran jiya da muka je asibiti duba shi mu hudu, mun iske shi da iyalansa, amma shi bai ma san mun zo ba, saboda jikin nasa ba dadi. Ashe ganin karshe na yi masa. magana kuma ba mu sami damar yin ta ni da shi ba. Wayyo Rayuwar kenan, sauran mu. Allah ka sa mu cika da imani. Amin.''
Shi ma fitaccen jarumi Sani Mu'azu, kuma aminin marigayi Malumfashi a shirin Kwana 90 wato Alhaji Bawa Maikada gwamnan Alfawa, ya wallafa hoton marigayin da sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan sana'arsu.
''Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Ina bakin cikin sanar da rasuwar abokin aikin mu Umar Yahaya Malumfashi da aka fi sani da kafi Gwabna, ko Bankaura. Allah ya gafarta masa, ya yafe masa kurakuransa.
"Allah ya sa ya huta. Allah ya raya abin da ya bari a baya. Allah ya sa mu cika da imani idan ta mu ta zo. Ina mika ta'aziyya ga iyalansa, da kuma masana'antar mu ta Kannywood baki daya.''
Shi ma Abba Al-Mustapha ga abin da ya ce:
''Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Allah ya yi wa Babanmu Alhaji Umaru Malumfashi wanda aka fi sa ni da ''Kafi Gwamna'' rasuwa. Za a yi jana'izarsa a gidan shi da ke unguwarsa ta Hotoro. Muna Addu'ar Allah ya jikansa ya gafarta ma sa kurakuransa ya sa Aljanna ce makomarsa. Idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani.''
Ita ma Rukayya Umar Santa da aka fi sani da sunan Dawayya, ta wallafa a shafinta na Instagiram, cewa ta kadu matuka da wannan babban rashi da suka yi:
Maza da mata, yara da manya a masana'antar Kannywood su na ta wallafa sakonnin ta'aziyya da abokan aikinsu, har da iyalai da abokan arziki.
Babu cikakken labarin tun wanne lokaci Kafi Gwamna ya kwanta rashin lafiya, sai 'yan makwannin da suka gaba ne batun ya fito.
Kuma ranar 20 ga watan Satumba, Mujallar Fim ta garzawa asibitin da aka kwantar da shi a unguwar Hausawa a birnin na Kano.
Mujallar ta rawaito cewa, bai iya hira mai tsaho da wakilin Fim ba, saboda yadda jikin nasa ya tsananta, amma duk da hakan, ya roki al'umma su taya shi addu'ar Allah ya ba shi lafiya.